Talatin

239 54 4
                                    

Rayuwata

Babi na uku

Duk wannan farin cikin yana karewa ne a duk sanda na sa kafa cikin gidanmu, gidan da ya ke matsayin na mahaifi na amma ya zame mini wurin da na ke tsoro fiye da ko ina a dukkan rayuwa ta.

Zaune su ke duk a falo suna kallo niko sai faman mopping in falon na ke. Duk na gaji saboda tulin wanki da wanke wanken da na gama sai haki nake amma ba wanda ya daga ido ya kalle ni balle in samu daman sannu.

Sadiya ce ta shigo da gudu kafan ta  ba takalmi duk kasa ta taka inda na ke mopping yayi caba caba, idanu nane ya kawo ruwa ban San lokacin da na ture ta ina fadin "haba Sadiya baki ganin nayi mopping ne kin ba..." Wani irin karan da naji ya sauka a tsakiyan kai na ne ya sa na kasa karasa abinda zan fada. Wani irin kallo da Anty Yana ke bina dashi ne ya sa na San yau fa kashina ya bushe. Karan ta cigaba ba kakkauta, Al-lawan ne yazo ya dauke ta yana fadin "kiyi hakuri mana, sai kace wacce za a kashe" kasa cigaba da mopping in nayi nayi turus ina kallon Adda Falmata da Anty yana jiki na sai rawa ya ke. Ban Ankara naji sauka. Bulala a jiki na ko ta ina tun ina muka har murya ta dishe. Sama sama na ke jin Sallama. "Lfy wa ake duka haka?" Naji murya kaman ta ya baba na magana.

"Au ashe kai ka dawo, duk ta kare sadiya kai tagani ta shigo ta fada wannan Mara imanin ta hankade ta ta fadi" kallona yaya baba yayi, sai faman nishi na ke, harara ya zabga min  "Wai Anty Yana har yanzu wannan bakan mujiyan ta na gidan nan?"

Tabe baki tayi tace "to ya zanyi da ita ta zame min karfen kafa, duk rashin dukana sai da ta sa yauwa na buge ta"

Adda Falmata ce ta zabga min harara  "yarinya sauran nawa ba ke muguwa ba, na fi iya mugun ta kuma ki ta shi ki cigaba da mopping In da kike" jiki na rawa na tashi na cigaban. Adda Falmata ce ta amshi jakan yaya baba ta wuce mai dashi dani ya bita yana fadin "ke in kingama mopping in ki kawo min abinci da ruwan wanka"

Da kyar na samu na karasa sannan na debo abinci na kai mai daki, suna zaune tare da abokin shi Umar Sanda na wuce toilet na dauki bucket na kawo mishi ruwan. Jiki na rawa na ke sanar mishi na gama. Wani kallo ya bini dashi mai cike da tsana yace "ke wai kina yar karaman ki har kin iya mugun ta ko yau zaki Sani, maza fara tsallen kwado" idona duk ya kawo ruwa haka na fara, tun ina daurewa ina yi har na fara kuka. Kallon shi ya ke hankalin shi kwance sai Umar sanda da ke gefe yana ta faman dariya "Adams wai dan wannan abu ta kewa kuka, come on spring ya kamata tayi ma wlh" Ya baba bai juye ya kalle ni sai cewa yayi "ai kinji abinda yace koh?" Ina share hawaye ne na fara spring in, abokin na gefe yana ta faman murmushi ni ko ina zuba mishi Allah ya isa a zuciya ta, da yaga nayi kaman zan fadi sai ya kwashe dariya har da rike ciki.  sai da ya gama alamun numfashi na na neman daukewa sannan Ya baba Ya ce wuce na bashi wuri. Tabbas a lokacin naji wani tsanan Ya baba a raina sai dai na munafukin abokin sa Umar Sanda ya wuce hakan Dan tsananin azaba da kyar na ke iya motsa kafan da dafen bango na karasa dakin, muryata har ya dishes dan kuka har majina ke fitowa, Ranar na tabbatar ya baba ya fi Adda Falmata mugunta.

Sai me? Ina shiga dakin Adda Falmata ta sani kneel down, na daga hannu sama na rude idanu, ko kadan ba ta damu da irin halin da na ke ciki ba. Na rasa wani irin zuciya yaran Anty Yana ke dashi ba, na kanyi takaici duk sanda na tuna yan'uwa nane. Haka ta dinga zabga min mari har sai da ta gaji, fuska na ya kumbura yayi suntum sannan ta kyale ni, wlh tun ina kukan har na neme shi na rasa. Bacci kam Ranar kaura yayi a idona, idona garas har asuba, sai dai sunyi jawur, kai na ko kaman garwashi dan zafi, wani mahaukaciyar zazzabi ne ya rufe ni a nan ta ke.

wan sanyi na dinga yi akan gadon da na ke kwance ni kadai har su ka tashi su ka fara zuwa makaranta, sai dai nasan ko da wasa bazan iya zuwa makaranta ba. Ina ji sadiya na taba ni wai ance na tashi na siyo musu waina da yar yau sai dai ko kwakwaron mosti na kasa yi.

Labarin Rayuwata Donde viven las historias. Descúbrelo ahora