Ina nan cikin zulumi washegari har wurin azahar ba ta farka ba. Ko da naje gaishe da mum ta tmby ni Amal in, nace mata tana baccin har yanzu.
"Ta fadi abinda ya same ta a jiya?" Sai lokacin na gane Amal ba ta fadawa mahaifiyar ta abinda ya faru ba a jiyan. Dan haka na dan sake. Amal fa har bayan Magreeb ba labarin ta, duk addu'an da na taba sani ba wanda ban jarraba ba amma ko motsin ba ta yi. Ko dana fadawa zayd ce min yayi "she overdose herself ki kwantar da hankalin za ta tashi"
"Kwanciyar hankali fa kace zayd ina na gan shi? Why are you so selfish ne Wai?" Bala'i na fara mishi a wayan da har sai da ya firgita. "Kai wani irin mutum ne ina fada maka halin da mutum ke ciki kana irin... You know what, I just realize you are not the best person to talk to" ina fading haka na kashe wayan, tsoron kar yar mutane ta mutu da alhakina yasa na gudu cikin gidan na fadawa mum abinda ke faruwa. Ina jin yan matan da ke gidan na ta kananan maganganu akan menene nake damuwa? Ai ba sabon abu bane da Amal ta sha drugs. Ban bi ta Kansu na isa ga mum. Da gudun ta ta nufi side in namu, ganin Amal ya ruda mata tunanin. Da ihu ta fara kiran driver ya fito, ni da wasu daga cikin cousins in Amal in ne mika dauke ta izuwa mota.
Ihun da mum ke yi yasa driver ke ta speeding har zuwa the closest hospital daga gidan. Direct su ma A&E su ka wuce da ita. Ba dadewa likitocin su ka sanr zuciyan ta na neman buguwa za a shiga da ita operation zuciyan ta za iya buguwa anytime soon. Kai wannan ranar na ga tashin hankali, ya guilt da ke ta faman bibiyata. Zayd ma yazo asibitin a rude, sai dai ba wanda ke ta tashi. Mum ta tana ganin zayd tq cakume wuayn rigan shi tana fadin "Duk abinda ya fara da diyata you will be hold responsible zayd, kai koya mata duk wani abinda take in ba haka ba ina Amal ina irin wannan drugs in? In ba kai ke kawo mata ba" da kyar ake raba mum da zayd saboda Marin da tayi ta zuba mishi sai da yayan Amal in Salim ya shiga tsakanin su. It was a terrible day saboda haka mika kwana ni da mum bamu runtsa.
Ko da aka fito da ita daga operation bata farka ba dai amma likitocin sunce it successful. Da kyar aka twankwashi mum mu ka tafi gida. Sai dai da gidan da asibitin kaman abu data ne, don ni a ganina ma asibitin har yafi sauki, at least a nan za ka leka ta ka ganta.
Har safiya Amal kam ba ta farka ba, a takaice dai kwana biyu ba a San tana rayuwa ko mutuwa ba. Gata nan kawai a Raye numfashi ma sai da taimako ta ke shaka, it hurt to see someone in comatose barin ma shakuwa irin namu da Amal, a girl with such a pure heart. A ranar na fizgi mota da kaina na tafi wurin Anty Umaymah, a vows na same ta. Ban tsaya mun gaisa ba ma nace mata "Am done Anty Umaymah"
Da sauri ta zare glasses in da ke idanun ta. Girgiza kai tayi tace "no you can't baby"
Siririn tsaki naja nace "shin kin san irin halin da na ke shiga a duk lokacin da nake abinda zuciya ta bata so, ko kinsan zafin pretending to be nice with people when all you are doing is breaking them? Kin san zafin ganin wanda ya so ka a rayuwa ya baka dukkan yarda da amana a kwance cikin mawuyacin halin da kai kasa shi a ciki. Baki san zafin butulcewa ba" da kuka na karasa zancen nawa. Da sauri ta tashi daga seat in ta ta dan jawo ni jikin ta tana comforting ina, she is so caring in every situation.
With a very cool voice tace "now tell me meke faruwa?" Cikin sheshekar kuka na sanar mata halin da Amal ke ciki a halin yanzu.
"Suhaima kenan to ai butulcewa shine ki kyale ta da zayd yana cigaba da zurmata cikin rayuwan da ba zai taba bata ba."
"He loves her" na fada ina kallon sju'umin murmushin da ke kwance kan fuskan ta.
"He claim so sai dai ke ma yana sonki right? Ga kuma matar shi Aminatu. To ki fada min waye ke so a ciki, kar ki manta fa yana tare da Amal in tuntuni ya gani kuma yace yana so. Ko an gaya miki in yaga wata macen ma bazai so ta bane?"
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...