Jigum Mustapha ya zama kafin farfadowan Anty, ko bayan ta farfado ma barin ta aka yi a asibiti ba abarin wani ya zauna gun ta. So Mustapha bai samu daman komawa Abuja ba duk yanda ya so hakan.
Yana nan garin kaduna har aka sallami Antyn sai ranar su ka hadu da Antyn, kallon shi kawai tayi ta dauke kai, to duk sanda ta mishi wannan ya san ba karamin fushi take dashi ba, barin ma yanzu da yake tunanin shine sila. Sai da ya bari a dan natsa washegarin dawowan ta yaje ya same ta its kadai a dakin ta. Ba ta mishi magana ba dai haka kuma bata daure fuska ba. A hankali ya taka har ya je gaban ta ya zauna, kwanciya kuma yayi ya daura kanshi akan cinyan ta. Yayi mamakin sa hannunta da tayi cikin suman shi tana shafawa. "Little drop that case bana ka bane na fada maka kaki ji, kai ba ka tsoron ba wani abu ya faru da kai?"
Murmushi yayi sannan ya dago yana kallon ta ya dan dukar da kanshi "Anty na ke kike min wa'azi akan taimaka ma duk wanda ya ke cikin halin neman taimako, yarinyar nan looks so innocent i have to help her"
"Looks can be deceiving Little kuma ma in taimakon kake so ai ba dole sai kai za kayi case in nan ba"
"Na riga na fara Anty kuma wlh ba accusing Faroukh nake ba kawai dai ina tunanin akwai abinda ya sani wanda ya boye min" shiru tayi kaman mai wani lissafi "Ba zan ce Faroukh ba zai iya aika ta koma mai kake zargin yayi ba but little Faroukh is my son, kai kawun shine da kuka matukar shakuwa shin ko ya yi abu kai ba mai iya kare shi bane?"
"Faroukh bai yi ma komai ba Anty, ai muna magana dashi kuma ko bayan zaman court in ba abinda ya dauka na fushi tsakaninmu, min samu kyakyawam fahimta saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Anty na, i have nothing against my boy" jinjina kai tayi tace "ban son hana ka abinda kayi niyya saboda a ko da yaushe kai mai yin biyyayane a gare ni, ba case in ku bane ya sani a halin da nake ciki little kawai news in yazo min ne a lokacin da nake cikin wahala"
A tsorace yace "me ke damun ki Anty na?"
"Stress little kuma jini na hawa"
"Ya ilahi!" Ya furta sannan yace "please Anty ki ajiye lecturing in nan" da ido ta amsa shi.
...
Abuja, Nigeria.
Dr Fahad da Barr zaune, kokari su ke su saurari labarin suhaima da har ya jawo mata fadawa irin wannan mummunar rayuwan haka. Sai dai abin yana neman ya gagara domin dai Suhaima ta ki basu hadin kai. Ita a ganin ta ko ta rayiwan ma ba wani amfani don haka she want to end everything for good.
"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta domin bakin tabon da ke jikin ta ba zai taba gogewa ba.
"Karuwan ci? Tabbas nayi shi haka kuma na kasance maci amana ga wadanda su ka bani yarda, shin me kuma kuke so ku sani bayan wannan? Ku barni kawai ayi hukuncin da ya dacen ina ganin nayi deserving komai ma.
"Kin yi yunkurin kashe Zayd" kaman ta daga kai ko za su kyale ta sai dai kalman kisan ya mata mugun nauyin da take jin ba ta ma kanta adalci ba in har ta amince da abinda ba tayin ba.
"Then ki bar mu muyi abinda ya dace" ba wanda yace komai ba har bayan yan mintunan "Suhaima please tell us" Dr Fahad ya fada cikin marairaicewa. Ita kam mamakin yanda su ka dage suna rokon ta akan abinda tasan ita zai amfana. Sai dai tasan duk yanda ta so basu labarin rayuwan ta yana da tsawon da ba zata iya zayyana shi cikin lokaci kankani ba. Ba ma wannan ba tukun, ba taji bakin ta xai iya dauriyan furta wahalolin da su ka mata katsalanda a dukkan rayuwan ta.
ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...