chapter 1

408 27 0
                                    

Jeguk (empire) high school makarantace wadda ta amsa sunanta na makaranta a babban birnin Seoul ta kasar Korea  makarantace wadda idan ka shiga cikinta ba zaka dauka a cikin makaranta kakeba saboda asalin haduwarta da tsarinta akwai komai na more rayuwa ta kasance 'ya'yan kasarma sai wadanda sukaci suka tada Kai ke iya halartar makarantar. Fatima kabir Ahmad na daya daga cikin jerin yaranda ke zazzaune a kujerun da suka yiwa hall din kawanya suna sauraren farewell lecture da director na school din ke gabatarwa ga daliban da zasu bar makarantar a Yau kusan dukkanin daliban hankalinsu na kan director Lee Jung sung banda Fatima da wasu tsiraru yan uwanta da hankalinsu yake kan planning dinsu na daga yau makaranta ta zama tasu sun zama sune seniors wadanne dokoki zasu canja wanne zasu kirkira wannan shi ya dauke hankalinsu har aka gama taron aka fara bada kyaututtuka ga dalibai masu hazaka kamar irinsu Ahmad kabir Ahmad (Halifa). Halifa ya karbi kyaututtuka da dama Wanda har ya taba zuciyar wasu daga cikin board members na jeguk grp domain akwai 'ya'yansu da yawa a wannan set din suna ganin ya zaayi wani can bare yazo kasarsu sannan yafisu iya rawa? Alhalin da yarensu ake koya musu ba turanci ko hausaba? Abin ya bawa mutane da yawa mamaki ya kuma bawa da yawa haushi. Sudai iyalan Alh kabir Ahmad suna cikin farin ciki sosai da wannan nasara ta Dan nasu alhmdulillah kawai suke cewa. Bayan an kammala taro an gama komai suka had a kan 'ya'yansu zuwa masaukinsu cikin farin ciki marar misaltuwa nan aka babe aka yiwa Halifa dan karamin party na tayin murna fatima tafi kowa zakewa dan tafi kowa shakuwa da dan uwan nata sai bayan an gama komai mahaifinsu Alh kabir Ahmad ya zaunar dasu tare da yi musu nasiha mai ratsa jiki da kuma Jan kunne akan duniya da kawarta sannan a karshe ya rufe da yi musu addu'a ta Neman tsari daga dukkan mai nemansu da wani sharri daga nan kuma kowa ya watse domin kwanciya bacci saboda gobe jirgin karfe 7am zasubi zuwa gida Nigeria. Fatima kam da Halifa da suka shiga daki ba kwanciya sukayiba gifts din da ya samu suka Fara budewa cike da farin ciki ba su suka kwantaba sai gab da asuba ai kuwa da kyar aka samu suka tashi yin sallah anan man sallayar fadimatu ta kuma bingirewa ta cigaba da baccinta. 6:20am suka Fara fitar da kayansu domain tafiya airport momy ta shiga dakin fadimatu da niyyar fito da kayanta kawai sai ganinta tayi tana bacci ai kuwa ta dala Mata kyakykyawan duka a cinya firhigit ta mike tana Sosa wajen tare da tabe duska kamar zatayi kuka cikin hade rai momy tace "wannan wanne irin iskancine fadima? Kinsan Yau zamu tafi gida amma kike kwance kina bacci? Kin fimu idon baccinne ko kuwa San baccin kika fimu? Kin tashi a wajen ko sai na kwada miki Mari tukunna?" Da sauri ta mike tayi toilet da gudu ai kuwa cikin abinda bai wuce 29min ba tayi wanka ta shirya komai da komai amma duk da haka a gurguje suka Isa airport din suka hau jirgi zuwa Lagos sannan daga Lagos suka hau wani zuwa kano ta dabo ci gari.

Alhaji kabir Ahmad Dan kasuwane mai ji da tashen dukiya Wanda kasuwancin gwangwan yake tafiyarwa yadda ya kamata babu wanda yasan Alh kabir (dady) da matarsa haj kubra (momy) daga inda suke kawai dai an gansu amma fa babu dangin uwa ba na uba, da farko sun zauna a wata unguwa da ake Kira da Jaen shago Tara daga baya bayan Allah ya kuma buda musu arziki ya kankama sai suka koma janbulo 3rd gate inda Alh kabir ka kankara musu wani aljannar duniya suke ciki da 'ya'yansu uku Ahmad (halifa) shine na farko Wanda dashi suka zo yana Dan jariri bayan an yayeshi aka haifi fadimatu wadda shekara dayace kacal a tsakaninsu da Halifa daganan kuma haihuwar ta tsaya da kanta wannan ya Kawo shakuwa marar iyaka tsakanin Halifa da fadimatu babu mai shiga tsakaninsu babu Wanda yasan damuwar dayansu sai su babu kuma Wanda ya Isa ya taba data ba tare da dayan ya shigar masaba duk da halinsu ba data bane ko kadan Ahmad yarone mai hakuri da kauda Kai sannan yana da juriya saboda Fadima zata iya yin laifi a makaranta amma sai ya tubure yace shine haka za'a zaneshi kuma wani abin dariyar shine shi ake duka amma fadimatuce mai kuka saboda ita kuma akwai ragonta amma fa akwai tsiwa da rashin kunya ga zuciya bata da hakuri ko kadan shiyasa kullum tana cikin fada da mutane baga 'yan makarantaba ba ga 'yan aiki a gida ba Halifa kawai take dagawa kafa dan shi na musammanne a zuciyarta sai KO dadynta amma momy ma kullum suna cikin fada saboda tana yi Mata fada kan ta gyara halinta ita kuma gani take ai kawai momy bata sontane.

FadimatuWhere stories live. Discover now