Chapter 11

87 7 0
                                    

Bayan mun gama cin abinci na koma dakin momy ina shiga tana farkawa dan haka na bata ruwa tasha dama na tafi mata da abinci na bata dakyar ta karba dan da kamar bata fahimci meyeba sai da nakaishi dai dai bakinta na kuma bude nawa bakin tana budewa na zuba mata sannan na samu ta tauna ta hadiye daga nan kuma ta fara karba ba tare da wata matsalaba wato ta fahimci meye kenan.
Bayan ta gama Halifa ya shigo tana ganinsa ta fara ja da baya tamkar mai tsoronsa dan haka ya tsaya daga bakin kofa nan da nan idonsa ya ciko da kwalla, cikin muryar kuka yace "Fadima ya zamuyine ya kamata mu gayawa dady gaskiya haka sannan mu dauke momy a wannan dakin saboda kudinmu yana kuma karuwa each second da ta zauna anan" na yadda da abinda ya fada dan nasan asibitin kudi nasan tsadar wannan asibitin sannan na kuma san halin da muke ciki dan haka na bashi amsa da "tabbas ya kamata dady ya san gaskiya amma ina tsoron abinda zai iya faruwa idan yasan gaskiyar kaga feenama batasan abinda ya faruba ina gudun karbar da momyn zatayi mata " Halifa yace "nasan da hakan amma komai boyewarmu dole gaskiya ta fito sannan the longer muka ja maganar the more zamuyi hurting dady dan haka ina ganin kawai muje da momyn muyi masa bayani idan yaso kiyi anfani da kulaki da take kiyi mana controlling nata" a hankali na mike daga gadon ina fadin "shikenan Allah ya takaita mana abinda zai iya faruwa koma meye ya kuma sa na iya controlling din nata, amma in case kaga feena ta taho wajenta da gudu ka riketa saboda na fahimci idan an tunkareta da saurine take tsorata" "OK ba matsala Allah dai ya taimakemu" nace "ameen".
Haka na kama hannunta muka fito muna tafiya tamkar wadanda kwai ya fashewa a ciki, kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa yayinda momy ke kalle kalle kamar irin yan kauyennan sun shigo birni, wannan abin kawai da takeyi sai da yasa naji kamar zanyi kuka wai yau momyna mai aji da kamun kaice wannan take kalle kalle irin haka, muna zuwa kofar dakin da dady yake muka tsaya kowa a tsorace, kallon kallo mukeyi ni da Halifa zuwa wasu yan seconds yace "you ready?" Sai da nayi inhaling deep then exhale sannan nace "yes" ahankali tamkar wanda ya dauki jariri haihuwar yanzu ya tura kofar, feena na zaune gefen dady a kan gado tana uwar magana shi kuma sai murmushi yake yana kallonta, ji nayi zuciyata ta karye saboda nasan wannan murmushin nasa yanzu zai gushe idan yaji wannan bakin labari. Kamar yadda nayi tsammani kuwa abinda ya faru kenan da gudu feena ta duro daga gadon tana hango momy tayo wajenta da gudu da niyyar rungumeta amma sai Halifa yayi saurin tareta ya dagata sama kamar irin yanayi mata wasannan har suka sami wajen zama ba tare da ya cikataba, tun da muka shigo dady ya kafe momy da ido ko kiftawa ba yayi har na sami cushion din dake dakin irin two sitter dinnan na zauna, ai kuwa momyma ta zauna a kusa dani kamar zata shige jikina, still idon dady na kan ta sai bayan ta zauna sannan ya maida kallonsa gareni yace "Fadima me ya sami momynku? Naganta wani iri" halifane ya sami damar bashi amsa domin already na fara kuka, nan ya kwashe labarin abinda ya faru kaf tun daga jiya fadowar da tayi har zuwa yanzu ya gaya masa wanda kafin ya gama shima kukan yakeyi sosai kamar zai shide haka dadyma kuka yake sosai, sai dai alhmdulillah abinda nayi zato bai faruba dady yayi tawakkali ya daiyi kuka sosai har kamar numfashinsa zai dauke amma babu wani abu daya faru bayannan, muna cikin haka Dr ya shigo Dan haka shima ya zauna yayiwa dady bayani sosai ya kumayi masa nasiha tare da bashi hakuri akan ya dau kaddara kar ya dami kansa da tunani in sha Allah komai zaizo karshe.
Cikin kuka dady yace "yanzu Dr kana nufin ina gani haka zanbar matata a cikin wannan halin batasanniba batasan 'ya'yantaba? Karfa ka mantafa Allah ne yace bai halicci wata cutaba sai da ya halicci maganinta sannan ka gayamin babu maganin wannan cutar? Dr a duba dai baza'a rasashiba" ajiyar zuciya Dr ya sauke sannan ya ce "alhaji bawai babu maganin cutarne gaba dayaba a'a akwai amma nidai bansan asibitin dakeyi a Nigeria ba, naje wani course ne ma a America naji labarin an fara yin aikinsa amma da idona ban taba ganin wanda akayiwaba saboda aikin nada hadari da kuma wahala shiyasa nace kawai kuyi hakuri ku cigaba da yi mata addu'a wataran ita kadai zata dawo dai dai in sha Allah" dady ya fara kokarin ci gaba da magana nan da nan jikinsa ya fara karkarwa numfashinsa na neman daukewa saboda yaune rana ta farko da yayi irin wannan doguwar maganar bayan kwanciyarsa sannan ga kuka da yayi, dan haka Dr ya dakatar dashi daga maganar da yakeson yi da cewa "kaga alhaji ya Isa maganar haka ka kwanta ka huta idan anjima zanzo mu cigaba amma yanzu ka huta, Bari ma nayi maka allurar bacci ka samu ka huta" yana fada yana hada allurar dan haka yana yi masa bacci ya kwasheshi, ita kuwa momy tunda na fara kuka farkon shigowarmu itama take kukan sai dai kana kallonta kasan da matsala a kukan nata dan babu emotion kawai yinsa take, haka Halifa da feena ma duk kukan suke.
Ranar dai haka muka wuni kuka da tagumi, babu inda nake zuwa dan momy ta kafa ta tsare ko motsi nayi sai tayi, dakyar ta bari feena tazo kusa da ita da feena ta ishemu da tambayar kawai ce mata nayi bata da lafiya batason a dameta shiyasa" .
Washe gari da safe Dr ya kuma zuwar mana da wata sabuwar muna zaune muna cin abinci ya shigo,bayan mun gaisheshi ya duba dady sai ya sami kujerar zama instead of fita kamar yadda ya saba, muna ganin haka mukasan da abinda zai fada dan haka muka bashi attention namu shi kuma ya fara "ahmm alhaji ina fatan zaku fahimceni kar kuyimin bahaguwar fahimta, wani tunani nayi jiya bayan nabar nan, wato ciwonku dukka ku biyun baya bukatar sai kun zauna a asibiti zaku iya komawa gida kuna shan magani kuna kuma yin addu'a bakwa bukatar ganin likita kullum, shine nace why not da kudin nan da kuke biya na asibiti tunda nasan halin da kuke ciki ku koma gidan ni na daukar muku alkawarin zan dauki nauyin gashin kashin da za'a rinka yi maka duk sati tunda ina aiki a Murtala Muhammad dan haka duk sati a rinka kawoka nayi alkawarin daukar wannan nauyin, ita kuma hajiya zan rubuta mata magani wanda zai taimaka mata regaining memoryn na ta indai ba wani abu kukaga tayi unusual ba bata bukatar Dr, dan haka Ku koma gida Ku zauna a daina cin kudinku a banza amma ku ya kuke gani" Kowa shiru yayi cikinmu ganin bazamu yi maganaba sai kawai yace " amma bari na barku kuyi shawara duk abinda kuka yanke daidaine amma dai inason ku tuna shi wannan asibitin na kudine kuma ba ni kadaine maishiba kusan ma ni ma'aikacine kawai dan haka bani da iko a kansa, sannan ku tuna kamar yadda na fada muku cewa ba dolene ku zauna a asibitiba dan bashi da amfani,wasu ciniki suke bukata ni kuma taimakonku na ke bukataryi, duk abinda kuka yanke ina office nan da zuwa 2pm" yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga dakin ya barmu jigum jigum.
Bayan wata daya
Mun sauki shawarar Dr tun a ranar ya bamu sallama bayan mun biya kudaden da ake binmu wanda yaso cinye dan ragowar kudin hannunmu, badan Allah yasa Dr ya bamu wannan shawarar mun bar asibitin a lokacinba inajin da nan gaba idan muka tashi biya sai mun hada da kuma saida wani abin kafin mu biya wanda banajin munada sauran abinda zamu iya siyarwa. Dan ragowar kudin da yayi saura a hannunmu Halifa yayo mana cefanen kayan abinci sannan ya saka feena a makaranta tare da siya mata abubuwan da zata bukata na makarantar danma government school ce, sannan aka siyowa su momy magungunan da aka rubuta musu kowa na wata guda. Jikin momy da dady alhmdulillah babu wani mugun abu da ya kuma faruwa, momy dai har yanzu bata tuna komaiba, nice babbar kawarta kuma mamanta dan momy ma take cemin kamar yadda nake ce mata Halifa kuma brother yadda muke kiransa ni da feena, feena kuma feena sai dady da haryau tsoronsa takeji shiyasa ma har yau bata bashi sunaba. A bangaren dady kuma alhmdulillah yanzu yana iya yin hira sosai har yakan daga hannunsa na dama ya dauki abu marar dauyi dashi.

FadimatuOnde histórias criam vida. Descubra agora