Ni kam kasa yin komai nayi sai binsu da ido da nake, can na jiyoshi yana cewa "Anty kubra ina uncle ina Halifa nayi missing dinsu sosai" yana fada yana neman shigewa cikin gidan, da sauri ta janyoshi baya sannan tace "ina zakajene Naim? Uncle dinka bansan inda yakeba rabona dashi tun ranar da muka baro gida tun a ranar muka rabu ban kuma sake ganinsaba har Yau" cikin tashin hankali yake girgiza kai "innalillahi wa innailaihir rajiun ban ganeba Anty bakisan inda uncle yakeba? Ya akai kuka rabu shi kuma ina ya tafi?" Tana kokarin goge hawayen fuskarta wani na zuba tace "tun a tasha da mukazo garinnan muka rabu ya bacemin ban kuma ganinsaba har yau" shiru yayi ya dafe kansa tashin hankali rubuce a fuskarsa zuwa can ya dago kai da sauri yana cewa "amma Anty idan har da gaske tun a ranar kuka rabu da uncle me yasa baki koma gidaba? Kinbar gidane sabodashi idan har bakwa tare ai babu amfanin zamanki ke kadai na tabbata da bakwa tare da tuni kin koma gida" hade rai tayi tace "kana tunanin zanyi maka karyane? Menene ribar boyeshi idan har ina tare dashi? Naki komawa gidane kuma saboda kunya, da wanne idon zan kalli goggo wadda na watsawa kasa a ido na zabi mijina a kanta sannan kuma ace mijin ya gudu ya barni a ranar dana zabeshin? Shiyasa na kasa komawa gidan bazan iya komawaba" kuka take sosai da sauri nazo na rungumeta sai a lokacin ya tuna dani yana kallona yace " ke ya sunanki?" Duk da na fahimci dan uwanmune amma bai isa yace zai wulakantaniba wai 'ke!'. Kallon tara saura kwata nayi masa nace "ban saniba" nan da nan ya kara hade rai "dallah Malama ba rainin wayo nace kiyiminba yaya sunanki nace" ina zunburo baki na "Fadima" da sauri yace "Fadima wa?" Kallon mamaki nayi masa nace "Fadima Kabir" da sauri ya waiga wajen momy dake kuka har yanzu yace "yes Anty uncle yananan tunda sanda kuka taho Halifa na jaririne kinga da kun rabu tun a ranar baza'a haifi wannanba" ya karasa fasa yana nunani da yatsa. Muna cikin haka Halifa ya shigo da sauri ya karaso wajen momy yana fadin "momy lafiya me ya sameki kike kuka? Fadima meya faru momy ke kuka?" Kafin na bashi amsa wannan bawan Allahn da naji momy ta kira da Na'im yace "Halifa?" Juyawa halifa yayi yana kallonsa nan da nan fuskarsa ta koma mamaki, kallonsa kawai yake shima yana kalllonsa, daga dukkan alamu kamar da sukeyice ta basu mamaki, zuwa can Halifa ya juyo ya kalleni yace "Fadima waye wannan? Ya akai naga yana kama Dani?" Da sauri Na'im yace "ko kuma kai kake Kama daniba dan na rigaka zuwa duniya" watsa hannu Halifa yayi yana cewa "whatever Abu mai muhimmanci anan shine waye kai menene hadina da kai?" Momyce ta katse masu maganar ta hanyar cewa "Na'im dan Allah ka tafi na gaya maka bana tare da uncle dinka dan haka ka tafi ka kyaleni rayuwata ta fara kyau karka dawomin da abinda na manta dashi" da sauri ya matsa jikinta yana cewa " Anty suwa kika manta din? Mu? Goggo, mama, abba, ko ni? Nasan ba Wanda zaki iya mantawa da kaf gidannan dan haka karma kice min kin manta damu, idan ma ke kin manta damu mu bamu manta dakeba haryanzu, Anty gaskiya ta fito yanzu kowa yasan abinda ya faru ki hadani da uncle inyi masa bayani ina son ganin uncle dina plss" haka ya cigaba da rokonta amma kememe tace masa uncle dinsa baya nan batasan inda yakeba ta kuma hanashi shiga gidan haka ya hakura ya juya ya fita, mu bamusan akan waye ake maganarba duk da ina zargin kan dadynmune amma idan akansa ake maganar meyasa momy taki barin Na'im ya shigo ga hadu da dadyn? Nikam kaina ya kulle da alama kan halifama a kullen yake.
Bayan mun koma ciki dakinmu ta wuce tace mu kyaleta she wants to be alone, dan haka mukabar Mata dakin muka koma falo nan Halifa ya tambayeni abinda ya faru na bashi labari sannan muka zauna neman shawarar yadda zamuyi menene kuma yake faruwa sannan shi wannan Na'im din waye shi?. Har dare babu abinda muka gano sannan momy bata bamu fuskar tambayaba dan haka muma sai kukayi shiru.
Da daddare bayan kowa ya kwanta momy ta shigo dakinmu ina waya da Saif ta zauna ina ganin haka nayi masa sallama na tashi zaune, kallona tayi tace "jeki kirawomin Halifa " to kawai nace nayi waje zuwa can muka dawo tare, waje muka samo muka zauna sannan ta fara magana " ina son yau zan baku labarin ko mu su waye saboda ina so ku tayani kare dadynku daga haduwa da Na'im idan ba hakaba komai zai iya faruwa dashi, bashi da ishashshiyar lafiyar da zai iya enduring ciwon kamar yadda yayi shekaru goma sha bakwai baya, dan haka inaso ku bani hankalinku sannan Ku fahimceni Ku kuma taimakeni kunji ko?" Kai kawai muka daga mata ta fara.
"Asalinmu ba yan kasarnan bane mu yan kasar Niger ne jahar Diffa a garin da ake kira da bosso. Acikin garin na bosso akwai wani attajiri mai suna Alh Ahmad mai fata, Alh ahmad yana da matan aure biyu haj rahama mai yara uku ibrahim kabir da zainab sai haj zulfa'u mai yaro daya sagiru yaran sun taso cikin gata da tarbiyya mahaifinsu na matukar sansu ya kuma tsayawa ilminsu boko da islamiyya haka haj rahama macece ta gari mai hakuri da biyayya sabanin abokiyar zamanta haj zulfa da take masifaffiya marar hakuri ko kadan. Kabir ya taso yaro mai hazaka sosai gashi da shiga rai shiyasa ma yafi kowa fada a wajen babansu sannan akwai shakuwa sosai tsakaninsa da babban yayansu ibrahim, haka yaran suka cigaba da girma yayinda arzikin mahaifinsu yake faman bunkasa a harkar safarar fatu daga kasashe daban daban kamar Nigeria chad, Cotonou da sauransu. Bayan girman yaranne soyayyar dake tsakanin Alh Ahmad da dan autansa Kabir ta kuma fitowa fili komai ya samu Kabir komai ya gani yace kabir , duk da kankantar shekarunsa amma kowanne harkar kasuwancin Alh Ahmad da Kabir a ciki wannan ya dasa kiyayyar kabir mai yawa a zuciyar haj zulfa tana ganin danta sagir da Kabir ai sa'annine shi me yasa ba'a sakashi a harkokin kasuwancin sai Kabir, koyaushe idan tayiwa Alh Ahmad mitar hakan sai yace "banda abinki haj zulfa sagir da Kabir ai ba daya bane sagir har yanzu bai girmaba abinda yakeyi ko dan karamin yaro bazaiyiba idan kina tsammanin bansan abinda yakeba to ki daina dan duk na sani na kyale shine kawai nayi shiru, amma yaronda har shaye shaye yakeyi kike tsammanin zan dora akan dukiyata?" Wannan magana ba karamin kona ran haj zulfa tayiba amma babu yadda zatayi tunda da gaskene sagir babu abinda bayayi shine shaye shaye shine neman mata duk shi kadai kuma tasan Kabir komai hassadar mai hassada sai dai yayi karya amma Kabir mutumne."
" haka rayuwar gidan ta cigaba kullum arziki na kuma bunkasa a haka har Ibrahim ya tashi yin aure aka hada dashi da zainab a lokaci daya itama ta sami nata mijin babban ma'aikaci a niemey, nan akasha shagalin biki, a wajen bikinma ba karamar bajinta Kabir yayiba su sagir kam sai hadiyar zuciya kawai da yakeyi, bayan biki rayuwa ta cigaba da tafiya yadda ya kamata. A cikin gidan akwai wata me aikinsu dattijuwa wadda suke Kira da goggo, goggo macece mai mutunci da hakuri ga aiki tamkar inji, tana da yarinya yar autarta wadda tazo da ita mai suna kubra tare suke zaune a kewayensu dake bayan gidan, kubra yarinyace mai ladabi da biyayya ga sanin ya kamata kamar mahaifiyarta, babu wanda yasan yadda akai sai ganin Kabir akai da kubra na soyayya hakan ba karamin faranta ran iyayensu yayiba yayinda ran sagir ya kuma baci domin duk duniya babu abinda yakeso kamar kubra, ada duk abinda mahaifinsu ke yiwa Kabir bai fiya damun sagir ba amma fa wannan karan akan kubra yaci alwashin ganin bayan Kabir to ta halin kakane.
ČTEŠ
Fadimatu
FanfikceLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...