Chapter 36

53 5 0
                                    

Bayan mun fito daga dakin Saif na zauna a falo ina jiran zuwan yaya Na'im, inanan zaune su maryam da Abdul suka shigo ya daukota daga makaranta, da sauri ta wuce daki tana cewa "yauwa alhmdulillah naji dadi da baku tafiba bari na watsa ruwa kafin yazo yadda zan samu rakaku airport" murmushi kawai nayi mata da yake sauri take har ta wuce ciki, Abdul ne ya zauna kujerar dake kallona yace "yadai naga idonki yayi ja kamar wadda tayi kuka me ya faru" nan da nan dama kamar mai jira sai hawaye, da sauri na saka hannu na rufe fuskata ina sheshshekar kuka sai da nayi mai isata sannan na dago kai ina goge fuskata nace "Abdul dan Allah wata alfarma nake nema a wajenka" idanunsa sunyi jajawur jijiyoyin kansa sun tashi alamar shima kukan yakesonyi yana daurewane kawai. Yana kallona yace "alfarmar me" na sake goge fuskata sannan nace "Abdul dan Allah karku share dakin Saif ina da kyakykyawan zato akan yana raye kuma zai dawo bazaiji dadiba idan yazo yasan mun sadaukar da dawowarsa, sannan idan aka share dakin kamar mun hakura dashine zamu daina nemansa da sakaran dawowarsa" ajiyar zuciya Abdul yayi sannan yace "Fatima bawai mun hakura dashi bane babu yadda zamuyine Saif tamkar yan biyuna yake tare muka sha nono tare aka yayemu mukayi makaranta daya bamu taba rabuwa ba sai da ya tafi Kaduna kinsan kuwa babu Wanda mutuwarsa zata daka Irina sannan share dakinsa baya nufin na hakura dashi na daina nemansa ko sakaran dawowarsa, amma babu yadda zanyine I'm helpless bazan iya binsa dajin da yakeba balle na nemoshi, sannan fatima idan kaddara tasa ya rasu bai kamata mu cigaba da barin dakinsa a hakaba saboda aljanu da shaidanu na amfani da irin wannan dakunan shiyasa akeson a budeshi at least a rinka shiga sannan a kwashe pics din dakin kingane? Zamu cigaba dayi masa addu'a idan yana raye ubangiji ya bayyanashi idan kuma ya rasu Allah ya jikansa" hawayen fuskata na kuma gogewa ina cigaba da sheshsheka na daga masa kai kawai, nan ya tashi ya shiga dakin nasa zuwa can ya fito da wannan zanen nawa ya mikomin, kallonsa na tsayayi yace "ki karba ki tafi dashi dama ke ya zanawa zai kaiwa kuma Allah baiyiba" ina karba nace "dama ya iya zane?" Murmushi Abdul yayi yana zama yace "sosai ma kuwa ya iya zane tun yana yaro" kai kawai na kada mukayi shiru dagani harshi, da alama duk tunanin Saif mukeyi. Bayan wani lokaci yaya Na'im yazo dan haka nayiwa mama sallama sannan su Abdul da maryam suka rakamu har airport, da zamu tafi maryam ta rungumeni tana cewa "yanzu sai yaushe zamu sake ganinki fatima" nace "sai Saif ya dawo" bata fuska tayi tace "bazaki kuma zuwaba kenan?" Nace "shi bazai dawoba kenan?" murmushi tayi tace "shikenan Allah ya dawo dashi lafiya" na amsa da "ameen" sannan mukayi sallama muka wuce wajen screening.
Ranar da muka dawo gida kowa yayi murna kamar zasu cinyeni musamman feena da bamu taba kwana ko daya ba tareba tunda muka dawo daga Korea balle yanzu har wata uku bama tare, Nima nayi murna sosai da dawota cikin dangina, ina shiga dakinmu na dora pic din saif  kan side drawer din gadona yadda ko juyi nayi zan rinka ganinsa. Bayan dawowata na cigaba da zuwa lesson dina kuma alhmdulillah yanzu ina jin French sosai dan dashi muke magana da su Rufaida da yaya Na'im saboda na iya sosai, ana fara bada admission a  Abdou Moumouni University zinder yaya Na'im ya nemamin admission nayi applying mass comm, yaya Na'im yayi tayimin dariya wai dama wannan dan banzan surutun nawa sai mass comm din, ban kulashiba yayi ya gama. Nayi sa'a kuwa admission list na fitowa sai ga sunana ya fito nan na fara shirye shiryen tafiya makaranta, alokacin Shanghai ma suka turowa Halifa acceptance dan haka ya fara nasa shirin shima duk da nasa ta internet yakeyin komai sabanin ni da sainaje makarantar, duk sanda zanje yaya Na'im ke kaini su Rufaida kullum fada suke ba karamin sa'arsa nakeci ba da yakemin kirki, sukance wai nazo a ancanja shi gaba daya dan da kafin mu dawo ba haka yakeba wai zafin zuciya gareshi da miskilanci nace musu "nima ya nunamin zafin zuciyar tasa ai farkon haduwarmu" nan na basu labarin abinda yayimin sanda muka fara haduwa, sunyi ta mamaki mukayi dariya muka bar maganar a wajen. Wani abu da ya fara damuna shine yaya Na'im ya canja gaba daya yanzu ba yadda na Saba dashi yakeba, bawai daina kulani yayiba ba kuma hira ya daina yiminba, duk cikin abubuwan da yakemin da har yanzu yana yimin su sai dai inaji a jikina wani abu ya canjashi na kuma kasa pointing ko menene, yanayin yadda yake kallona yadda yakemin magana da sauran abubuwa duk sun canja kuma gaskiya nafison wancan Na'im din akan wannan.
Ana ya jibi zan fara shiga lectures na tashi tun da safe na shirya dan yau zan tafi naje na karbi hostel na shirya gobe na huta jibi sai shiga lectures kawai, su Rufaida sun riga da sun koma makaranta a lokacin dan haka na fito da niyyar neman abinda zanci, ina saukowa falo yana shigowa tsayawa kawai mukayi muna kallon juna na wasu yan seconds sannan nayi saurin karasa saukowa ina wayancewa da cewa "eyyeh yaya irin wannan daukan wanka haka sai kace mail zuwa wajen budurwa?" da gaske yayimin kyau ba kadanba maybe dalilin da yasa na tsaya kallonsa ma kenan, shima gyaran murya yayi yana cewa "na zata ai baki tashiba nace kin manta yau zaki tafi ecole?" hanyar kitchen nayi ya biyoni a baya ina cewa "tab ban mantaba tun da na tashi da asuba ban komaba saboda zumudi da fargaba" dariya ya fara yimin yace "wayaga sabun shiga" nima dariyar nayi sannan na karewa kitchen din kallo ina cewa "ko ma me zanci? Nifa ba girkinba sanin abinda zancin shine matsalar" yace "ke dai kice baki iyaba" nace "kaima kasan na iya dan bazan manta lokacin da nayi abinci na aka cinyeminba kuma akayi kamar za'a dakeni dan nayi magana" dariya ya fara alamar ya tuna lokacin yace "kai mi sœur kinyi min rashin kunya a rayuwarki bansan ya akayi na rinka kyaleki ba ban taba ballaki ba" nace "saboda kasan duk lokacin da nayi maka rashin kunyar laifinkane shiyasa Kai kake tsokanata" kan worktop din kitchen din ya hau ya zauna sannan yace "birgeni rashin kunyar taki takeyi, shiyasa nakeson na tsokaneki ki fara kawai nayi ta kallon wannan dan bakin yana fitsara" da mamaki nace "rashin kunyar ke birgeka?" Shiru yayi yana kallona sai can yace "amma taki kawai kuma har yau inason naga kina fada, har yau tana birgeni sosai" mamakine ya kamani kawai na saki baki ina kallonsa shi kuma yasa hannu ya rufemin bakin yana cewa "to rufe bakin kar kuda ya fada ciki" da sauri na rufe fuska ina dariya shima yana murmushi yace "kinga idan zaki nema mana abinda zamuci ki nema mana zaki makara fa" nan da nan na nutsu ina cewa "ni wallahi bansan abinda zamuci ba" yace "debo dankali" ido na zaro nace "we are already late zakace dankali?" Yace "eh mana ba ga fryer nanba zaiyi sauri" da sauri na debo dankalin na dauko mana peeler guda biyu muka feraye tare sannan na dora sannan na dauko kwai na fasa, kafin wani lokaci mun gama komai muka dawo falo a tsakiyar falon muka zauna mukaci da tea irin na buzaye. Bayan mun gama na dauko jakata da wayata sai a lokacin nayi knocking kofar ammie tana fitowa ta rike baki "badai har kin shiryaba?" Ina murmushi kaina a kasa nace "wallahi kuwa ammie kinsan tafiyar ne da nisa" tace "hakane kam zinder ba nan ba to Allah yakare a kula dai sosai Fadima kiyi abinda ya kaiki idan zaki iya rinka zuwa weekend din kamarsu Rufaida to kema sai ki dau niyya" nace "tab ammie dama ai na fada nikam bazan iya wannan wahalar ba mutum kullum yana mota babu Hutu" tace "nima na hanasu sunki hanuwa Allah dai ya tsare" nace "ameen" sannan muka sauko tare da ita, naje nayiwa su momy ma sallama dasu Abba shima yana shirin fita uncle sagir kam har ya fice haka Abbie ma duk basanan, har bakin mota suka rakoni mukayi sallama muka wuce feena nata ihu sai ta biyoni.
Halifa da yaya Na'im ne kawai muka tafi tare, Halifa ma next week zai wuce China. Muna cikin tafiya yaya Na'im  yace "Fadima" nace "naam" yace "karkiga kin Fara university kiyi tsammanin wata dama ta samu da zakiyi abinda da bakyayi, banda kawaye da samarin banza kinji ko? Karkiga muna shiri idan kika fara kula samari fada zamuyi na gaske ma kuwa" Murmushi nayi nace "yaya Na'im kenan gwara ma kawayen zance zan kula amma kaima kasan samari bani da hadi dasu masu neman mijin aure suke kula samari" kallona yayi suna dariya da Halifa sannan ya maida kallonsa titi yace " ke bazakiyi aure ba kenan tunda baki neman miji ko" da sauri nace "noo ba haka nake nufiba kawai kaga ni ai da mijina a hannu dan haka duk Wanda na kula ya zama kamar yaudara kenan" halifa na dan murmushi yace "waye mijin naki?" Nace "Saif mana" kallona suka  kumayi sannan kowa ya dauke kai ba wanda ya kuma tankamin nima na dauko waya na fara bawa Saif labarin yau zan shiga makaranta.

FadimatuWhere stories live. Discover now