Chapter 18

74 9 0
                                    

Tun daga ranar ban kuma ganin wannan bawan Allahn ba, da alama dama customer ne dan haka na manta dashi na cigaba da harkata kamar babu abinda ya faru. Yanzu wata biyu kenan da tafiyar saif Kaduna ba karamin missing dinsa nayiba shima haka kullum yana cikin gayamin yayi missing dina. Kullum cikin gayamin kalamai masu dadi yake. Wani irin feeling nakeji akan saif ina jinsa kamar wani barin jikina jinin jikina bana iya tashi banji muryarsaba kuma bana iya yin bacci ba tare da naji muryarsaba, kullum bani da farin cikin daya wuce naji muryarsa, ayanzu na tabbatar rabani da saif tamkar rabani da ruhinane dan ina jin sonsa a zuciyata tamkar wadda akayiwa asiri, bansan lokacin da na fara sonshiba sai da yayimin mugun kamu idan na zauna bani da labarin da ya wuce na saif burina kawai ya dawo na ganshi ko naji sanyi.
Jikin dady alhmdulillah dan yanzu yana iya motsa ko'ina a jikinsa dan haka wannan juma'ar ma da muka kaishi sai suka maida masa gashin wata wata, momy kam har yanzu babu wani ci gaba banda miskila da ta zama yanzu ko ni idan batayi niyyaba batayimin magana haka zaka ganta a zaune kamar kurma tun abin na damunmu munayiwa Dr complain har mun daina tunda kullum cewa yake babu matsala babu abinda yake damunta mu kyaleta kawai.
Yau nayi dutyn afternoon karfe 9:15pm na tashi na fito ina kokarin cire uniform din jikina ina tunanin banda cikin wajennan akwai ac ai da ansha wahala a zafinnan a hada mutane da wannan uwar riga. Wata motace a gabana a harabar store din ta haskemin ido, nayi saurin kare idona da hannu ina mita amma ko alamar mai motar zai kashe fitilar babu, da sauri na zagaye ta gefe ina tsaki amma ga mamakina sai mai motar nan ya Fara yi min horn dan haka na dago kai na galla masa harara duk da tint ne glass din amma nasan dole shi ya ganni. Ina juyawa zan wuce naji ance "ban yadda ba wannan hararar kar a kuma yiwa kowa ita" da sauri na juyo ina kallon motar muryar saif nakeji, shin missing dinsa da nayi har yakai na fara hallucinating ko me yake faruwa? matsawa nayi sosai ina kallonsa tabbas shine amma anya kuwa ba mafarki nakeba? Dan na tabbatar da zatona sai na saka hannu na dungure masa kumatu, wow shine da gaske ba mafarkiba kawai na fara dariyar farin ciki shima yana dariya yace "idan kin gama tabbatarwar ki shigo mu tafi gida dare na kuma yi" ai kuwa da sauri zagaya ina murna na shiga motar nace "Yayana?" Yace "naam kanwata" na kuma cewa "Yayana" yace "naam" haka muka ringayi har sau uku nace "wai da gaske Kaine?" Yana dariya yace "baki tabbatarba har yanzu?" Nace "amma me yasa dazu da muna waya baka gayamin ka dawoba?" Yace "ai a dazun ban dawo dinba amma ko a lokacin na saka jakata a mota bayan naje office na wuto nan, kafin nazo kuma kin taho aiki dan haka muka gaisa dasu momy kawai na shiga harkata nace nazo daukaki nayi miki surprise" ina jinjina kai nace "lallai kam u surprised me, har yanzuma ji nake kamar a mafarki" haka mukayi ta hira har mukazo gida, da  mukazo ma zamanmu mukayi a mota har past 10 muna hira sai da Halifa ya leko sannan mukayi sallama ya wuce gida nima na shiga gida. Yau nayi kwanan farin ciki, har nayi bacci murmushin dake fuskata bai daukeba.
Washe garima da yamma  shi ya kaini wajen aiki, muna ta hirarmu a mota har mukaje zahra store da Zan fita yace "Fatima idan kin tashi zanzo na daukeki zamuyi wata magana kinji?" Jinayi gabana ya fadi nace "Yayana maganar menene" yake "idan na dawo kyaji" na marairaice fuska cike da shagwaba nace "please ka fadamin mana yanzu ko dan hint ne ka bani" sai da ya maida fuskarsa serious sosai sannan yace "shikenan tunda kin nace aure zanyi" nan da nan naji jikina yayi sanyi wani irin tashin hankali ya tasomin hannune kawai ban dora aka na zunduma ihuba. Cikin yanke kauna nace "yaushe?" Yace "hint kawai kikace kuma na baki dan haka ragowar maganar sai na dawo" da kyar na iya jan kafata na fito daga motar ko sallama ban iya yi masaba na wuce ciki, wani irin zafi zuciyata takeyi jikina har karkarwa yake, wato dama can false alarm yake bani ba sona yakeba? Duk wannan kulawar kawai dan yana yayanane ba wai soyayya bace? To meyasa ma na yadda da zugar zuciyata na yadda dashi? Meyasa kullum idan yana maganata yake cewa cikin abinda yakeao 'ya'yansa su gada a wajena zasu gaji dimples dina? idan dai bai shirya ni zan haifa masa suba ta yaya zasu gajeni? Ranar dai tamkar marar lafiya haka na zama daga bayama sai da sukace kawai na tafi gida saboda shirme kawai nakeyi, dan haka na fito kawai na koma gida, ina shiga gida na tarar dashi tare da Halifa suna kallon ball a falo, kallonsu kawai nayi na saki labulen nayi dakinmu su kuma suka biyoni a tare suna tambayar lafiya suka ganni yanzu? Ina jefar da jakata akan Gado nace "kaina ke min ciwo shine sukace kawai na taho gida" ina gama fadin haka nayi kwanciyata dole suka fita suka barni, zuwa can saif ya kwankwasa kofar na amsa sannan ya shigo ya zauna bakin gadon da nake, wani haushinsa nakeji kamar na rufeshi da duka dan haka nayi saurin juya masa baya. Bayan ya zauna a bakin gadon yace "Fatima kinsha magani kuwa" nace  "eh" ba tare da na juyo ba shiru yayi can yace "akwai abinda kikeson ci?" nace "aa" yace "Fatima kinsan banason ganinki a cikin damuwa ko wani ciwo plss da gaske kanki ke ciwo? Idan wani abu ke damunki ki fadamin wallahi nima duk kinsa hankalina ya tashi gaba daya, ko kinaso nima na kwanta ciwonne?" muryata na rawa saboda wani kuka da yakeson kwacemin nace "a'a babu abinda yake damuna kuma na sha magani tun a zahra" da irin wadannan kalaman ya cuceni yanzu zaizo yana kuma wani nuna ya damu dani bayan ashe yana can yana soyayyarsa da wata. Tashi kawai yayi ya fita amma ana jimawa sai gashi ya kuma dawowa ya leka fuskata na dago ido na kalleshi sai kuma yayi murmushi "na dauka kinyi bacci" Kala bance dashiba ya kuma fita ni dai har barcin ya daukeni yana zirya daga falo zuwa dakinmu bansan lokacin da ya dainaba.
Cikin bacci naji ana tashina na bude ido a hankali Halifa na gani a gabana ya dafa goshina yana cewa "kamar zazzabine ma a jikinki ki tashi kiyi sallah kici abinci sai kisha magani kinji" kai kawai na daga masa ya taimaka min na tashi zaune sannan ya fita, nima na taso na fito waje nayi alwala saif na kofar falo yana kallona inajin Halifa na ce masa "wai ka fasa fitarne? ba unguwa kace zaka da la'asar ba?" Ji nayi gabana ya kuma faduwa wato zance zashi kenan ko? Ya bawa Halifa amsa da "na fasa zuwa baka ganin kanwata ba lafiya?" Shidai halifa dariya kawai yayi yace "dama bakayi niyyar zuwaba amma banda haka ai ba a kwance takeba kuma ba ita kadaice a gidanba" shidai bai kuma bashi amsaba har na shige daki sannan najishi shima ya koma falon. Bayan nayi sallah na fito falon na tarar ya siyomin fruit da magani nadanci kadan nasha maganin, Halifa yace "to tunda ga mai jinyanan nidai Bari na fita da dady idan yaso ma biya ta islamiyyarsu feena mu taho da ita " to kawai nace ya fice saif kuma ya cigaba da lallashina akan na kara fruit din amma naki ni baisan ma irin haushinshi da nakejiba abinda yake. Haka yayi ta fama dani har bayan magriba sannan aka kirashi a waya ya tafi gida.
Yau da wuri na kwanta saboda wani zazzabi dake nukurkusar jikina, bayan na kwanta saif ya kirani ina dauka yake "kanwata ya jikin?" Nace "da sauki" yace "bakisan yadda nakejiba wallahi kamar na dawo, banason naji wani abu yana damunki har zuciyata nakeji wallahi" da yana gabana tabbas da zan iya kwada masa mari wai har zuciyarsa? Hmm rainin hankali ma kenan. Can ya cigaba "kanwata nace zamuyi magana bamuyiba gashi gobe nakeson komawa aiki kuma gashi baki da lafiya yanzu ya za'ayi" cike da fargaba nace "nima ban saniba" yace "to ina jin yadda za'ayi muyi maganar ta waya duk da tafi karfin wayar idan yaso gobe idan jikin yayi sauki sai na tafi idan kuma babu sauki sai na hakura dan banajin zan iya tafiya na barki a haka" dan Allah wani ya toshe masa baki shin dole sai ya bani labarin auren da zaiyi? Sai ya bani labarin soyayyarsa? Ya barni naji da abinda nakeji mana, Amma babu yadda zanyi dole nace "ina jinka" shiru yayi kamar bazaiyi maganaba har na fara tunanin ko qayar ta kashene zuwa can kuma naji yace "Fatima kinsan menene soyayya?" Ji nayi kamar da gayya ma yakemin abinda yakeyi, soyayyarsace fa ta kwantar dani yanzu amma yana tambayata idan nasan meye soyayya, sai dana hadiye wani abu dake shirin tafiya da numfashina sannan nace "me yasa ka tambaya?" Yace "saboda tayimin mugun kamu idan ba wanda ya santaba ba yadda za'ayi ya fahimceni" "hmm" kawai nace masa dan bani da abin fada, ina fatan dai idan yaji na daina numfashi zaiyi saurin sanar da dan uwana dan a rate din da zuciyata ke bugawa zan iya mutuwa a kowanne second. Can na jiyo muryarshi yana fadin abinda ya kusa karasa daukemin numfashin gaba daya "Fatima ba karamin kamu soyayyarki tayimin ba ina jin kamar zuwa nan da dan lokaci Zan iya haukacewa saboda yawanta, tun ranar Dana fara ganinki na fara sonki a lokacin na fahimci gaba dayanku a zuciye kuke bazaku taba fahimtataba shiyasa na rike kayata saboda bana son rasaki ko na second daya, na cigaba da rainonta ina dakon lokacin da zan iya gaya miki amma na fahimci iya limit din hakurina kenan bazan iya koda bacciba idan ban fadaba, nasha kwana ina tunaninki babu bacci ko kadan babban tashin hankalina shine idan na tuna zaki iya cewa bakya sona ko kuma ki fara son wani a rashina tunda yanzu bama tare, wannan shine babban tashin hankalina dan Allah Fatima karkice baki sona na yadda kice zakiyi tunani ko in baki lokaci zan iya zaman koya miki son nawa amma idan kikace baki sona zan iya mutuwa wallahi" shiru mukayi dagani harshi, Allah dai yasa baya iya jiyo bugun zuciyata dan yadda nakejinta tabbas feena da idonta biyu sai taji. Can yace "Fatima kiyimin magana mana please kinji?" Bansan lokacin da na kashe wayarba na kasheta ma gaba daya sannan na tura kaina cikin filo, wata muguwar kunya na lillibeni tare da farin ciki, da sauri na tashi zaune ina cewa 'Allah dai yasa bai gane halin dana shiga yauba kai wannan abin kunya da yawa yake' nayi saurin sake rufe fuskata da filo ni kaina kunyar kaina nakeji ba irin zagin da banyiwa budurwar da yakeso ba dazu ashe kaina nake zagi rashin sanima dai baiyiba.
Washe gari da wani irin farin ciki na farka duk gidan sai da suka fahimci ina cikin farin ciki. Na shirya feena yau Monday muka fito zamu tafi ina bude kofa na ganshi tsaye jikin motarsa yana facing kofar gidan, wata muguwar kunyace ta rufeni nayi saurin sa hannu na rufe fuskata ina jin feena na gaisheshi sannan ta dawo tana jana "sister ki taho mana zan makara fa" ina iya hangoshi ta tsakanin yan yatsuna ya baro jikin motar yazo dab dani sannan yace "saifeena wai sister dinki kunya takeji yanzu ya za'ayi kenan?" Feena tace "to meyasa takejin kunyar?" Still ina iya feeling idonsa a kaina yace "saboda jiya ta aikata babban laifi ta kusa kashe dan Adam" da sauri na bude idona ina cewa "kisa kuma?" Yace "eh mana bakisan kashe wannan wayar daidai yake da tsayar da bugawar zuciyataba? Banason mutuwa ban kuma ganinkiba shiyasa na kokarta ban mutumba kuma nazo nan ina jiranki yadda zan mutu a daidai" da sauri na zagayeshi tare da kama hannun feena muka wuce, ya daga murya yace "menene ansata?" Juyowa kawai nayi nayi masa murmushi mukayi gaba.
Ranar ba karamin wunin farin ciki nayiba haka yan zahra ma sukayi ta tambayata me ya faru sai dai kawai nayi murmushi, bayan na dawo na tarar Halifa ya tafi dan haka bamu hadu dashiba sai da daddare bayan ya dawo, har daki ya biyoni muka zauna muna hira bayan mun gama cin abinci, can sai cewa yayi "lallai Fadima wato soyayyata dake akwai limit ko?" Da sauri na kalleshi da mamaki nace "limit kamar yaya Halifa dama soyayya nada limit? Musamman ma wadda nake maka?" Ya bani amsa da "gashi kuwa da labari a bakinki amma kinki gayamin saboda son da kike masa yafi nawane ko me ya faru ban saniba" na kuma fahimci inda ya dosa dan haka na rufe fuskata da sauri ina dariya, shima dariyar yake yace "oya to fadamin kina sonsa?" A hankali na daga kai nace "sosai ma " nan ya fara dariya "eyye yar kanwata an girma mu ganta" nidai dariya kawai nake ina rufe fuska can nace "to wai waye ma ya gaya maka?" Yace "idan ke kinki gayamin kina zaton shi zaiki fadaminne?" Kafin na bashi amsa naji wayata na vibrating dan haka na mike da sauri na daukota akan gado koban dubaba nasan me kiran dan shi kadai ke kirana dan haka ina dauka na fada kan gadon sannan na amsa tare da juyawa Halifa baya. Tashi yayi yana dariya yana hada kayan da muka gama cin abinci yana cewa "shikenan tunda soyayya za'a fara Bari kiga nayi nan sai da safe" hannu kawai na daga masa ya girgiza kai ya fice. Munsha hirarmu ta soyayya sai a lokacin nace yaya ban ganshiba gaba daya yau? Shine yace ai daga gidanmu ya wuce kd. Haka mu kayi ta hirarmu danma idan ya hau layin soyayyar shi kadai nake bari yayi kidansa yayi rawarsa amma duk da haka sai da muka kai 12am sannan mukayi sallama tunda gobe kowa yana da wajen zuwa da safe.

FadimatuWhere stories live. Discover now