A yanzu kudin da yayi saura a hannunmu bai wuce kudin da za'a siyawa su momy maganiba ga kayan abincinmu ya kusa karewa, rannan ina zaune a tsakar gida ina yiwa momy tsifa Halifa ya shigo zama shima yayi kusa da momyn sannan ya kalleni yace " Fadima shawara nakeso muyi dake" nace "shawarar me?" Ya gyara zama yana kallona ya cigaba "kinga kudin hannunmu yanzu zanje na siyowa su momy magani dashi idan yayi ragowa sai a karo wani Abu a kayan abincin idan kuma baiyi ragowaba sai mu lallaba abinda mukedashi a yanzu ina tunanin Zan fara neman aiki ko dakone tunda kinga zaman a haka bazai yiyuba gashi har mun cinye kudin tunda dauka kawai akeyi ba'a sakawa kuma banajin wani zai daukeni aiki da secondary certificate dan haka dole sai dai aikin karfi amma ya kike gani" na share hawayen da ya biyo fuskata cike da takaici wai yau dan uwanane zaiyi aikin dako? Kai wannan wacce irin rayuwace sai yaushe zamu koma irin rayuwar da muka saba ne? Hannu Halifa ya dagamin tare da cewa "kinga banason wannan kukan karma ki fara, babu damar azo ayi miki magana sai ki fara kuka, Fadima kinsan ba son wannan kukan naki nakeba amma bakyajin magana, kuma idan banyi miki maganaba da wa zanyi? Da dady? Yadda zan kuma tada masa da hankali ko kuwa da momy da batasan ma wayeniba balle ta fahimci me nake fada mata? Ko kuwa Safeena kikeso na tasa a gaba nayi magana da ita? Ya kamata nima ki rinka tausayamin dan Allah" ya karasa maganar shima yana share nasa hawayen, cikin muryar kuka nace "dan Allah Halifa kayi hakuri wallahi babu yadda zanyine nima ba'ason raina nake kukanba kawai yafi karfinane, amma kayi hakuri na daina in sha Allah" na karasa ina goge hawayen fuskata, sai da na tabbatar babu hawaye ko daya sannan nayi ajiyar zuciya na fuskanceshi nace "to amma yanzu kana ganin zaka iya aikin karfin? Akwai wahala fa, ni da tunani nake ko yan gidajennan zan dinga shiga ina tambaya maybe wasu suna neman mai aiki kaga sai na dingayi musu kamar zaifi" tunda na fara fadar nawa suggestion din Halifa ya fara girgiza kai ina sa aya kuwa ya dauka" bazai yiyuba Fadima tab baki ma da hankali ta yaya Zan barki kije aikatau alhalin nasan me ake yiwa yan aikin? Over my dead body, kawai ki bari zan iya zan gwada idan naga bazan iyaba sai na nemi wani aikin, abinne sai a hankali beside yan unguwar basu sanmuba dabadan hakaba ko jiran shago ai zan iyayi to kinsan sai an yadda da amanarka ake baka irin wannan" shiru mukayi na wani lokaci can nace "to Halifa ko irin awararnan ko wainar fulawa zan dingayi a kofar gidannan muna samun wani abin?" Kallona yayi da wani murmushi yace " kamar iya awarar kikayi" sai a lokacin na tuna ashefa ban iya awararba ai kuwa mukasa dariya gaba daya har da momy da batasan hirar me mukeba, bayan mun gama dariyar nace "amma idan ban iya awaraba ai na iya wainar fulawa ko?" Yana wani murmushin yace "harda kimci" nan ma dariya muka kumayi dan na tuna lokacin da na rinka koyar girkegirken Korea Allah sarki Korea kamar bamujeba, friends Dina ma har na manta dasu rayuwa tayi zafi, Halifa na kalla nace " kai Halifa na yadda babu best teacher a duniya irin rayuwa kasan rabona da kallon Korean movie kuwa?" Yana mikewa yace " ko kinaso na samo miki?" Dariya kawai nayi ban bashi amsaba sannan yace bari na duba dady ko yana bukatar wani abun" da sauri nace "yauwa Halifa kana ganin baza'a samowa dady wheelchair ba kuwa? Shima a dinga fitowa dashi waje yana dan shan iska?" Sai da yakai kofar dakin sannan ya bani amsa da "kudinne kawai matsala amma zan ga yadda za'ayi ko taimakone sai mu nema ko za'a samu" kai kawai na daga masa na fara taje ma momy gashinta dana gama tsefewa, kan momy na bukatar wanki amma bazan iya wanke mataba idan ba relaxer aka saka masaba saboda cikarsa da tsahonsa dan haka bansan yadda za'ayiba.
Washe gari Halifa yaje ya fara neman aikin dako ganinsa da kwanji yasa akayi saurin daukarsa sunyi tsammanin karfine dashi (da yake dady da Halifa gaba daya jikinsu a mummurde yake kamar wasu yan dambe) sai da yamma tayi sukaga ba wani abin arziki yayiba sukayi ta fada, haka ya dawo gida yayi ta ciwon jiki harda su ruwan zafi, washe gari kuwa yana komawa suka fara yi masa zille zille wai babu aiki an riga an bawa wani haka ya hakura ya tafi wani shagon ranar dai har yamma ya dawo bai sami wani aikin arzikiba, haka rayuwar ta cigaba da juyawa har kayan abincinmu ya kare gashi aikin halifan yayi wahala baya samu ko ya samu ba wani abin arziki yake samuba.
Ranar wata juma'a tunda muka tashi da safe bamu da komai sai taliya kwaya daya ko mai da yaji babu dan haka na tafasa mana ita muka sami naira 50 a hannun Halifa muka siyo mai da magi muka cita, sai da muka bari dady momy da feena suka koshi duk da dady ba fiya cin abincin yake sosaiba, wadda suka rage muka samu mukaci ni da Halifa bayan mun gama yace "Fadima bari na fita nagani ko zan samo mana wani abun kinga dole a nemi abincin rana dana dare" to kawai nace masa sannan ya juya ya fita. Tun muna jiran Halifa zai dawo har la'asar babushi ba alamarsa, feena da momy sai kuka sukemin yunwa sukeji tun ina basu hakuri har nima na saka kuka bansan yadda zanyiba bani da abinda zan basu suci bani kuma da yadda zanyi dasu, na shiga daki na fito yafi a kirga tunanina kawai me zan daga na siyar? Kaf gidan duk abinda na kalla sai na ayyana na dagashi na siyar amma sai na tuna bani da wanda zan kaiwa ya siya bansan inda zani na siyarba, tun feena da momy na bina duk inda na shiga suna kuka har suka hakura sukayi bacci kan kafet a tsakar daki, ina shiga bedroom naga dady ma na hawaye da sauri naje kusa dashi ina goge masa hawayen nace "ayya dady kaima yunwa kakeji ko? Kayi hakuri Halifa ya fita tun dazu nasan in sha Allah zai samo abinda zamuci ya kusa dawowa kayi hakuri kaji" girgiza kai yayi tare da cewa "ko daya Fadima ba yunwa nakejiba ina kukane saboda na zama marar amfani, rayuwata bata da amfani ina raye amma dana dan shekaru 18 shine keyin dako maimakon karatu, duk wahalar da kuke ciki babu yadda zamu iya taimaka muku dagani har momynku sai ma kara muku nauyi da mukayi, kuyi hakuri Fadima kuyi hakuri" maganganun dady ba karamin tausayi suka baniba ina kuka nima nace "dady ka daina fadar haka, karkayi sabo babu wanda zaice rayuwarsa bata da amfani duk yadda ubangiji yayi dakai da manufarsa tayin hakan ka kwantar da hankalinka komai zai koma yadda yake da izinin Allah kuma ku ba nauyi bane dady babu abinda bazamuyi mukuba kamar yadda nasan babu abinda bazakuyi manaba idan da mune a halin da kuke dan haka dady ka kwantar da hankalinka in sha Allah yanzu Halifa zai dawo kaji?" Kai kawai ya dagamin na kuma koke masa hawayen nace "ka daina kuka kaji dadyna" kai ya kuma dagawa yana murmushi nace "yauwa that's my dady Bari na koma wajensu momy karsu farka kasan halin matar taka" wani hawayenne ya kuma zubo masa yace "sai na gaya mata" da sauri na tashi na fita na shige dakinmu ni da feena na fada kan gado kuka nayi sosai dan na tuna lokacin da muke gulmar momy is so stubborn dady yace sai ya gaya mata gaya matan da har yau bai sami damar yi ba kenan.
KAMU SEDANG MEMBACA
Fadimatu
Fiksi PenggemarLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...