chapter 07

128 13 0
                                    

Bayan shigarsu office doc ya kalli momy bayan ya zauna a kujerarsa ya kuma nuna mata kujera itama ta zauna sannan yace "haj na gaya miki shima na gaya masa last time da kukazo nan idan bai rage tunani yana kuma hutawaba komai zai iya faruwa, yanzu gashinan abinda nakeji din ya faru I'm sorry to say muna suspecting  cerebrovascular accident ya samu Wanda yayi causing stroke" da sauri momy ta toshe bakinta da hannayenta dukka biyun hawaye na zubowa daga idonta, shikansa Dr sai da ya ajiye zuciya kafin ya cigaba" sannan ga matsalar zuciyarsa kullum kara worst yakeyi, yanzu sai dai ku tayamu da addu'a Allah yasa bai samu paralyzed ba saboda bazamu iya ganewaba sai ya farfado sannan jikinsa ya koma normal, Allah dai ya kiyaye ya kawo komai da sauki" a hankali momy ta goge hawayen da take ambaliya a fuskarta sannan ta amsa da muryar da ita kanta sautin bai Kai kunnentaba balle ta saka ran shi zaiji.
Bayan momy ta fito daga office din Dr ta tarar dasu fadima har yanzu kuka suke sai dai na yanzu hawayene kawai ke zuba amma babu karfin fitar da sauti, tana zuwa ta zauna kusa da fafima tare da riko hannunta cikin taushin murya ta fara magana "halifa Fadima dan Allah ya Isa haka kukan kowa ya share hawayensa yanzu dadynku ba kuka yake bukataba addu'arku yake bukata kuma ita ya kamata kuyi masa Allah ya bashi lapiya ya dawo cikinmu sannan ya warware masa duk wata matsala da yake fama da ita" Fadima ta share hawayenta sannan tace cikin muryar kuka  " momy dan Allah Dan annabi ki gaya mama me yake damun dady? Me ya sameshi? Muna bukatar sani me Dr yace miki" wani murmushi momy tayi irin mai ciwo dinnan sannan tace " Fadima ki kwantar da hankalinki boye-boye ya kare zan gaya muku abinda yake faruwa amma yanzu kuje gida ku huta kuci abinci idan kuka dawo sai na gaya muku, OK?"  Da sauri suka girgiza kai a tare " no momy bazamu iya tafiya mubarki ke kadai anan ba gaskiya bazamu iyaba" "ni kuma bazan fada muku komaiba sai kunyi abinda nace" da sauri halifa ya sauko kasa kusa da kafafunta ya dafa gwiwarta sannan yace "momy baki ganeba bawai saboda labarinne bazamu iya tafiyaba no saboda babu abinda zamuyi a gidan alhalin ku kunanan a asibiti, bazamu iya yin komaiba dan haka dan Allah ki barmu anan kinji?" Sai da ta dauki wasu seconds sannan tace " shikenan ku zauna amma idan dare yaja dole ku tafi gida".
Bayan wani lokaci Dr ya barsu suka shiga dakin da dady yake amma da sharadin bazasuyi hayaniyar da zata iya tashinsaba, sai a lokacin suka samu sukayi sallar la'asar suka jira akayi magriba ma sukayi sannan momy ta fara fada musu abinda yake faruwa:
"Kamar yadda kuka sani dadynku yana business ne na kayan sakawa yana da shaguna da yawa a kasuwanni da yawa Wanda yake business dinsa dasu, so akwai wani customer dinsa da suka saba sosai dashi wata rana sai yake bashi shawara da ya fara business na motoci, sun dade suna maganar ni kaina yasha zuwa ya gayamin ya nemi shawarata, tun Ina ganin abin ba mai yiyuwa bane har da yadda a lokacin kuna Korea, dan haka dady ya dauki kudi masu yawa ya bashi ya tafi dasu America a cewarsa kusan fin rabin rayuwarsa a can yayita dan haka zai iya turo musu motoci direct daga can, bayan tafiyarsa ya turo motocin an kuma siyardasu nan da nan da yake masu kyaune, ganin irin ribar da suka samu sai abin ya yiwa dady dadi dan haka ya saka gaba daya shagunansa a kasuwa da duk wani hannun jari da yake dashi ya hada kudinnan ya turawa mutuminan Wanda shi yana can American bai dawoba, ban taba kukan rashin dangiba sai a lokacin saboda bansan lokacin da ya aikata hakaba Dana sani dinma nayi masa magana amma sai yakiji ya rifeni da fada akan na dinga kyautata zato, gashi bani da Wanda zanje na gayawa ba uwa ba uba shima babu nasa dangin balle nakai kararsa, kuma bakwanan balle na gaya muku mu hadu mu rokeshi kozai fasa, haka inaji Ina gani ya bada kudinnan babu yadda zanyi tamkar wanda akayiwa asiri, babu abinda ya rage a kudinnan bayan wanda yaje yasai wani makeken fili aka zagayeshi aka gina offices da komai wanda nanne zai zama wajen sayarda motocin, ya yiwa wajen register an gama komai sai motoci ake jira, amma sai me babu motoci babu kudin motoci, da farko idan ya kirashi yana dauka idan yayi masa maganar yaushe zai turo motocin sai yace ai sunada yawane saboda haka paperwork din da za'ayi ba Dan karami bane dole abin zai dau lokaci to daga bayama sai ya daina samunsa ma kwata-kwata, babu irin neman da baiyi masaba abu kamar wasa yanzu shekara guda kenan kullum yana hanyar nemansa, ya siyar da wancan filin har american ma yaje yaje companyn da fari sukaki kulashi saboda abinda yake nema ya sabawa customer privacy na companyn sai daga baya bayan ya samu Wanda ya sani sukayi cuku-cuku aka duba masa report na companyn nan yaga tabbas wannan bawan Allan ya yi signing papers da yawa na siyan motocin amma bai kai ga biyan kudinba kuma an nemeshi an rasa, sune asibitoci gurin yan sanda babu inda basu nemaba amma babushi ba alamarsa a America baki daya haka ya dawo, to tun dawowarsa komai ya lalace kullum yana hanyar neman mutumin nan shine wajen ambassador shine wajen malamai ayi masa addu'a ahaka ragowar kudin da yake dashi ya kare, dawowarku daga makaranta ma gidansa na shago tara ya siyar yayi mana kudin jirgin zuwa da duk wasu formalities na makarantar duk da bai samu kudin biya miki ragowar shekararki dayaba amma kullum maganarsa kenan komawarki schl dalilin da abin NASA ma ya zama worst kenan, yanzu ya saka gidanmu da muke cikima a kasuwa saboda kudin makarantarki sannan yanaso ya fara wani business din ko yayane sai kuma wannan abu ya faru" a hankali ta saka hannu ta goge kogin hawayen dake fuskarta, zuwa wannan lokaci Fadima sai da ta toshe bakinta da hannu bibbiyu saboda kukan da take haka halifa ma kuka yake sosai cike da tausayin mahaifinsu, bayan momy ta lafa sai ta cigaba " bansan wayar ne akayi masaba amma nasan bazai wuce maganar mutuminba dama kuma tun tuni jininsa ya hau dan munsha kwana a asibiti kafin ku dawo saboda hawan da jinisa yayi sannan ga ciwon zuciyar da yake dashi tun asali, yanzu likita ya gayamin sai dai kawai muyi adda'a amma suna suspecting paralyze" ta karasa maganar muryarta na rawa sosai cike da tashin hankali, zuwa yanzu Fadima har wani shidewa take jin abinda ya samu dadyn dinsu, batason wani abu ya faru da dady. Haka suka hadu su hudu suka sha kukansu kamar idonsu zai tsiyaye, da dare yayi kuwa kasa tafiya gidan sukayi haka suka kwana suna sallah suna gayawa mai duka, ba wai sai kudinsu ya dawoba ba Dan basu damu da wannanba lafiyar dady kawai suke roka har gari ya waye, nan momy ta tilasta musu komawa gida Fadima ta hada Mata breakfast halifa ya kawo mata suma sukaci nasu, sai a lokacin suka samu sukayi bacci shima ba wani na arziki ba bayan la'asar suka koma asibitin ita kuma momy ta taho gida ita ma ta samu tayi wanka tayi bacci, karfe goma ta koma Fadima halifa da feena suka dawo gida. Haka suka cigaba dayi har kwana biyu still dady bai farkaba, a ranar ne kuma Wanda zai sai gidansu yazo akayi ciniki da komai a gaban halifa da momy ya basu kudinsu cash. Nan momy ta rokeshi akan ya basu ko 2wks ne saboda su sami wani gidan su kuma kwashe kayansu ba musu kuwa ya yadda ya basu 2weeks din. Bayan tafiyar mai siyan gidan momy ta tambayi dillalin da ya kawoshi ko zai samo musu wani gidan da zasu iya zama? Dan karami amma, nan yace ba matsala akwai gidaje ma a hannunsa, dan haka ya daukesu suka je gidajen da yakeda su a hannunsa, a karshe dai Wanda suka zaba karamine sosai dan saida halifa yaki amma sai momy ta nuna masa ba matsala zasu iya manage saboda kudin akwai abubuwa da yawa akansu sannan kuma na wani lokacine kadan in sha Allahu everything is going to be alright, dan haka ya hakura aka fara cinikin gidan, gidane dan karami da dan dogon soro da daki a cikin soron sai kuma ciki dan tsakar gidan dan madaidaici da dakuna ciki dai-dai guda uku sai kicin da bandaki suma a tsakar gidan da wani ban dakin a dakin soro, kaf gidan sumintine bandakunanne kawai masu tiles, babu maganar a.c kuwa ko wani abin more rayuwa kamar yadda suka saba tun tashinsu.
*Rayuwa kenan* .

Follow me on my wattpad @maman saifeena

Fadimatuजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें