Washe gari tun asuba na farka amma kafata taki takuwa, tun ina kokartawa had na hakura inaji a masallaci ana sallah ba damar tashi, had saida gari ya fara wayewa sannan na samu na rarrafo da kyar nayi alwala nayi sallah, ai kuwa a wajen na kuma zubewa, dai wajen 8 Halifa ya shigo yana tambayar ya yaga Yau feena ba zata school ba? Da yake dama shi yake kaita idan na gama shiryata, nan na gaya masa bazan iya tashiba kafata ciwo take shiyasa ban tashetaba tuntuni. A ranar dai halifane yayi mana girki dayake ma Allah ya taimakemu da ragowar kudin jiya a hannunsa sai kawai ya siyo mana bread ya dafa shayi, sai da ya bawa kowa nasa , ya bawa day ma ya tabbatar ya koshi sannan yazo ya tasani a gaba nima sai da ya tabbatar naci sannan ya fita kasuwa.
Ganina a kwance sai gaba daya jikin momyma yayi sanyi tazo itama ta kwanta a gefena it a kuwa feena tanacan ta tasa dady a gaba da surutu daga dakinmu ma ina jiyo surutunta, can wajejen 12 na jiyo sallama a soro kafin na yunkura feena tayi waje da gudu dan haka na kyaleta kawai ta dubo ko ways, zuwa wasu yan mintina naji bata dawoba sai kawai zuciyata ta bani an saceta, wani karfi naji yazomin gaba data ai kuwa na mike na manta ma da qai kafata tana ciwo nayi waje da sauri, ina zuwa wajen na gansu ita da wani mutum tana tsaye shi kuma yana tsugunne yadda tsahonsu zaiyi daya suna magana amma ban Kai ga jin me suke cewaba, ina fita yayi saurin dago kai yana kallona, yadda ya kafa min ido yasa na fahimci ba mayafi na fito dan haka nayi saurin kunce na kaina (dayake mayafin doguwar rigane a kaina) na yafa sannan na Fara kokarin komawa gida ina cewa "feena zuwa duba sallamar kenan ko?" Ba dashi nakeba amma shi ya bani amsa "gaisawa muka tsaya yi tunda tasan yayarta da yayanta bazasu tsaya mu gaisaba" sai da yayi magana na ganeshi dan haka na juyo da sauri ina kallonsa, jiya kwata kwata ban kalli fuskarsa yadda zan ganeshiba sannan kuma dama ina da matsalar gane mutane ban fiya saurin rike fuskaba, a hankali na sunkuyar da kaina ina fadin "ayya sorry wallahi ban ganeka bane ina kwana" instead of ya amsa sai cewa yayi "ashe kafar tayi tsamin? Dama jiya Dr yace zatayi tsami" ya baro jikin motarsa inda da yake yazo ya tsugunna a gabana yana kallon kafar sai da na danyi baya sai kuma ya mike yana kallon cikin idona yace " ko zamu koma asibitinne? Naga kamar ta tumbura ko?" A zuciyata nace 'ko a ina yaga ta kumburan oho kafa a cikin zani' amma a fili kawai cewa nayi "aa basai munjeba ba wani kumburi tayinba kuma wa ma yace maka tayi tsami? Babu abinda tayi" da murmuahi ya juya yana kallon feena tare da mika Mata hannu tayi saurin kamawa ta taho wahensa yana cewa kanwata ta gayamin ai Yau saboda kafarki na ciao bazaki iya shiryataba shiyasa bataje makarantaba ko saifeena" da sauri tace "eh hakane saifeena" da mamaki nace "meye kuma saifeena?" Suka kalli juna ya mika mata hannu suka tafa sannan yace "sunanmune" nace "ohh feena kinji wani wajen daga ganin mutum har kin saba dashi saboda surutu, to me saifeenan yake nufi?" Da sauri feena ta bani amsa da " saif + safeena = saifeena" na kuma cewa "to wa kuma kika samu said?" Kawai wai sai ganjn mutum nayi ya dafe kirji wai "ashsh it hurts, yanzu baki san sunana ba?" Ba karamar kunya najiba sai yanzu na tuna tabbas bai gayamin sunansaba ni kuma ban tambayaba. Muna cikin haka na jiyo momy na kirana nace " oya feena wuce muje ga momy can na nemanmu, amm Mal na gode sosai da kulawa kuma naji sauki basai ka kuma zuwaba na code" na mikowa feena hannu da niyyar ta Kama lmuje gida sai cewa yayi "bakison ganina shiyasa kikace haka ko?" Da sauri nace "no ba haka bane kawai wai kaga basai ka dinga takurawa kankaba na tunda na warke" maimakon ya tafi sai cewa yayi "to idan no kuma ni kuma inason ganinki fa?" Da mamaki nake kallonsa nace "me yasa zakaso ganina?" "Saboda ina sonki" baki kawai na bude ina kallonsa sai yayi saurin sunkuyawa wajen feena yace "ina sonki saifeena kema kina sons" ai kuwa ta fara tillika dariya da gudu ta taho wajena "yaya fadima wai saifeena yana sona nima ina sonsa ko?" Tsaki kawai nayi naja hannunta mukayi cikin gida.
Bayan kwana biyu kafata ta warke sumul kamar banji ciwoba, rayuwa kuma alhmdulillah tana man yadda take babu abinda ya canja har yanzu dady da momy sunan a yadda suke sai sababbin abubuwa da momyn ta koya take amfani dasu, ranar wata alhamis da yamma muna zaune da Feena a tsakar gida sai ga Halifa ya dawo daga kasuwa, feena ta tashi ta taroshi ta karbo ledar hannunsa ta kawomin yana cewa "kwadayayya kayan miyane ba alawa ko wani abin Ciba" ai kuwa ta zunbura baki "brother ba abinda ka siyomin a kasuwar?" Yace "ayya sai dai kiyi hakuri na manta" kawai yarinya sai ta saka kuka, da sauri yace "kinga ungu kije wannan shagon na waje ki siyo alawar yanzunnan ki dawo kinjiko?" Da murna ta karba tayi waje ina "feena karfa ki zauna" tana fita tana cewa "to yanzu zan dawo". Zama Halifa yayi a gefena bayan ta fita yace "Fadima gobe Friday gashin dady gashi babu mota babu kudin mota, dama nayi zaton Yau zan samo wanda zai ishemu kuma ban samuba ya kike ganin za'ayi?" Nayi shiru na wani dan lokaci zuwa can nace "wallahi Halifa idear ta ta kare nima bansan me zamuyiba yanzu, amma a gidannan kana ganin ba zamu iya daga wani abu mu siyarba? A kitchen baza'a rasa abinda za'a iya siyarwaba, kaga akwai food flacks akwai coker gas kamar zata danyi daraja ko?" Yace "bawai siyarwarce matsalarba Fadima was za'a siyarwa shine matsalar kuma da nasan da hakan tun tuni da nayi tambaya a kasuwa naji ko da me siya ko Wanda yasan inda za'a iya siya" nace "to a titi baka ganin wani shago da ake saida electronic? Maybe su siya " shiru yayi zuwa can yace "gaskiya ban saniba amma zan duba yanzu tunda goben da safe muke bukatarsa" shiru mukayi dagani harshi na tsahon wani lokaci sai can nace "kaga yarinyarnan sai da nace karta dade amma sai da ta zauna tanacan tana uwar magana dan Allah Halifa dan dubo mana ita" da sauri ya mike yana cewa "wallahi nama manta da fits tayi" nan dai yayi waje can shima najishi shiru nace 'to kodai bai gantaba? Bari dai na bisu' sai kaqai na dauko hijabina na bi bayansu, ina fito na gansu tsaye tare da wannan mutumin da Halifa da feenan duk fuskarsu a hade da alama ma feena kuka take ta kuma takure jikin mutumin, da alamar tambaya nake binsu da kallo ai kuwa da gudu feena ta taho ta rungumeni tana kuka nima na rungumeta ina cewa "Halifa lafiya meke faruwa? Me ya sami feena na ga tana kuka?" Juyowa yayi a fusace zai shige gida nayi saurin kamo hannunsa ina masa kallon tuhuma kawai sai cewa yayi "idan feena ta kara fitowa waje ko na ganta da wasu wallahi sai nayi mata mugun duka banza suda fadi ba'a tambayekaba kin rife wannan shegen baking ko saina fasa miki shi? " ai kuwa ta kuma kankameni shi kuma ya juya ya nuna saif da yatsa "kai kuma wallahi ka kuma zuwa gidannan sai na wulakantaka karkaga bani da komai ko ka girmeni wannan ba zai zamemin matsalaba zan yi maka rashin mutuncibe wallahi" kafin ya gama rufe bakinsa shima saif ya dauka "kayimin duk abinda kakeso Halifa amma bazan daina zuwaba saboda inasonku fun da na hadu da kanwarka kawai something is telling me akwai dalilin haduwarmu, akwai wani abu da yasa Allah ya hadani daku sannan na kuma yadda da zargina daya sakamin sanku gaba dayanku, kwana biyun da banzoba ina ganin kamar wani mummunan laifi na aikata, sannan karka sake ka daki feena ba laifinta bane Nina tambayeta dan haka bata da laifi" nikam sun barni da kallonsu bansan me yake faruwaba dan haka nace "will you both stop it? Wa I me yake faruwa? Ina bukatar sanin abinda yake faruwa fa duk akan meye ake wannan cecekucen?" Halifa bai kai ga bani amsaba sai kawai cewa yayi "ku wuce muje gida" na kare musu kallo kawai na juya Zan shiga gidan saif yace "feena ta gayamin halinda kuke ciki" da sauri na juyo nace "what? Ta gaya maka me? To ita wannan yar yarinyar me ta sani da zata fada maka? Me tace maka" Halifa yayi saurin juyo dani yace "kyaleshi wuce muje" ganin zamu shiga gida saif ya daga murya yace "ka barta na fada mata mana indai kasan abinda feena ta fada ba haka bane? Tace min babanku ya samu paralyze mamanku tayi loosing memory sannan da a babban gida kuke yanzu kuma kuka dawo wannan gidan" juyowa kawai nayi iana kallonsa sannan na kalli feena dake zazzare ido a gefena na kifa Mata mari har sai da ta kai kasa, da gudu ya karaso ya dagata ai kuwa ta shide a jikinsa tana kuka, nima kukan na fara ina fadin "feena ashe ban hanaki surutuba? Baba hanaki ganin mutane da baki sansuba kizauna kina uwar maganaba? Yanzu ubanwa ya gaya miki duk wannan maganar? Wacce irin yarinyace ke ?" Ganin irin kukan da nake ga mutane har sun fara haduwa sai Halifa ya jani zuwa cikin gida da sauri shi kuma saif ya biyomu da feena amma sai ya tsaya a soro, muma muka tsaya a soron na kalleshi ina goge hawayena nace " wai bawan Allah me nace maka ? Ba cewa nayi karka kuma zuwa gidannanba? Meye kawoka? Bani kanwata yarinyace Kai wanne iron mutumne zaka yadda da abinda wannan yarinyar ta fada? Idan baka saniba shekararta hudu kawai dan haka kayi gaba babu gaskiya cikin abubuwan da ta fada" "momy?" Innalillahi wa innailaihir rajiun shikenan momy ta karyatani, idonsa kawai nake kallo yayinda shi kuma yake kallon bayana. Da sauri na juya na kama hannun momyn nayi cikin gida da it a na barsu a wajen sai daga baya Halifa ya biyoni da feena a hannunsa still tana kuka furkarta har ta kunbura. Bansan ya halifa sukayi da saif ba, ban kuma san shima saif din me yayiba dan bamu kuma tada zancenba kamar ma ba'ayiba amma fa kowa ka kalli fuskarsa a hade take har washe gari.
Bamu sami kudin kai dady gashiba da gari ya waye Dr ya kiramu sai kawai mukace masa bazamu sami damar kawoshiba wannan satin sai dai ko wani satin, dan haka yace shikenan Allah ya kaimu, shima dady mukayi masa bayanin babu kudin da zamu dauko hayar mota sai dai yayi hakuri zuwa wani satin shima yace ba matsala yayi ta saka mana albarka tare da adduar Allah ya buda mana ya kawo garshen wannan wahalar mukace ameen.
Ban taba ganin mutum me danbanzan naci ba kamar saif duk rashin mutuncin da Halifa yayi masa jiya yauma sai gashi ya kuma dawowa, ina zaune ina wanke wanke yayi sallama a bakin kofa, na tashi na saka hijabina na fito soro wajensa bayannmun gaisa yace " Fatima nasan jiya ranki ya baci haka halifama sannan bansan menene takamaimai ya samekuba ban kuma san dalilin da yasa nakeson sauna saniba amma abu guda data danake da tabbas shine wallahi wallahi wallahi fatima no ba mugu bane sannan kuma bada muguwar manufa na shigo rayuwarkuba bakusan me Allah yake nufi da haduwarmuba karkuyimin mummunar fassara kuma nayi alkawarin koma menene ya sameku bazan gujekuba zan taimakeku iya iyawata, gaba dayanku yarane dagake har halifan dan haka ina muku kallone tamkar kannene na mini bazan taba cutar kuba ba kuma zan Bari a cucekuba" shiru mukayi na wani lokaci mai tsaho sai daga baya na fara bashi labarinmu tunda nasan bamu kuma da wani qabu da za'a iya damfara yanzu, na gaya masa komai tun daga dawowarmu daga korea har yau babu abinda na rage masa, ina fada ina kuka domin sai yanzu da na hade abubuwan a waje daya na kuma tabbatarwa munga gararin rayuwa iri iri sai dai fatan Allah ya saukaka mana haka ameen.
YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...