Ranar dai bamu mukayi bacciba sai da aka fara kiran sallah, asubar farko kuma Na'im ya buga mana gida. Haka dole badan momy tasoba aka barshi ya shigo sai dai munyi duk yadda zamuyi mu hanasu haduwa da dady. Tun daga ranar Na'im ya samu wajen zuwa idan baizo da safeba zaizo da yamma, wata Rana ma sukazo tare da Tj babu yadda basuyi da momy ba akan ta koma gida amma taki ta kumayi musu kwakwkwaran kashedi akan idan har suka sake suka gayawa gida sun ganta to wallahi zata kuma bata.
Duk zuwanda Na'im keyi gidanmu har Yau bai bani hakurin wulakancin da yayiminba ni kuma haryau bana kulashi idan yazo sai dai suyi ta hirarsu dasu momy da Halifa nikam sai dai idan da Tj yazo shine muke hira dashi kullum yana cikin bani labarin kakannina da kannansa yan biyu da ragowar family tun ina jinsa kawai har yanzu bani da abin so irin na ganni tare da yan uwana, ya kamata momy tayi hakuri suga dady ko masan abinyi wai hausawa sukace da rashin tayi akan bar arha.
Yau nake saka ran dawowar Saif yayinda satin Na'im biyu da shigowa rayuwarmu. Tun safe na bawa Halifa sakon cefanen kayan miya na girkin da zanyiwa Saif, bayan ya dawo da rana ya kawomin a lokacin Na'im ma ya shigo gidan, sai kawai ka kalleni wai "yau kuma girki za'ayi mana na musamman irin wannan shiri haka" ko kallonsa banyiba ya gaji da jiran amsata sai ya kuma cewa "ko ba mu za'a yiwa bane" dago kai nayi na kalleshi nace "masu daraja dai za'a yiwa" da mamaki yake kallona "wato mu bamu da darajar kenan ko?" Ganin yana neman takuramin na kinkimi kayana nayi kitchen ina cewa "ni dai banceba ". Bayan na gama girkina sinasir da wainar shinkafa da miyar alaiyahu sai lemon tamarin da yaji kayan kanshi Allah ya taimakeni kuma da wuta na sakashi a fridge yayi sanyi. Na raba abinci na zubawa kowa da ragowa ma a kitchen sannan na shiga wanka bayan na fito na zauna kwalliya dan yacemin gashinan ya fito daga gidansu zai taho nan, yau so nake nayi masa kwalliya ta musamman a matsayinsa na saurayina ba yayanaba. Bayan na gama na fito Zan shiga dakin su momy sai ganin Na'im nayi daga kitchen da plate a hannu ya karo abinci, kallonsa kawai nayi na dauke kai shikuma ya Bini da wani mayataccen kallo da yasa na kusa tuntube a bakin kofa, har na shiga dakin su momy sai kuma kaina ya bani anya ba abincin Saif Na'im ya taba minba? Dan haka najuyo da sauri har dady na tambayar lafiya nace ina zuwa nayi kitchen da sauri, ina zuwa kuwa na tarar shi din ya diba alhalin ga waninan a babbar kula, aikuwa nayo falo a xuciye ina zuwa na daga labulen dakin da tsiwata nace "Halifa wa yace ka tabamin abinci?" Da sauri ya kalleni yace "abinci kuma? Abinci kikaga inaci?" Nace "to waye ya tabamin akan wanne dalili za'a tabamin baga waninan a kulaba? Sai Wanda na ajiye zanyi amfani dashi za'a tabamin?" Tj na dariya yace "wannan tsiwar dai ba tanan bace ta can ce" ya fada yana nuna Halifa da Na'im "tunda dai ba Halifa kika gani yana cin abinciba" Halifa ma dariyar ya fara yana cewa "Ashe ka gane dan uwa saboda ni ne marainin wayonta shine zatazo tanayimin rashin kunya can ki nemi Wanda ya taba miki abinci" Na'im da ko kallona baiyiba tunda na shigo ya dago ka kalli Halifa yace "kai ta raina shiyasa idan yarinya ta isha tazo tace zatayimin magana ta ga yadda zan ballata nan wajen" ai kuwa ya kuma tunzuroni " wallahi baka isa ka ballaniba har gidan ubana ba binka kaga inayiba balle ka kuma wulakantani kuma ba tsoronka nakejiba na fada wayace ka tabamin abincina?" Ina magana ina kuka, ai kuwa nan da nan Halifa da Tj suka taso suka fara rarrashina amma dan rainin hankalin sai cewa yayi "ayya bayan rashin kamun kai hadda ci kike dashi kenan dan banga ta yadda zaki iya cinye wannan abincinba ko kuma rowace ke dawainiya dake ban saniba" nace "nayi rowar ina ruwanka ai ba kai ka dafaminba ba kuma dankai na dafaba kawai zaka debarmin" momyce ta shigo dakin tana cewa "wai me yake faruwane Fadima wa kikewa rashin kunya haka? zaki bata kwalliyar taki da hawaye" ai kuwa na kuma shagwabewa "momy abincin Saif fa wannan ke ci hakanan bayan yaci nasa kuma saboda bai iya bada hakuriba yake gayamin magana" baki momy ta rike tana cewa "aw wai da Na'im ma kikewa wannan fitsarar kamar sa'anki? Na zatama halifane ko Tj maraina wayon naki?" Jin tana neman goyon bayansa na fara buga kafa a kasa ina cewa "momy abincin Saif ne fa" azuciye Na'im ya mike yana cewa "wai who the hell is this Saif ne kin damu mutane da Saif Saif ?" Kamar daga sama naji a bayana ance " and who the hell are you? How dare you zakana mata shouting aka?" Da sauri momy ta daga hannu ganin abin na kuma zama worse tace "ya isa haka dan Allah kai Na'im baka kyautaba kema baki kyautaba kuma ki bashi hakuri dan ba sa'anki bane, Saif kai kuma karka shiga maganar na kasheta haka, abincinki kuma zan dafa miki wani yanzu shikenan?" Na kuma zumbura baki " momy ni Wanda na dafa nakeso " kallona kawai momy keyi da mamaki Sai da Saif yayi gyaran murya ya fara gaisheta sannan ta dauke ido daga kaina, bayan sun gama gaisawa ya mikawa Na'im hannu maimakon ya miko masa kawai sai ya koma mazauninsa ya cigaba da cin abincinsa har na bude baki zanyi magana Saif ya kalleni da sauri ya girgiza kai dole na hadiye abinda zan fada amma fa na kullata, sun gaisa da Halifa da Tj Halifa na tambayarsa wajen aiki suka danyi hira sannan nace " taso mubar musu dakin akwai yan bakin ciki a ciki gwara mu koma dakin Halifa" wani mugun kallo yayimin nima na maida masa sannan na fice ina jinsa yana cewa Halifa "Halifa wallahi wataran zan balla kanwarnan taku idan baku ja mata kunneba, yarinya sai shegiyar rashin kunya kamar rainon kan titi?" Da sauri na juyo Zan bashi amsa Saif ya rike hannuna sannan yace "kyaleshi neman magana ne kawai muje" haka na bishi muka koma dakin Halifa sai da muka gaisa sannan na shiga debo masa abinci, ina shiga na leka falon da suke nace " dadin tama uwa dayace ta rainemu kaga duk mu biyun rainon titinne" na juya nayi ficewata.
Tun daga ranar Na'im bai kuma zuwa gidanmuba sai dai Tj shima ba sosaiba dama shi karatu yake anan shiyasa bai fiya shigowaba, wannan zuwan na Saif munsha soyayya kamar bazamu rabuba kullum sai yazo idan muka fara hira kuwa jinmu muke tamkar mu kadaine a duniyar gaba daya, bamaji bama gani danma kar a damemu kullum a dakin Halifa muke zama, wannan karan Saif a matsayin saurayina yazo ba a matsayin dan gidan ba. Na'im da Tj har yau Allah baisa sun hadu da dadyba saboda mun daina fitowa dashi yanzu kuma kullum sai yayi mana mita, daya tambayemu surutun suwa yake jiyowa a falo sometimes sai mukace Saif ne da Abdul bai kuma Kawo cewa yaji surutun way before Saif ya dawoba dan haka ya yadda. Ina feeling guilty koyaushe akan karyar da muke masa amma bansan yadda zanji na fada masa gaskiyaba ba tare da nayi hurting dinsaba, banason jikinsa ya kuma rikicewa bana kuma son nayi raising hope na sa akan family dinsa kuma abin ya zama ba yadda nake tsammaniba dan haka I have no choose but to continue lying.
Rannan kafin Saif ya koma ya gayyaceni zuwa gidansu dan haka na tambayi momy ta yadda tace amma mu tafi tare da feena, dan haka na shirya yazo ya daukemu ni da feena muka tafi. Munje gidansu da antynsa mai kirki sosai kana ganinta kasan jinin Saif ce dan sunfi kama da Saif ma akan su Abdul data haiha, mun tarar da kannensu mata uku da namiji auta yaran ma sun karbeni sosai maryam sa'a tace dan haka Saif yace ya hada mu kawance dama ni bani da kawa ko daya banma tabayiba da farko halifaane kawai abokina da mukaje Korea ma Lee yoo shing ne abokina dan haka ban taba kawaba. Da zamu taho antyn Saif ta bawa feena kayan kwalliya da yawa nima ta had am in set na kayan wanka da mayuka masu kyau mukayi godiya Saif ya daukomu, a hanya yake bani labarin wai ya gaya Mata a store dinta nake aiki tayi ta mamaki da mamaki nima na kalleshi nace "au dama store dintane bana Abdul ba?" Yace "kusan haka jada kudi dai sukayi amma tafishi share shi kuma shi yake kula da store din kinga nasune su biyu, sunantane ma akai ai Fatima zahra" na jinjina kai ina cewa "haba nifa akwai sanda nayi ta mamakin me zahran yake nufi Ashe Fatima zahra" haka dai mukayi ta hira har ya dawo dani gida.
BINABASA MO ANG
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...