Chapter 16

93 11 0
                                    

Fadima POV
Wata irin shakuwace ke shiga tsakanina da saif haka shida feena ma, tun muna tsoron bashi ita su fita tare har mun daina, kullum suna tare yau ya siyo mata wannan gobe wancan.
Rannan dai sai gashi ya shigo da sauri yana kirana ni kuma lokacin ina zaune a falo ina karanta wani littafi da saif din ya taba kawomin, ya shigo da sauri yana kirana na amsa daga daki sannan ya leko yana cewa "surprise surprise" na fara dariya ina cewa "surprise" yazo ya zauna a kusa dani "yaudai na Kawo miki Abdul har gidannan da kyar ya yadda zaizo" dariya kawai nayi nace "to yana ina? Nidai kai kadai na gani" mikewa yayi yana cewa "bari na shigo dashi yana waje"  ina nan zaune ya shigo dashi, tubarkallah shima kyakykyawa dashi dan abinda na fara noticing kenan suna shigowa, fuskarsa a hade kamar zaiyi kuka haka yazo ya zauna shima saif ya zauna, da kyar na daure na gaisheshi saboda wani cin magani da yakeyi, kawai naji baiyiminba mutum sai shegen girman kai? Haka saif yayi ta surutunsa ina tayashi shi kuwa dan mulkin danna waya kawai yakeyi har sai da na gaji sannan nace "wai Yayana ina da tambaya" ya juyo yana kallona sosai yana cewa "ina jinki kanwata" na kalli Abdul sannan nace "shi wannan dan uwan naka bebene ko kurma?" Da sauri ya dago kai yana kallona ni kuma na dauke kai na juya na kalli saif da yake uwar dariya, sai da ya gama dariyarsa yace " kai kanwata da bebe ko kurma yayi miki Kama?" Na yamutsa fuska nace "to ai abinne naga sai hira ake amma shi banda danna waya babu abinda yakeyi kamar baisan abinda akeyiba kamar ma babu mutane a wajen" saif na cigaba da dariyarsa su Halifa da feena suka shigo nan aka cigaba da hira amma har yanzu ko a baiceba, can ya mike "bro nikam nayi gaba idan ba yanzu zaka tafiba" da sauri feena tace "kaiii saifeena dama wannan yana magana?" Ai kuwa muka kuma kwashewa da dariya kawai sai naji ya ja wani uban tsaki yayi waje da gudu saif ya bishi yana Kira mudai mukayi ta dariyarmu.
Washe gari da safe ina cikin sharar tsakar gida naji yaro yayi sallama na amsa nace ya shigo sai gashi da buhun shinkafa irin karaminnan da mamaki nake tambayarsa injiwa sai cewa yayi yana kofar gida dan haka na dauko hijabina da sauri na biyo bayansa a soro muka hadu da wani yaron da katan na taliya nayi saurin yin waje nan naga saif yana fito dasu daga boot din motarsa su kuma yaran na shiga dashi ciki, nayi saurin zuwa wajensa ina tamabayar "Yayana meye wannan din daga ina? Kuma na waye?" Bai kulaniba yana cike na farin ciki kamar kullum ya gama bawa yaran kayan suka shiga dashi sannan ya dauko wheelchair ya wuce ciki ya barni a tsaye dan haka na bishi da sauri ina tamabaya "saif ina magana ka ki kulani meye wannan?" Sai da ya shiga tsakar gida ya ajiye wheelchair din ya budeta sannan ya dago ya kalleni fuskarnan kamar gonar auduga yace " yaya dai ko idon ya sami matsalane mu tafi asibitin Makkah? Kinga mubar wannan maganar me kike gani wannan?" Ya nuna wheelchair din gabansa nace "wheelchair" yace "yauwa yau dady zai fara fitowa bakya ganin yawan kwanciyar da yakeyi zai gaji dashi?" Da sauri nace "kaga alhaji ba wannan nake maganaba wannan kayan abincin nake tambayarka na menene?" Ya kalli kayan yace " kayan abincine mana ko dai da gaske sai an hada da glass din da gaskene?" Kamar an gayawa Halifa meke faruwa sai gashi ya dawo yana shigowa yace "ya dai? Meke faruwane?" Da sauri nace "Halifa kalli wasu kaya da saif ke shigowa dasu gidannan kasan da wannan maganar?" Da sauri ya girgiza kai yana cewa "no ban saniba me ya faru haka saif?" Jikinsa a sanyaye yace "dama ashe laifine dan da ya dauki salary yayiwa yan uwansa da iyayensa shopping? Nayi tsammanin nima dan gidannanne? Kullum kana fita aiki kuma kanayine dan ka samo abinda zakuci a matsayinka na dan dady da momy ashe ni dannayi haka sai ya zama laifi ko kuwa dan basu suka haifeniba?" Da sauri Halifa yace "bawai haka muke nufiba amma kamar bamuyi haka da kaiba a yarjejeniyarmu ko?" Shima ya bashi ansa da "bamuyi hakaba amma a cikin responsibilities na da Baku cemin akwai abinda zan iya da Wanda bazan iyaba" kallonsa Halifa yayi sannan yace "me kakeso saif? kanaso ka kashemin zuciyane na daina abinda nakeyi? Dan me nake fita aikin dan musami abinci da kudin magani idan ka dauke wannan kana tsammanin zan cigaba da fita aiki?" Za sauri ya bashi amsa da "sai ka koma makaranta dama karatu ya kamaceka ba aikin karfiba" a zuciye Halifa yace "saif will you stop it? Na gaya maka ina son karatu?" Shima a zuciyen yace " Halifa I'm trying to help can't i?" Da sauri Halifa yace "yes idan har kanason ka taimaka manane to ka nemamin aiki amma ba ka siyo mana kayan abinciba, bakaji me bahaushe yaceba? Daka bawa mutum kifi gwara ka koya masa kamun kifin, idan ka bamu yanzu sanda bakanan kuma wazai bamu?" Nidai ina gefe bansan me zanceba ban kuma San me zanyiba kawai na tsaya ina kallonsu. Shiru saif yayi zuwa can yace "yanzu Halifa wanne iri aiki zan sama maka da secondary certificate? Babu dole sai dai aikin karfin ko kuma ka koma school" kallonsa Halifa ya kumayi sannan yace "wai kana tunanin Zan biye maka na koma makaranta? Kai kuma ka rinka ciyar damu kana kuma daukan nauyin karatuna? Haba mallam mutuwar zuciyar tawa bata kai hakaba kuma idan ba zaka taimakemu mu nemi kudi da kanmuba to karma taimakemu da kudin ka gane?" Yana gama fadar haka ya juya yayi hangar waje zai fita da sauri saif yace "shikenan Zan samo maka aikin na yadda amma da sharadi" dawowa Halifa yayi yace "sharadin me?" Saif ya ansa da "nima duk taimakon Dana Kawo gidannan bazakuki karbaba" juyawa Halifa ya kumayi yana cewa " ban yaddaba barshi kawai" har yakai soro saif ya kuma kiransa ya leko "shikenan na yadda bazan kuma Kawo komaiba amma zaku karbi wannan sannan idan kuna cikin matsala zaku gayamin" dawowa gaba daya Halifa yayi cikin gidan ya mika masa hannu "deal?" Shima saif ya mika nasa sukayi shaking yana cewa "deal" da sauri na daga hannu nace "ni kuma duk ban yaddaba" da mamaki suka juyo suna kallona da alama ma sun manta Dani a wajen, murmushi saif yayi yace "me kuma me kike so" sai da na hade rai alamar ba wasa sannan nace "nima sai an samomin aikin" gaba daya suka hada baki wajen cewa "what?" Nace "eh nima sai an samomin aikin duk da za'a samowa Halifa" Halifa yace " Fadima kina haukane? Su momy kuma waye zai zauna dasu idan kema kika fita aikin? Kinason rigimane kawai ko?" Nace "ko daya ba rigima nakesonyiba kawai na gaya muku koma aikin me za'a samo maka wallahi nima sai nayi" saif yace "Fadima wallahi fa kikace ni yanzu bani da wani aiki shima da Zan samo masa indai bana karfiba sannan idanma kince zaki iya su momy fa kina tsammanin zaku fita gaba daya kubarsu su kadaine?" Kafada kawai na daga nace "oho ayi wannan maganar daga baya amma abinda na Sani shine nima wallahi sai nayi aikinnan koda yayane insha Allah ".
Kwananmu biyu muna wannan rigimar kullum maganar kenan amma naki yadda  nace nima sai nayi aiki. Tun a ranar aka saka dady a wheelchair din, aikuwa ba karamin dadi yajiba da aka fito dashi waje yasha iska, dakyar ya yadda ya koma ciki sai ance a maidashi sai yace shifa bai gajiba daga baya dai sai barinsa mukayi sai da magriba ta gabato sannan na maidashi daki. Tun daga ranar kullum dady nakan wheelchair akai yake sallah akai ake masa wanka Wanda ada saidai a goge masa jiki da towel kawai, har waje Halifa yake zagayawa dashi ko kuma da yamma su zauna a kofar gida sai anyi kiran sallah sannan su dawo gida.
Na dawo rannan daga dauko feena daga makaranta na tarar da saif yazo yana zaune a mota Halifa kuma yana daga waje suna hira, ina zuwa na leka motar nace "Yau kuma yan zaman kofar gidane sukazo?" Dariya kawai yayi sannan ya bude motar ya fito suka taba da feena ya ja hannunta sukayi ciki, da alama akwai abinda me damunsa. Cikin muka bisu ni da Halifa muka tarar dasu a falo ina zama nace "oya feena aje a cire uniform akai jaka daki" ta dauki Jakarta da har an yarda ita a tsakar daki tayi dakinmu da gudu, tana fita ya gyara zama yace "Fatima har yanzu kina kan bakanki nayin aiki?" Da sauri nace "eh" ya girgiza kai kawai zuwa can yace " nayi iya bakin kokarina na neman aikin da Zan samo muku mai sauki na rasa amma ga shawara idan kuna ganin zaku iya akwai store din Abdul zahra zan iya samo muku aiki a can amma gaskiya Fatima banason aikinki a wajen saboda wajene na jama'a yawancin maaikatan wajen ma mazane kinga bai kamatabadama hakura kikayi kawai" ai kuwa na bata rai nace "Baku yadda dani bane?" Da sauri yace "ba haka nake nufiba kawai dai.." Na katseshi da cewa "indai kun yadda Dani ni kuma nayi muku alkawarin kare mutuncina, ba cikin mazaba ko Tasha aka kaini nayi muku alkawari zan kare mutuncina" Halifa saif ya kalla shima yace "shikenan ba matsala Allah ya karemu baki daya ya kumasa hakanne mafi alkhairi" muka amsa da ameen sannan yace "amma wai su momy fa?" Ajiyar zuciya saif yayi yace "ba matasala indai kun yadda da zaharn zaku iya dutyn safe da yamma kunga idan daya ya tafi sai daya ya zauna idan dayan ya dawo shi kuma sai dayan ya tafi ko?" Duk mukace shikenan, nan Halifa ya mike "Bari na dan fita da dady waje" nace to ya juya ya fice, shiru mukayi na wani lokaci sannan saif yace "Fatima" nace "naam" yace "Fatima zan koma wajen aiki" da sauri na kalleshi wani iri naji babu dadi already har na fara missing dinshi nace "yaushe" muryarshi kamar zaiyi kuka yace "gobe " da sauri nace "what? Gobe fa kace amma sai yanzu kake fada mana? Saboda me?" Ya taso daga kujerarsa ya tsugunna a gabana gaba daya idonsa yayi ja kamar bashiba yace "nima yanzu nasan da tafiyar tun sati biyu daya wuce hutuna ya kare ban komaba dazu akayomin waya akan maza gobe na koma bakin aikina, nima banason tafiyarnan inajin kamar na hakura da aikin saboda banason nayi nesa daku ko kadan" wani kukane yazomin da gudu nabar dakin zuwa dakinmu na kwanta nayi me isata, banaso ya tafi inajin zuciyata namin wani irin zafi, ji nake kamar idan ya tafi bazai dawoba shikenan ya tafi kenan, haka nasha kukana inajinsa ya tafi amma ban sami fitowaba. Ranar haka na karasata kamar marar lafiya Halifa yayi ta tambayar abinda ya sameni amma naki fada masa saboda bansan me zance masaba.

FadimatuOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz