I'm sorry

90 15 0
                                    

Fadimatu POV
Bansan me yake faruwaba sai da momy tace nazo muje gida zamu hada kayanmu , da mamaki na kalleta " momy Ina zamu koma?" Kafin ta bani amsa dan monitor din dake jikin dady ya fara beefing alamar ya tashi, da gudu dukanmu mukayi kansa kowa na kiran sunansa amma wani abun mamaki ko motsi baiyiba, ni da halifa muka rike hannayensa yayin da momy tayi waje da gudu kiran Dr. A hankali ya bude idonsa wanda yayi ja sosai kamar ba na mutumba, da ganin yadda yake juya idon kasan baya ganin komai sai a hankali ya fara ganinmu murna mukeyi da hawaye da komai sai dai wani abin mamakin shine ya kasa yiwa kowa a cikinmu magana sai bi da Ido, gashi dai daga dukkan alamu yana kallonmu kuma ya ganemu domin akwai wani emotion cikin idonsa da ya nuna hakan amma ya kasa furta komai, muna cikin haka momy ta dawo tare da Dr da wasu nurses guda biyu kowacce da farantin Silva da kaya a ciki, suna shigowa yace mu dan basu waje dan haka muka fito bakin kofar dakin muna jira tare da addu'ar Allah ya jishemu alkhairi yasa wahalar dadynmu ta make ameen. At least sun dau kusan mintina talatin a cikin dakin kafin suka fito kallon fuskar Dr kawai nayi naji wata Katanga ta ruguzo a kirgina domin babu alamar farin ciki sai wani mugun tashin hankali dana karanto. Office dinsa kawai Dr ya nufa ai kuwa babu gayyata mukabi bayansa gaba dayanmu muna zuwa ya zauna a kujerarsa ta gado ni da momy kuma muka zauna kujerun gaban table din yayinda Halifa ya zauna daya daga kujerun dake jere a gefe da feena a cinyarsa, ahankali Dr ya fara magana " I'm so sorry haj kubra but abinda nake tsoro ya faru wato paralyze, Alh kabir ya hadu da paralyze na barin hagu, baki dayan left side nasa yanzu baya amfani tare da wasu manyan bangarori kamar bakinsa da sauransu munyi iya kacin kokarinmu amma mun kasa shawo kan matsalar dan ada munyi tsammanin komai ya daidaita sai yanzu daya farka mukaga ba hakaba dan haka sai dai kuyi hakuri yanzu kuma mu dorashi akan treatment na paralyzed." Ni kaina bansan me ya faru daniba ban saniba suma nayi ko mutuwa ta wucin gadi oho? Amma na san kaina ya dauke na wani lokaci dan ba gaba dayan abinda Dr ya fada na fahimtaba, kukan momyne ya dawo dani hayyacina da sauri na tashi daga inda nake naje na rungumeta tare da sakin nawa kukan, innalillahi wa Inna ilaihir rajiun wannan wacce irin masiface? Da fari talauci yanzu kuma cuta ya ubangiji ka bamu ikon cin wannan jarabawa ka tashi dadynmu ya Allah kar ka dauke mana dady ba yanzuba ya ubangiji. Haka mukayi ta kukanmu babu mai rarrashin wani daga baya muka bawa juna hakuri muka fito tare da komawa dakin da dady yake, wato ashe bamuga tashin hankaliba sai da muka shiga dakin muka koma kan dady, gashinan dai idonsa a bude amma babu abinda yake motsi a jikinsa sai ido, bakinsa ya karkace zuwa barin hagu ga wata mahaukaciyar rama da yayi wadda duk ada bamu ganiba sai yanzu, nan kukanmu ya dawo sabo muna masu tausayawa dady da kuma kanmu dan muma abin a tausaya mana ne, ba mu muka dawo nutsuwarmuba sai washe gari dan anan asibitin muka kwana gaba dayanmu.
Washe gari Dr ya kira momy yayi mata bayani akan wani aiki da yake suggesting ayiwa dady wanda yana saka ran in sha Allah idan anyi zai iya samun sauki, yayi mata bayani sosai kuma ta gamsu sai dai fa aikin na da tsada dan akallah ba akasaruba ana bukatar 10m, wannan shi ya kashe wa momy jiki amma ganin akwai kudin gidanmu da aka siyar kawai sai ta yadda menene amfanin kudin idan babu lafiya? Mun cigaba da kasancewa kullum a gaban dady muna yi masa hirar da zata saukar da jininsa dan yana farkawa ya sake hawa kuma Dr ya gaya mana yana jin abinda duk muke fada kawai dai bazai iya maidawa bane saboda karkacewar da bakinsa yayi, mun manta ma da maganar wani tashi daga gida mun dukufa addu'a da shirin aikin da za'ayi nan da sati guda, kowannenmu hankalinsa na kan dady da addu'ar Allah ya bada sa'a a wannan aiki muma muga dadynmu ya kuma takawa da kafarsa. Kwatsam rannan muna zaune muna cin abincin da naje gida na dafo mana Ina yiwa momy lissafin kayan abincinmu fa sun kusa karewa kawai sai ga waya daga wanda ya sayi gidanmu cewar sati biyun da ya bamu fa ta kare kuma baiga alamar mun fara shirin tashiba, ba karamin tashi hankalin momy yayiba saboda ta ma manta shaf da wannan maganar nan dai ta bashi hakuri tare da alkawarin ya kara mana kwana biyu in sha Allah zamu tashi, munyi sa'a mutumin nada mutunci dan haka ya kara mana kamar yadda muka nema.
Muna gama cin abinci nurses suka shigo suka bawa dady maganinsa tare da allurai dama lokacin baccinsa yayi nan da nan kuwa bacci ya kwasheshi da yake har da allaurar bacci a ciki, yanayin bacci momy ta kallemu fuskarta babu yabo ba fallasa tace "tunda yanzu dady yayi bacci at least zai sami 3-4 hours nan gaba kafin ya tashi dan haka ku wuce muje mu fara hada kayanmu zuwa gobe Halifa sai ka samo mana motar da zata kwashe mana kayan kunga mutuminnan yayi mana mutunci kar mu kaishi bango" a hankali muka jinjina kai tare da mikewa muka kamo hanyar gida gaba dayanmu.
Bayan munzo muka fara hada kaya mune kayan sawa, yan kayan kichin din da zamu bukata hatta da furnitures mun dauki wani abun amma iya wanda zai iya shiga gidan namu, mun gama hada komai a ranar washe gari mota tazo ta kwashe mana zuwa wancan gidan dady na kuma yin bacci ni da momy muka tarar da Halifa acan nan muka jera komai muka shirya gidan, washe gari kuma dan abinda ba'a rasaba muka koma muka cinta a tsohon gidanmu tare da karasa gyaran sabon gidanmu sannan muka bawa mai gida gidansa, da zamu fito a gidannan na yi kuka kamar raina zai fita, shikenan gidanmu mun rabu dashi sai dai wani ikon na ubangiji kuma, aranar ne kuma aka biya kudin aikin dady washe gari kuma aka shiga dashi theater.
Ya daukesu wajen 4hours kafin su fito dashi nan aka kuma dawo dashi dakinsa inda mu kuma muke ta faman sallah da rokon ubangiji sassauci, dady bai farkaba sai washe gari da asuba sai dai kuma me? Babu abinda ya canja bayan bakinsa da yake iya motsawa shima ba'a fahimtar me yake cewa sai hannunsa da kafarsa na dama da suka fara motsi.
Ina ganin hakan na kalli Dr dake faman wani dube dubensa a fayil din dadyn raina a bace nace " Dr ko zaka iya yi mana bayanin me yake faruwa? Nayi tsammanin cewa kayi koda bai mikeba zai iya motsa gabobinsa idan ban mantaba har cewa kayi idan har anyi aikin sai dai ya koyi tafiya da magana kawai ko ba haka kaceba?" Nan ya fara wani mitsitstsika ido yana in ina " amm.. Ai dama.. Wallahi abinda ya faru.. " kafin ya gama hada karyar da zai fada Halifa ya shaki wuyansa ya hadashi da bango, Halifa yana kuka yana fadin" sai ka gaya mana me ya faru da mahaifinmu me kayi masa? Ina duk kudin da muka biyaka? Kai wanne irin azzalimine ko tausayinmu bazakajiba?" Da kyar aka kwaceshi a hannun Halifa dan ba karamar shaka yayi masaba, Sai bayan an rabasu sannnan Dr ya samu bakin magana " kar kuyimin sharrin wani abu dama aikin theater ya gaji haka kun biya kudinku kuma nayi muku aiki ba gashinanba ya Fara motsi? Ai saukin ba a hannuna yakeba sai ku cigaba da addu'a ko ku canja masa asibiti idan kuna ganin cutarku nayi" yana kaiwa nan yayi waje da sauri yana rike da wuya ganin Halifa ya kuma yin kansa, nan ya barmu a tsakiyar dakin rungume da juna muna faman kukan bakin ciki.
Wai me yasa mutane basu da tsoron Allah? Da fari danfarar dadynmu akayi dalilin da ya sakamu a wannan situation din kenan yanzu kuma Dr din da muka saba dashi tun yarintata nasanshi da yan gidanmu shima ya kuma danfararmu, ya Allah gamu gareka

FadimatuWhere stories live. Discover now