Chapter 20

141 13 0
                                    

Na zubowa momy abinci ina shigo dakin na tarar da ita a kasa ta dora kanta a cinyar dady Halifa kuma ya dora kansa a cinyarta duk su ukun suna kuka, da sauri na isa gareta na ajiye abincin ina tambayar me ya sameta? Ko wani wajenne yake Mata ciwo amma maimakon ta bani amsa sai kawai ta jawoni ta rumgume tana kuka tana cewa "I'm sorry Fadima I'm so sorry maimakon na tsaya na zama kwarin gwiwarku na zama katanga a gareku sai na kuma zame muku aiki na godewa Allah daya bani yaya irinku banda haka Allah kadai yasan da ayanzu halinda nake ciki dagani har dadynku kuyi hakuri na kuma yi muku alkawari insha Allah hakan bazai kuma faruwaba I will always be there for you" ahankali na taso daga jikinta nima ina kuka domin na fahimci kukan da suke yanzu, hannu nasa  na share hawayena nace "momy don't be like that kefa musulmace kinfi kowa sanin bake kika dorawa kanki ciwonba ba kuma dadyne ya dorawa kansa nasa ciwonba so u don't have to be sorry, sannan bai kamata kiyi alkawari akan abinda baki da iko dashiba bamu fatan wani abin ya kuma samunki amma nasan lafiyarki ba a hannunki takeba so karkiyi alkawarin hakan ba zai kuma faruwaba kinji? Kuma menene a ciki jarabawace ta ubangiji babu abinda zamuce sai hamdala da kuma fatan Allah yasa mu cinyeta baki daya muna fatan kuma Allah yayi farin ciki da tawakkalinmu kinga kuwa idan har muna son ubangiji yayi farin ciki da mu to dole muyi hakuri da duk jarabawar da ya dora mana sai kiga ya shige mana gaba ko nan gaba, momy banaso ki feeling guilty akan abinda ba ke kika dorawa kankiba mu yayankine bazamu taba gajiyawa da keba dan haka ki kwantar da hankalinki ranar Monday zamuje asibiti su kuma checking dinki sosai su tabbatar babu abinda ke damunki sannan mu cigaba da rayuwarmu Allah yana nan OK? Komai zaiyi daidai kinji?" Kai ta gyadamin tana shafa kumatuna tace "Allah sarki rayuwa kenan yarinyata ta girma tayi hankali, wazaice wannan fadimatunace?" Duk dariya mukayi sannan na bara bata labarin duk abinda ya faru tun daga ranar data fado daga stairs har karshe wato yau data dawo hayyacinta ban boye mata komaiba, wani wajen muyi dariya wani kuka wani mamaki. Haka dai har muka gama inayi ina bata abinci a baki, sai bayan min gama sannan tace "wai ina feena takene? Ni tunda na farka bangantaba" sai a lokacin na kula feena bata dakin dan haka na mike ina murmushi nace "maybe tana dakinmu naga ai ta tsorata da faduwar da kikayi saboda ita ta zubar da ruwan bari na kirawo miki ita" ina gama fadar haka nayi waje zuwa dakinmu da niyyar kiran feena amma me? Babu feena babu alamarta, nice kitchen falo bandaki duk batanan nan Halifa ya fito mukayi ta nemanta amma shiru. Wasa wasa fa feena bata cikin gidannan nan fa hankalinmu ya tashi mukayo waje har momy da dady mune makota da layukan bayanmu amma babu feena nan muka dawo kofar gida inda mukabar momy da dady na jira, hankalina fa ya tashi kuma kuka kawai nakeyi ina kiran sunan feena nan Halifa yace mu koma cikin gida zaije yayi reporting wajen yan sanda, ni kuma abinda banasonji kenan saboda inajin ance yan sanda zan kuma tabbatarwa feena ta bata, muna cikin haka sai ga saif yana parking ya fito nayi wajensa da sauri ina "saif na shiga uku feena ta bata banaso wani abu ya sameta ka taimakeni" da sauri ya fara "shishhh ya isa haka ya isa" sannan ya bude back seat na motarsa sai ga feena ta fito a ciki na tafi da sauri zan rungumeta ta kankameshi tana kuka kawai na tsaya ina kallonta. Sai daya kamo hannunta sannan ta taho suka matso kusa damu dady yace "saif me ya faru ya akai na ganka da ita?" Cike da girmamawa yace "wallahi dady nima bansan ta biniba kawai naje gida nayi parking sai dana shiga ciki ina alamurana sai naji hayaniya ina fitowa na ganta yan gidanmu sun rasa wacece daga ina take shine nace na santa na tambayeta shine tace wai tsoro takeji ita ta zubarda ruwan momy ta fadi taji ciwo dama Fatima tayi mata magana tasan yanzu sai ta daketa shine munacan daki taje ta buya a bayan motata wai tasan ni bazan daketaba" kowa mamaki ne ya kamashi nidai hamdala nake da motar saif dinma ta shiga ba wani wajen tayiba, nan na tsugunna na mika Mata hannu da kyar ta taho nace "feena dama dukanki nakeyi?" Ta girgiza kai nace " to meyasa kika gudu?" Tana kuka tace "sister tsoro nakeji momy taji ciwo?" Ina dariya me hade da kuka nace "no sister momy bataji ciwoba wancan ciwon ma da taji ta warke yanzu ta tunaki jekiyi Mata magana ki gani" kallonta kawai ta tsaya yi sai da momynma ta tsugunna tace "come here baby " sannan ta fara matsawa a hankali har taje wajenta momyn ta rungumeta suna kuka nima matsawa nayi jikinsu ina kukan Halifa ma haka, saif ne yayi gyaran murya yace " ahmm momy ko zaku koma daga ciki nan unguwar yan tsurkune har an fara taruwa ana tambayar me ya faru" nan da nan muka mike mukayi ciki dan da munma manta a waje muke.
Tun daga ranar muke cikin farin ciki da daddare Abdul ya kirani ya tayamu murna sannan yace ya bamu hutun sati guda, ranar Monday muka kai momy asibiti sunyi checking dinta sosai kuma sunce babu wani sauran ciwo a jikinta, da yake Dr hanya yayi mana a Murtala sai kudin ya zamana kadan ba kamar da ace a private hospital bane, sannan momy ta jawo wani dan karamin akwati ashe duk sarkokinmu na ciki rashin sani bamusan dashiba sai yanzu dan haka da aka siyar mun sami kudin masu dan dama ba laifi nan akace wata Sana'a za'ayi dasu bawai tasasu zamuyi gaba mu cinyeba.
Adaidaita sahu aka yanke shawarar za'a siyawa Halifa ya rinka aiki da ita ni kuma na cigaba da zuwa zahra kafin abinda hali yayi, nan saif ya taimaka mana duk da ya koma kd ya hadamu da wani mutum da sukaje da Halifa suka siyo adaidaitar aka fara aiki ba kama hannun yaro.
Yau kwanan momy biyar da warkewa muna zaune a tsakar gida ni da ita Halifa kuma ya fita aiki dady na daki feena na islamiyya, muna cikin hira naji sallama a soro nasan saif baya gari dan haka na tabbata ba shi bane dan haka na tashi na saka hijabina na leka, ina fita na sandare a wajen saboda mamaki mutuminane wannan bawan Allahn mai Kama da halifa, kallonsa kawai na tsaya yi na ma kasa magana sai da yayi gyaran murya sannan na dawo hayyacina da sauri nace "mallam me kamun kai me kuma ya kawoka gidan marasa kamun kai? Ko ka fara saida shine ka fahimci ina bukata? Anyway idan ma hakanne bana bukata zaka iya yin gaba" na zuwa zan koma ciki yayi saurin shan gabana "kinga tsaya magana nazo muyi ba wukanci nace kiyiminba" da mamaki nake kallonsa nace " maganar me? Nayi tsammanin bamu da hadi? Kamar kai ba dan kasarnan baneba ma ko? Then go away" yana wani yamutsa fuska yace "dama nima baninaso zuwaba Tj ne ya takuramin wai sainazo dan haka zaki iya yin gaba aikin banza kawai" yana gama fada ya juya zai fice nayi saurin cewa "hey waye me aikin banzan tsakaninmu? Kai kazo wajen aikina a wancan lokacin kai kuma kazo gidanmu a wannan lokacin dan haka kaine cikakken mai yin aikin banzan useless kawai" ina gama fada nima na juya zan shige ciki ita kuma momy ta leko tana cewa "fadimatu ke dawaye haka me yake faruwa?" Da sauri nace " no momy ba komai muje ciki dama tambaya yake na kuma bashi amsa" na jata da niyyar komawa ciki sai ji nayi yace "Anty kubra? Is that you?" Da sauri muka juyo duk mu biyun, wani irin yanayine kwance a fuskarsa da sauri ya matso ya Kama hannun momy "oh my God Anty kubra kece da gaske? Ke nake gani a idona da gaske?" Kawai ga mamakina sai yasa kuka momy ma kukan ta fara ni kuma suka barni cikin duhu.

Yanzu fa aka fara

FadimatuOù les histoires vivent. Découvrez maintenant