Chapter 32

72 6 0
                                    

Ban san iya kacin wahalar dana sha ba saboda most of the time bana cikin hayyacina amma nasan na wahala, har lokacin komawarmu Niger yayi suka daukeni suka tafi Dani a haka. Wani lokacin idona biyu ina kallon mutane amma yawan tunanin dake cikin kaina yafi karfin na fahimci me suke cewa balle har na bada amsa, Na'im da ada shine babban abokin fadana yanzu dashi kadai nake iya yin hira sai sometimes halifa.
Watannin Saif biyu kenan da bata ( haryau ban yadda mutuwa yayiba yananan a raye) haryau ba'a ganshiba sunma daina nemansu daga shi har dayan abokin aikin nasa, dajin kuma ba wajen da mutane zasuje bane balle yan uwansa suje su nemeshi dole sai sojojin to kasata Nigeria ta daina neman yaran da aka sace dinma balle sojojin da akace an tabbatar sun mutu dan haka tuni aka rufe wannan case din.
Ranar da muka dawo Niger muna sauka a airport na diffa muka tarar da motoci na jiranmu dan haka muka shiga suka kwasomu zuwa gida, ada banyi tsammanin arzikin kakana ya kai hakaba sai da naga get din da aka bude mana, wannan ba wai gida bane aa estate ne wanda kana shiga akwai katon mansion a tsakiya sannan six two storey buildings uku iri daya uku iri daya a zagaye dashi sai incomplete guda biyu, daga bayan mansion din ina iya hango green land wanda nake kyautata zaton garden ne. Muna zuwa gaban na tsakiyar aka ajiyemu wanda yake 3 storey, muka fiffito muka dunguma zuwa ciki, katon falone irin na finafinan turai sai dining area mai dauke da dining table kato wanda ina tsammanin yana zagaye da kujeru sama da goma, sai kitchen da wasu dakuna da bansan na wayeba. Anan falon muka zube gaba dayanmu nan da nan yan aiki suka cika mana wajen da kayan sanyi dan jika makoshi, bayan shigowarmu da abinda bai wuce mintina 20 ba wani mutum ya turo kofar falon ya shigo tare da iyalinsa mata daya da yara biyar maza biyu Mata uku, ina ganinsa nayi assuming wanna ne sagir din yayan dady. Tsugunnawa yayi a kusa da kafafun dadynmu a kasa da sauri dady ya kamoshi ya zaunar dashi akan kujera kusa dashi nan ya Fara magana "Kabir dan Allah dan annabi nasan nayi maka laifi wanda yake da girma nasan ban cancanci yafiyarkaba amma nasan kai ba Irina bane zaka iya yafemin sannan ko baka yafeminba nasan kasan na karbi laifina kuma nayi nadama dan Allah dan annabi Kabir ka yafe mana ni da mahaifiyata ko nai karshe mai kyau ita kuma taji dadin kwanciya dan Allah" da hawaye da komai yake rokonsa, rungumeshi dady yayi shima yana kuka yana cewa "na yafe maka sagir na yafe muku baki daya, kuma ai ni hakan alkhairi ya zamemun tunda na koyo darussa Kala Kala wadanda dana zauna a gida bazan taba koyaba, Allah ya gafartawa umma ya kyautata kwanciyarta mu kuma ya yafe mana ya kyautata karshenmu ya kuma hada kanmu" gaba daya muka amsa da ameen sannan sagir ya kuma cewa "na gode na gode sosai dan uwa, ba karamar kunya najiba kai dama haka Allah ya halicceka daga kai har mahaifiyarku zuciyarku ta musammance da wanine bazai taba yafeminba na gode sosai Kabir" rumgumeshi dady yayi yana dariya yace "ka manta sunanmune? Kabir sagir dan haka karka damu sannan kuma kai dan uwanane zan iyayi maka komai koda kuwa abinda yafi hakanne kaji ko?" Kai ka gyada sannan ya tashi daga jikin dady ya koma wajen Abba shima ya sake neman gafararsa haka dai sukayi ta koke kokensu da dararraki nidai su Rufaida sukace na taso mu tafi wajensu, daya daga cikin two storey buildings dinnan guda shida muka shiga gidan yayi kyau kamar wancan katon falone da kitchen dining area da kuma dakuna guda biyu sai dai wannan bai kai wancan girmaba, sama mukahau zuwa dakinsu Rufaida Ashe a sama bedrooms din suke. Ina shiga toilet na wuce dama fitsari ya addabeni sannan nayo alwala daga can nazo nayi sallolin da ake bina, ban dakin na koma na hada ruwa mai zafi sosai na shiga ciki kawai nayi kwanciyata. Saboda gajiyar da nayi da dadin ruwan bansan bacci ya daukeniba sai da naji ana jijjigani, da sauri na bude ido Rufaida ce hankalinta a tashe tace "haba Fadima wallahi kin tsoratamu bacci a bandaki? Munyi zaton wani abunne ma ya sameki dan Allah ki rinka gudun tashin hankalin family dinki kamar yadda muke gudun naki, kiyi sauri ki karasa tun dazu ana jiranmu zamuci abinci kinanan." Tana gama fada tayi waje ba tare da tajira abinda zance mataba, da sauri na karasa wankan ruwan nawa ma har ya huce, ina gamawa na dauro towel na fito, wata goduwar Riga na tarar a kan gado Rufaida dake zaune bakin mirror tace "ga kayan da zaki sakanan su Abbie na jiranmu a falon Abba zamuci abinci" kai kawai na kada sannan na zauna na shafa mai na saka kwalli dama yanzu iya kwalliyartawa kenan kwallinma sai da kyar momy ta saka ni nake sakawa, ina gamawa na zira rigar tayimin kyau sosai ta kumayimin daidai, ina gama sakawa Rumaisa ta shigo "yauwa ashe kin fito kuzo muje dan Allah suna ta jiranmu" dankwalin rigar kawai na yafa akaina muka fito tare, dukkanmu kayanmu iri dayane ni da Rumaisa da Rufaida banbancin kawai bakace gaba daya tawa da ratsin green ta Rufaida pink Rumaisa kuma red kowa favorite color dinsa.
Mansion din da mukabar su dady can muka koma, muna shiga gaba daya suka mike zuwa dining area dama mu ake jira technically ma ni ake jira, kowa ya sami kujera dan sai da na shiga wajen na kirga kujeru ashirinne a wajen dan haka kowa ya sami wajen zama yayin da dady ke kan wheelchair dinsa, haka mukaci abinci bayan Abbie yayi mana addua tare da godiya ga Allah daya hadamu a waje daya bayan fitar da rai da haduwar tamu, kusan kowa a wajen sai da yayi kukan farin ciki, sannan uncle sagir ya kuma rokar kowa gafara akan abinda ya faru su dady kuma suka ce kar ya kuma roka abinda ya wuce ya wuce. Silently mukaci abincinmu har aka gama sannan aka shiga sabuwar hira, nan ammie tace " ni dai Kabir kasan me nakeso?" Kai ya girgiza yace "sai kin fada Maman Na'im" tana kallona tace "fadimatu zaka bani ta dawo wajena kaga ga yan uwanta su Rumaisa sai ta fi jin dadi akan ace ita kadaice a wajenku ko? Kuma duk gida daya muke balle ace zatayi missing dinku" ta karasa maganar tana maida kallonta ga dady, shima murmushi yake yace "indai fadimace dama ai takice gaki gata" goggo tace "har muna cewa mu za'a barwa Fadima? Tunda mune muke shiru babu dan baribari" da Sauri ammie tace "goggo ga feena nan tunda dan bari bari kuke nema" nan kowa ya kwashe da dariya tace "shikenan mun dauka Allah ya tayamu ruko ko hajiya?" Ta fada tana kallon mama, itama dariya take tace "lallai kam mun dauka dama feeena sai tafi tunda waccen kwanannan zatayi aure ta kuma barinmu amma feena a lalace zatayi nan da shekaru 15 kafin a fara mata maganar aure" kowa yace hakane kam. Nayi iyakacin kokarina na ture tunanin Saif a yau dan nayi enjoying reunion dina da family na, kuma alhmdulillah so far dai ina enjoying until now da mama ta kayo maganar aure, dady momy Halifa da Na'im gaba daya hankalinsu ya dawo kaina dan sunsan dole abin yayi affecting dina, shiru nayi kaina a sunkuye ban kuma kallon kowaba ban kuma fahimtar me suke cewaba har aka gama zaman kowa ya mike dan zuwa a kwanta ayi bacci dan dare yayi sannan ga gajiya, hannuna Rufaida ta kama na dago ina kallonta idona yayi ja a hankali tace "taso mu tafi mu kwanta dare yayi" a hankali na mike tana rike da hannuna Rumaisa na rike da dayan tamkar wata makauniya har mukazo bakin kofar gidansu, "Fatima" da sauri na waiga jikina har rawa yake dan ganin wanda ke kirana, Na'im na gani yana tahowa nan su Rufaida suka cikani sukayi ciki ni kuma na tsaya jiransa, yana karasowa kusa dani na kai masa duka yayi saurin kaucewa yana dariya cikin muryar kuka nace "na gaya maka ka daina cemin Fatima kaki ko? Na gaya maka banaso ka daina" hannu ya daga sama alamar surrender yana murmushi yace "Allah yabaki hakuri na daina, amma nima inason na rinka fadin fatiman nima nafisonsa dan Allah a barni na ringa fada" da sauri na Fara girgiza kai ina cewa "no way ban yaddaba idan zakacemin Fadima ka fada idan bazaka fadaba shikenan kawai ka barshi" shiru yayi na wasu yan seconds sannan yace "to kin yadda na dinga ce miki Sœur?" Fuska na yamutsa nace "me kenan? Ba dadi" dariya ya kumaba yi sannan yace "sister kenan amma tunda ba a Nigeria kikeba bazance sister ba sai dai sœur" har yanzu fuskata a yamutse take alamar har yanzu sunan baiyiminba nace "da wanne yaren kenan" yace "France " girgiza kai nayi nace "sai nayi tunani tukunna" wata dariyar ya kumayi (bansan ada ya iya dariya mai kyauba sai yanzu kodan da bayayimin?oho) sannan ya maida fuskarsa serious yace "naga yadda furkaski ta canja lokacin da mama tayi maganar aure nasan kuma har zuciyarki ma ta canja dan haka nake rokonki dan Allah karki saka abin a ranki ya dameki ya hanaki bacci,  ban shirya zuwa asibiti gobe ba kinji mi Sœur " ya karasa yana murmushin tsokana, nima murmushin kawai nayi na kada kai ya kuma cewa kinyimin alkawarin zakiyi bacci?" Na daga kai dan yatsansa na karshe ya mikomin yace "pinki promise?" Dariya na fara na kasa bashi nawan yace "come on promise me" sannan nima na sakala nawa dan yatsan cikin nasa ina dariya, shima dariyar yake yace "wato bakyason France sai English ko? Mu kuma gamu ba turawaba" nace "sai mu ringa yin Hausa ba dole" kada kai yayi yace "lallai kin kawo shawara, OK bye idan kin kasa bacci ki kirani a waya kar ki sake kiyi tunani kinjiko?" Na daga kai kawai sannan ya daga min hannu ya wuce ni kuma na shiga gida.

FadimatuDonde viven las historias. Descúbrelo ahora