chapter 41

77 6 0
                                    

Bayan na hau sama wanka na kuma yi nayi shirin bacci sannan na zauna bakin gadona, a lokacin su Rumaisa har sunyi bacci dan haka na zauna sannan na dauko dan kwalin kyautar yaya Na'im na bude, wata sarkace mai dan banzan kyau kwadonta dan karami mai shape din star daga ciki kuma an kwakwile anyi shape din moon, ta azurface sai kyalli take tayi kyau sosai, cikin kwalin na kuma dubawa naga wata farar takadda da alama letter ce dan haka na ajiye sarkar kan bedside drawer dina gaban hoton Saif na dauko letter din na bude na fara karantawa "mi sœur you are the moon that can never get away from the star called Na'im and I will never give you up no matter what happen I won't let this moon go. I love you and happy birthday."
Na dade ina karantawa ina maimaitawa shikenan ta faru ta kare wai hausawa sukace anyiwa mai dami daya sata, dama ina ta addu'a kar Allah ga bashi ikon furtamin yana sona amma sai da ya fada, dama nasan duk wannan abin da yake inda zashi kenan kuma gashinan yazo wajen. Sarkar na dauko ina Kara kalla, sai yanzu na fahimci abinda take nufi, wato nice moon din dake tsakiyar sarkar shi kuma star din daya zagayeta, har wajen asuba banyi bacciba dayake Allah yasa bana sallah kawai sai nayi kwanciyata har baccin ya daukeni.
Firgigit na farka ina salati, a hankali na fahimci ashe mafarki nayi dan haka na sauke ajiyar zuciya sannan na koma na kwanta, ba kowa a dakin duk sun fice nan na fara tuna mafarkin da nayi wai naje ina cewa da yaya Na'im na karbi soyayyarsa ina sonsa kawai sai ya rikide ya koma min Saif yana cewa "alkawarin da kikayimin kenan? Kin manta dani kenan? Kina tsammanin son da yake miki yakai nawane? Kin gaji da jiranane? Kin min adalci kenan?" Irin tambayoyin da ya rinka yimin kenan wasuma har bazan iya tunasuba, ina ja da baya kuma yana bina har nayi untube da wani abu na tafi zan fadi shine na farka. Juyawa nayi na kurawa hotonsa dake kan bedside dina ido, nikam na rasa ma menene zanyi idan nayi tunanin yadda da ya rasu sai naji zuciyata tana gayamin yana raye idan kuma nace yana raye sai mutane su rinkayimin kallo mahaukaciya. Har azahar ina kwance a wajen toilet kawai naje na dawo na cigaba da kwanciya ina tunani da neman mafita. Sai la'asai ammie tazo tace na taso haka na shiga mutane kwanciyar ta Isa haka, dole na tashi naje nayi wanka na shiga wajensu momy.
Tun daga lokacin ban yiwa yaya Na'im magana akan letter dinba shima baiyiminba tun ranar ya turomin text a waya yace "nasan baki shiryawa soyayyataba amma duk ranar da kika shirya ina nan ina jiranki kisa sarkan aduk ranar da zuciyarki taji zata iya karbata a matsayin masoyi".
Mun koma rayuwarmu kamar yadda muka saba kullum muna tare da yaya Na'im idan nazo gida idan ina makaranta kuma muna tare a waya har muka gama wannan session din zan shiga level 300 su Rumaisa kuma sukayi graduation, a lokacin kuma maganar aurensu ta taso dama kowacce da mai sonta kuma gida sunsan da zamansa su kawai ake jira su kammala karatu, nan da nan aka Kawo kudin Rumaisa da saurayinta muazzam bayan sati daya kuma aka Kawo na Rufaida da nata Abdullahi. Ai kuwa kamar daman jira ake nan kowa yayo kaina kamar zasu cinyeni wai nima sai na fito da miji idan ba hakaba kuma zasu zabarmin da kansu, wannan karan kam babu wanda nake kaiwa kukana ya sharemin hawaye kowa nayiwa magana sai ya nuna ai hakanne daidai tunda na girmi su Rumaisa amma gashinan zasuyi aure su barni. Ranar da akayimin wannan tijarar nayi kuka kamar raina zai fita hatta dadyna ma ya juyamin baya Na'im kawai nake da shi shi kuma idan har ina da kunya bai kamata naje masa da irin wannan zancenba.
Ina kwance a daki ina tunanin mafita dan gaskiya ya kamata na nemowa kaina mafita tun kafin ruwa ya karewa dan kada, shekaru uku kenan ina zaman jiran Saif babushi babu alamarsa ya kamata na hakura dashi nai moving on a rayuwata kuma, ina da masoya yan diehard akaina saboda bayan yaya Na'im akwai kusan mutum biyu zuwa uku a makaranta wadanda da ace zance su fito na tabbatar zasu fito ba tare da bata lokaciba, amma duk su abarta tasu ma ga dan uwana nan mai zai hana na faranta ran iyayena dashi? Amma wata zuciyar tana gayamin kamar bazanji dadin auren yaya Na'im ba saboda munyi kusa dashi da yawa, kuma gashi a gidanmu zan zauna idan na aureshi kamar abin ba tsari, haka dai nayi ta tubka da warwara ni kadai har su Rumaisa suka shigo suka tarar dani a kwance, zama Rufaida tayi akan gadona tace "Fadima yaya dai menene yake damunkine?" Kai na daga na kare mata kallo sannan na tashi zaune sosai nace "Rufaida kinsan abinda yake damuna kinfi kowa sanin matsalata na kuma rasa mafita na rasa yadda zanyi wallahi, shekaru ukune fa kawai idan nayi aure nayiwa Saif adalci kenan? Idan ya dawo fa?" Murmushi tayi tana gyara zama sannan ta kamo hannuna tace "Fadima babu Wanda zaice bakiyiwa Saif adalciba saboda iyayensa Kansu sun fitar da rai dashi sun hakura sun yadda ya rasu, Fadima ko bai rasuba ke kinsan bazai iya rayuwa a wannan dajinba sannan gaba daya dajin zagaye yake da yan boko haram suna ganinsa a matsayinsa na soja kinsan ba barinsa zasuyiba ki yadda da kaddararki mana ki hakura kiyi aurenki ke kiyi farin ciki iyayenmu suyi farin ciki, me zaki zauna kiyi a gidan alhalin mu zamu tafi? Kina tunanin zaman zaiyi miki dadi? Fadima kinada masu sonki Mal Nura ba karamin so yake mikiba nasani kinga idan kika aureshi zakuyi zamanku cikin makaranta ki cigaba da karatunki bayanshi Yayana ma nasan yana ciki duk da kunki ku fada dagake harshi amma kowa yasan yaya Na'im sonki yake kema kuma kina sonsa dan haka ki tsaya kiyiwa rayuwarki adalci kar lokaci ya kure miki" shiru nayi ina saurarenta har ta gama sannan nace "lokaci ya kuremin kamar yaya?" Ta bani amsa da "eh lokaci ya kure miki mana Fadima, shekarunki kullum Kara tafiya suke yanzu cikin shekaru 22 kike kinga mazan dake zuwa neman auren naki zasu kare kenan nan da wasu shekaru kalilan, shima yaya Na'im zai iya samun wacce take sonsa ya rabu dake ya koma kanta yayi aurensa kinga kuwa ai lokaci ya kure miki" gabana naji ya fadi dana hasko Na'im da wata macen a matsayin mata, da sauri na kurama Rufaida ido nace "yanzu yaya Na'im zai iya auren wata kenan?" Dariya ta fara tace "me zai hana? tsab zai auri wata ni najima kamar su dady na maganar shima ya kamata ya fito da mata duk a hadamu kinga kuwa zai iya sabule miki kenan" zuciyata naji ta fara zafi kawai na koma na kwanta na juya mata baya. Yanzu idan na karbi soyayyarsa tabbas zaice dan naga bani da wanine yasa na yadda dashi kuma banaso ya Kawo wata daga waje.
Ranar dai ban fito daga wajensu ammie ba sai bayan la'asar na tafi garden, wajen water fountain dinnan naje na zauna ina kallon kifayen dake sha'aninsu kamar basu da waya matsala koda yake dama basu da matsalar, ina zaune na kafawa wajen ido naji alamar an zauna kusa dani, a hankali na dago kaina na kalleshi yayi min kyau sosai cikin kananan kaya da alama kuma yaje wajen aski yau gyaran fuskarsa yayi kyau sosai ya fito tas dashi, ido kawai na kafa masa ina kallo ba tare da nasan inayiba sai daya busamin iska a fuska sannan na lumshe idona ina sauke ajiyar zuciya, musmushi yayi yace "wannan ai sai ki cinyeni irin wannan kallo haka" wata kunya naji ta kamani nayi saurin rude fuskata ina dariya yace "kinga bude fuskarki ki cigaba da kalla ni da zaki cinyeninma da ai ba hakaba" fuskata na bude na zunburo baki nace "na cinyeka sai kace wata mayya?" Yar dariya yayi yace "eto baza'ace miki mayyaba kam tunda gashinan kinaso amma kina kaiwa kasuwa mayu kam idan sunaso ai kwaf daya sukeyi" hannu na saka a ruwan ina wasa dashi nace "me nake so nake kaiwa kasuwa?" Kamar Wanda dama yake jira azonan yace "ni mana" kai na dago ina kallonsa nace "kai kuma?" Yace "eh mana kina sona kina nuna kamar bakyayi kuma duk wanda ya zauna dake yasan kina sona" kallonsa na kuma tsayawa inayi kafin na mike tsaye hawaye na zuba a idona nace "akan wanne dalili zaku rinka yankemin hukuncine? Kaf cikinku akwai Wanda yasan menene a zuciyata da zaku rinka cewa ina sonka? Banason irin wannan ni bance inason kowaba da zaku rinka yankemin hukunci da hasashenku" tashi yayi shima tsayen yace "to Fadima me yasa bazaki soniba? Menene laifina?" Ayanzu kuka nake sosai nace "ni ba cewa nayi bana sonkaba amma idan na karbi soyayyarka banyiwa Saif adalciba me zance masa idan ya dawo?" Gabana ya dawo sosai yace "Fadima ba wai son Saif kikeba kina ganin kamar kinci wani bashinsane da ya zama dole ki biya, Fadima Saif baiyi miki abinda yayi miki domin ki biyashi da kankiba yayine domin Allah domin yana sonki sannan yanzu baya duniyar balle kice sai kin biyashi bashin da kikaci masa Fadima you have to move on rayuwar yar kadance" ina goge hawayen dake zirya a kumatuna wasu na fitowa nace "idan kuma bai mutuba fa? Idan kuma ya dawo fa?" Kallona Na'im ya tsayayi na wasu seconds sannan yace "idan ya dawoma zai fahimceki, kin jirashi na tsahon shekaru uku da wani abu sannan danginsama sun fitar da rai dashi amma ke baki fitarba dan haka zai yadda dake zai fahimceki" komawa kawai nayi na zauna kaina har wani sarawa yake na rasa mafita kaina kuma kullewa yake. Zamashima yayi a kasa a gabana yace "Fadima wallahi ina sonki sannan nayi miki alkawarin cigaba da sonki har karshen rayuwata, bazance bazan taba hurting nakiba amma zan iya alkawarin I will try my best naga na zame miki mijin da ba zaki taba danasanin auraba" ido kawai ya zubamin ni kuma nama rasa inane zansa rayuwata banda ajiyar zuciya babu abinda nake, zuwa can yace "Fadima kiyi magana mana dan Allah ki bani chance zakiyi mamakin irin son da nake miki" kallonsanayi nace "shikenan yaya Na'im na yadda da soyayyarka na yadda Zan aureka amma da sharadi" da sauri yace nama yadda ko menene" ban kula masar tasaba nace "sharadina shine ko an zauna daurin aurenmu Saif ya dawo na fasa" shiru yayi yana kallona zuwa can yace "na yadda".

Sarkar birthday din Fadima daga Na'im.

Sarkar birthday din Fadima daga Na'im

¡Ay! Esta imagen no sigue nuestras pautas de contenido. Para continuar la publicación, intente quitarla o subir otra.
FadimatuDonde viven las historias. Descúbrelo ahora