Chapter 49

83 7 0
                                    

Not edited
Wata takardar ya zaro a bayan wadda ya zana hotona yace "wannan fa?" Dago kai nayi ina allonta, fuskar wata yarinyace da ba zata wuce shekaru 13-15 ba kyakykyawace sosai tanada dogon hanci da manyan ido ga gashi ya zubo kan kafadarta, tubarkallah yarinyar tayimin kyau sosai, kallonta na tsayayi na wani lokaci sannan na kalleshi muka hada ido ashe shima ni yake kallo, maida idona kan takardar nayi ina girgiza kai nace "bansantaba" dan murmushi yayi yace "dama bazaki santaba dan baku taba haduwaba amma batayi miki Kama da kanki?" Kallonta na kumayi tayi kama da hoto sosai kamar ba zaneba kamar zaka kira sunanta ta amsa, abu daya zan iya cewa nawa da nata sun danyi kama shine ido,  kai na kuma kadawa nace "ni dai ban ganiba" juyowa yayi sosai yana kallona yace "kin tabbata?" Kai kawai na daga ya kalli hoton da kansa yace "to kodai nine nake ganine? Ko kuma a lokacin da ina kishirwar ganinkine naga kuna kama? Allah kuwan ni dai kamarku nake gani" karbar hoton nayi nace "towai wacece ne wannan din idan 'yar uwatace kaga dama dole aga kama ta jini ko?" Yace "ba 'yar uwarki bace murjace yar gidan Baba Wanda na zauna a wajensu a askira" kai na fara kadawa wani tausayin yarinyar na shigata nace "Allah sarki baiwar Allah yanzu tana ina?" Juyawa yayi ya jingina da gadon da muke zaune a gabansa yace "a camp na barota bansaniba ko tanacan ko tayi wani wajen?" Wani hawayene ya tararmin na tausayin yarinyar yarinyace 'yar karama amma an zalinceta saboda rashin tausayi nace "amma ya zaka barota a can alhalin kasan komai zai iya faruwa da rayuwarta? Sojojinnan fa sunfi yan boko haram din rashin imani sunfish son mata please ka daukota daga wajen" juyowa yayi yana kallona da sakakken baki, ganin ya kafamin ido nayi saurin goge hawayen da ya zubomin na sunkuyar da kai amma bai daina kallon nawaba bai kuma rufe bakinba. Dagowa nayi na kalleshi nace "dan Allah ka daina kallona haka me nayi?" Yace "ohh baakima San me kikayiba ko? Bakima San me kikace ba ko?" Shiru nayi ina tunanin abinda nace ganin bazan tuna laifi a cikiba na girgiza kai ai kuwa ya zauna sosai yace "wato mu sojoji munfi yan boko haram rashin imani ko? Mun fisu son mata ko? Kinsan kuwa su waye yan boko haram din? Wato namafisu zalinci ko?" Har ga Allah ni nama manta shi sojane dan haka nayi saurin rufe baki ina dariya nace "ayya Yayana ba haka nake nufiba kaga ai ba cewa nayi dukkan sojojinba amma kasan dai yawancinku haka kuke ko? Amma ai kai na musamman ne" na fada ina cigaba da dariyata, mikewa yayi ya fara hada kayan zanensa ya wuce wajen table din da suke ransa a bace, hankalinane kuma ya tashi nima na mike nabi bayansa ina cewa "haba Yayana wallahi ba haka nake nufiba kawai dai nafison ka daukota daga wajenne amma ai ba cewa nayi kaima haka kakeba ni wallahi nama manta kaima sojane Allah kuwan" juyowa yayi da sauri har muka kusa yin Karo nayi baya da sauri, fuskashi ya turbine na fara ja da baya yana biyoni har muka koma bakin gadon sannan ya hankadani ya juya ya cigaba da abinda yake yana cewa badai kince mu mugaye bane? Zaki gane kuranki" tashi nayi na zauna ina kallonsa tsakani da Allah baya overreacting? Yana gama abinda yake ya kuma juyowa a fusace ai kuwa na mike nayi hanyar waje da gudu yayi sauri riko hannuna yana dariya "zo zo kiji kanwata da wasa nake miki kinsan dai koni azzaluminne ke kam bazan mikiba magana zamuyi" da kyar na tsaya amma fa na tsorata dan haka nace sai dai ya zauna a farkon gadon na zauna a karshe yace ya yadda.
Fuskarsa ya maida serious yace "fatima wai yaya zamu tsara future dinmune? Next week zaki koma makaranta ya kamata musan halin da muke ciki, zinder da kaduna ba kusa bane, ya kike ganin zamuyi?" Shiru nayi ina tunani tabbas garuruwan ba kusa bane ta yaya zamuyi zaman aure alhalin ni ina zinder shi yana Kaduna? Ganin bance komaiba yace "ina ganin abu dayane zamuyi, na karasa retire na idan yaso sai na fara kasuwancin da nayi niyya tun farko kinga idan ya zamana business nake zan iya zuwa wajenki a duk lokacin da nakeso babu mai hanani babu wanda zan tamabaya" nan ma shiru nayi can yace " fatima kinyi shiru ki yi magana mana" kai na dago na kalleshi sannan na kuma dauke kai na rasa dalilin da yasa yanzu bana iya kallonsa, nace "gaskiya ban yaddaba saboda kanason aikinka bazaka rabu dashi sabodaniba" masowa yayi daga karshen gadon da da na kaishi ya nade kafarsa daya a kan gadon daya kuma a kasa ya kamo hannuna duk biyun yace "fatima inason aikina amma nafisonki nafi son zama dake sama da aikin 2yrs fa kafin ki gama bazan iya jiraba" dan murmushi nayi nace "ayya Yayana menene shekaru 2 muka zauna jiran juna na shekaru huduma balle biyu? Karka manta wancan zaman ma munyishine ba tare da sanin halin da juna ke cikiba, amma yanzu zamu rinka waya zamu iya ganin juna koda sau dayane a shekara sannan munsan akwai ranar da hakan zai kare wancan fa? Bamu da tabbas din zai kare bare mu san sanda zai kare din" shiru yayi yana kallona jijiyoyin kansa har sun fara tashi yace "amma fatima..." Dan yatsa na dora kan bakinsa nace "shishhh bazan barka ka ramu da aikinka dakasha wahala akansa sabodaniba, karka manta ba iya business kayiba kanaso ka koma jobless alhalin kayi aure?  Kawai ka yadda a ranka we can do this together OK?" Dan murmushi yayi yace "yanzu zaki iya rayuwa shekaru biyu babuni?" Nima dan murmushi nayi zuciyata na gayamin bazata iyaba amma sai cewa nayi "as least I know that you are alive somewhere in this world ba kamar waccan hudun da kullum ake gayamin ka mutuba, kaga bazan zama as miserable as wancan karonba" caressing kumatuna yayi yace "I'm sorry" wani hawayene ya zubomin kawai na kada kai dan bazan iya bude baki nayi wata maganaba.
A ranar yayiwa mama magana akan murja washe gari yace nazo muje nayi masa rakiya. Maiduguri muka tafi farkonta kafin ka shiga ciki bansan sunan wajenba anan naga wani camp na yan dugin hijira, wajen filine Babba mai yashi sosai ga mutanenan kamar kasa babu kyan gani, kana ganinsu kasan suna cikin wahala dan nayiwa da yawansu kuka, ya kamata masu halinmu su rinka taimakawa irin wadannan wajen da duk abinda Allah ya hore musu koda kuwa soyayyace kawai, suna cikin mawuyacin hall babu ishashshan abinci babu kayan sakawa ga sanyi babu abunuwan rufa yan yara sai kuka suke abin gwanin ban tausayi. Wajen wasu sojoji Saif ya tafi sukayi maganganu sannan yazo yace nazo muje. Da muka shiga cikinsu kuwa nayi kuka kamar me dan har saida na fara wannan hakin Saif ya daukoni ya dawo dani mota shi kuma ya koma neman murja bayan ya bani ruwa na sha na dan dawo hayyacina. Bayan tafiyarsa na kwantar da kujerar motar na kwanta na lumshe idona dan ba karamin zafi zuciyata takeba akan abinda na gani yau a camp dinnan, ina kwance ya dawo ya zauna a motar yace "you OK?" Kai kawai na kada masa ya cigaba "ban sametaba wasu wadanda suka santa sunce ta shiga cikin gari amma yanzu zasu dawo my jirata ko?" Nanma kai kawai na kada masa. Munanan zaune nace "wai da su nawane 'ya'yan baban?" Wayar da yake dannawa ya ajiye yace "su ukune maza biyu mace daya amma gaba daya sun mutu saura ita kadai" kai na jinjina ina kara jin tausayinta. Zuwa can wasu yan mata su uku suka dan gota motarmu da sauri Saif ya bude motar ya fita yana kiran "murja" ta tsakiyafce ta waigo ai kuwa tana ganin sa ta zubar da abinda ke hannunta ta taho da gudu ta rungumeshi ta kuka "yaya ina ka tafi ka barni na zata kaima sun kasheka yaya nayi ta nemanka ban gankaba dan Allah karka kara tafiya ka barni bani da kowa a duniyarnan sai kai dan Allah karka kara tafiya ka barni" kuka take sosai tana sambatu Wanda nima ya sakani kukan fitowa nayi na zagayo nasa hannu ina dan shafa bayanta, sai da ta gama kukanta sannan ya dagota yace "murja kinga ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki bazan sake tafiya na barkiba yanzuma zuwa nayi na tafi dake zaki bini ko?" Kai ta kada tana goge hawayen idonta, Saif yace "kinga antynki bakiyi Mata maganaba" da sauri ta juyo tana kallona sai kuma dariya, rungumeni nima tayi tana cewa "lahh Anty fatima ai bangankiba" sakina tayi ta kalleni sannan ta juya ta kalli Saif tace "wallahi kuwa yaya da gaske tafi kyau a fili" dariya gaba daya mukayi. Bamu muka dawo kanoba sai 12 na dare muna zuwa muka kwanta bacci sai washe gari aka gabatar da ita wajen su mama wadanda dama da saninsu da yaddarsu muka daukota.
Ranar juma'a na koma Niger tare muka koma da maryam da Anty Aisha matar yaya nuru babban yayansu Saif da kanwar babarsu da kanwar babansu da Saif saboda suyi mana rakiya, bayan munje gidan Abba suka sauka sai dare suka kaita gidan yaya Na'im bagan munyi 'yar walima ta iya kacinmu yan gidan, anyi niyyar maidawa maryam kayan lefena amma Anty Rayya tace "aa ai itama da nata kayan wannan nawane yace yabarmin" ai kuwa muna raka maryam saiga kayan lefenta Anty Rayya ta kawo abinda ya bawa kowa mamaki harshi kansa yaya Na'im din saboda ashe uncle sagir ne ya bada kudin ta hado. Bayan an gama komai ranar Sunday Saif ya maidani makaranta, da zai tafi kamar ba zamu rabuba har da dan kukana inajin kamar idan ya tafi zai sake batane, banason rabuwa dashi kona minti daya, wani abin mamaki shine tunda aka dauramana aure shikenan gaba daya naji yaya Na'im ya fita a raina a matsayin masoyi, ina jinsa tamkar Halifa na damu dashi dai sosai ina jinsa kamar wani sashe nawa amma ba ji na soyayyaba ji irin na dan uwa.

AFTER TWO YEARS
Ayau makarantar abdou moumouni dake zinder ta kasar niger take bikin yaye dalibanta da suka kammala karatun degree na farko, nima Fadima Kabir Ahmad ina cikin daliban da sukayi katarin kammala karatun, na sami second class upper honour a fannin mass communication, yan uwana da yawa sunzo tayani farin ciki da mijina abin alfaharina, Rumaisa da Rufaida kowacce tazo da dan jaririnta na Rumaisa mace na Rufaida namiji maryam kuma da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Naji dadin soyayyar dasuka nunamin duk da dama nasan ni yar gatace a wajen dangina.

Kuyimin afuwa kwana biyu na sami matsalar wayane gaba daya ta hargitse komai ya lalace shiyasa amma in sha Allah zaku jini yanzu ta dawo dai dai.

Two more episodes to go.
Thoughts and theorist.

FadimatuDove le storie prendono vita. Scoprilo ora