Can na hango momy jikin wata tsohuwa itama tana kuka nace waccan ce goggo kenan, ina cikin kallonsu naji an rungumeni da sauri nima na rungume koma wacece sai da ta dago naga wadda ta fara rungume momyce ta dago tana murmushi nima shi nake mata tace "Rumaisa kuzo ga yar uwarku" da sauri na kalli wadansa takewa magana wadannan yan matan guda biyu nace wannan sune kannen Tj kenan yan biyun da kullum yake bani labarinsu dan haka da sauri na hadasu duk su biyun na rungume ina cewa "oh my God Rumaisa Rufaida" suma rumgumeni sukayi muna farin ciki.
Ranar dai haka muka kwana ana rungume juna ana kuka da dariya, sai yanzu na gane da wadda muke kama ni da feena da goggon momy ne kamarmu daya danma ita jiki da jini ta tsufa amma kamar tamu ta fito sosai. Sai asuba feena ta farka muna baje a tsakar gida ta fito tana yamutsa fuska sai kuma ta kame kawai tana kallonmu ganin mutane da yawa a baje a tsakar gidan, ganin tana neman rikicewa na mike tsaye saboda ina tsakiyar yan uwa sai surutu nake nace "feena kin ganni nan taho" na fada ina mika mata hannu da sauri kuma ta taho jikina tana karewa mutanen kallo, dady na mata dariya yace "mama wannan yar autata kenan feena" da fara'a tace "tubarkallah yaki feena zonan" ta miko mata hannu ita kuma ta dane kafada ta kuma maida kai jikina, ina dariya nace "kinga feena ba rannan kinzo kina tambayata su waye grandmother da grandfather ba?" Ta daga kai da sauti na cigaba "yauwa to kinga wannan 'na Nuna abba' shine grandfather dinmu gaba daya wadannan kuma 'na nuna mama da goggo' sune grandmothers dinmu kije ki gaishesu" da sauri ta mike cikin farin ciki tana gaishesu bakinta har kunne, sai data gaishesu sannan ta dawo wajena tace "wadannan kuma su waye ko kuma grandmother dinne" kowa sai da yayi dariya saboda su Rumaisa ta nuna, nace Mata "aa su wadannan yayyenkine sunansu sister Rumaisa da sister Rufaida wannan kuma dady dinkine Abbie wannan kuma momynkice itama ummie wannan kuma ai kinsanshi ko?" Na tamabaya ina nuna Na'im da sauri kuwa tace "eh yaya Na'im" nace "yauwa good girl suma kije ki gaishesu" Haka mukayi ta murna dai ranar.
To Allah ya taimakemu idan Halifa ya dawo da daddare bayan normal kudin da ake tarawa na kayan abinci da sauransu akwai 1k da kullum ake ajiyewa da ba'a amfani da ita no matter what it's for emergencies dan haka dana dauko bankin da ake tarawa na tarar an tara kudi da yawa sannan jiya aka turomin salarina na zahra ko daukowa banyiba a banki sannan gana kayan abinci da aka tara tunda daman wata yazo karshe a ka'ida zamuje siyan kayan abinci, dan haka na tattara na bawa Halifa dukka tare da ATM card dina ya tafi siyayya zuwa can sai gashi da dukkanin wani abu da zamu bukata buhun shinkafa, katan na taliya, macaroni, kus kus jarkar mai, dankali, doya, kwai da sauran kananan kayan amfani sannan ya bani ATM card Dina yace baima dauko salarinba na hannunsa ma ya isah harda ragowa nan muka zubasu a kitchen sannan na nemo su Rufaida muka fara shirya abinda za'ayi breakfast dashi. Mun kusa gamawa Na'im ya shigo ya kare mana kallo sannan yace "da fatan dai kar ayi mana kwaba mu kasaci ko ayi mana kazanta a ciki" ko kallonsa banyiba sai su Rumaisa ne suka bashi amsa da "haba yaya sai kace yau muka fara girki?" Yace "eh gwara gwara ku maybe ku danyi abin arziki wasu kuma fitsara kawai suka iya" na fahimci dani yake dan haka na dago na kalleshi cikin ido dan na nuna masa bani da kunyar nace "eh shiyasa a ban iyaba naga har kwacen na mutane kake kana daukar Wanda ba'a bakaba" ina gama fadar haka na juya na cigaba da dama kunun da nake ban kuma kallonsaba ya gama surutansa ya fice su Rumaisa dai dariya kawai sukeyi mana.
Bayan an gama cin abinci nan aka fara labarin abinda ya faru bayan tahowar su dady. Bayan sun taho dukiya ta koma hannun sagir sai dai me? Kafin shekara ta dawo Komai ya lalace kamar wanda wani bala'i ya fadawa komai ya lalace, nan fa aka fara bibiyar me yake faruwa sai da akayi bincike sosai sannan aka gano sagir diban kudin kawai yakeyi yana bushasharsa dan haka suka fara fada da Abba yace duk wani kudi dazai shigo ko ya fita sai an sanar dashi kuma shi zai ringa mu'amala da customers dinsa. Nan fada ya kuma rincabewa aka bawa uncle Ibrahim ragamar komai duk da shi likitane ba harkar kasuwancin yakeba amma babu yadda ya iya dole ya karba ya hada da aikinsa, wannan abu fa ya kona ran sagir dan haka ya tari Ibrahim da fada yana cewa "duk wahalar da mukasha ni da mahaifiyata banda uban kudin da muka kashe dan muga mun share kabir daga gaban mahaifina amma sai ya zamana kai muka yiwa aikin? Shekaru biyu kawai da fara dandanar zumar arzikin ace za'a kwaceshi to wallahi baka isaba yadda na hadawa dan uwanka tuggun da ya bar gidannan kaima sai na koreka daga gidan" yana wannan maganar bai saniba ashe Abba na jinsa dan haka yace sai ya fasa masa wanne tuggu ya hadawa Kabir din shi kuma yaki fada wasa wasa abu dai har saida takaisu ga yan sanda sai da jikin sagir ya gaya masa sannan ya fadi duk yadda sukayi: maganar cocaine sanda ya rungumeshi a harabar gidanne ya saka masa a aljihu audio kuma ganarsa aka dauka sai sagir din yayi maganar da aka kunnawa Abba da aka saka a computer sai suka cire muryar sagir suka saka ta Kabir dan haka ya zamana kamar kabirne keyin maganar, ana cikin wannan umma ta Fara ciwo aka kaita asibiti sukace blood cancer ganin da gaske ta kamata yasa ta fadi duk yadda abin ya kasance da kuma asirin da tayiwa Abban ta rufe masa baki ya kuma yadda da duk abinda sukace masa aka kuma saka masa kiyayyar Kabir din mai tsanani ya mantashi gaba daya, sai da yaji wannan maganar da sagir keyi sannan asirin ya karye. Jin wannan makirci da aka shiryawa Kabir nan Abba ya fadi ranar a asibiti ya kwana tun daga ranar kullum cikin tashin hankali babu inda bai nemaba amma ya rasa Kabir kullum zancensa a nemo masa Kabir dinsa ya nemi yafiyarsa. Haka suka cigaba da lallashinsa tare da kwantar masa da hankali har Na'im ya girma dan haka ya maida kasuwancinsa hannun Na'im sannan ya dau son duniya ya dorawa Na'im kullum yana cikin rokonsa akan ya nemo masa Kabir ya nemo masa Kabir kamar karatu, bayan bayyanar gaskiya da shekara guda umma ta rasu bayan ta nemi yafiyar mijinta da kishiyarta sannan ta roki duk ranar da Kabir ya dawo a nema Mata gafararsa ko Allah zai sassauta Mata.
To bayan neman kabir na shekaru goma sha biyar bayan barinsa gida da shekaru goma sha takwasa kwatsam jiya da yamma kawai suna zaune sai ga Ibrahim ya shigo yana bawa Abba waya wai Na'im ya Kira waya daga Nigeria yace kuma maganace mai muhimmanci nan aka saka wayar a hands free Na'im ya fara magana da dashashshiyar murya kamar wanda yasha kuka yace "Abba albishirinka" Abba yana dariya yace "goro dan gidan Abba mata ka samominne" da sauri yace "eh Abba harda matarma amma da na fara samo maka Abba naga uncle Kabir da Anty kubra" nan da nan kowa ya shiga nutsuwarsa jikin Abba har karkarwa yake yace " alhmdulillah Na'im a ina ka gansu yaushe zaku taho? Kabir na cikin koshin lafiya ko? Kace masa ya dawo gida nayi kewarsa" muryar Na'im na rawa kamar mai kuka yace " Abba bashi da lafiya yace bazai tahoba sai ya warke na gaya masa gaskiya ta fito amma yace sai ya warke zai dawo" nan da nan jikin Abba yayi sanyi yace "Na'im har yanzu fushi yake dani ko? Dama na sani Kabir nada zuciya kuma nayi masa laifi mai girma shiyasa dama nasan bazai yafeminba" kawai sai kuka dan tsoho abin tausayi, shima Na'im kukan yake haka ragowar yan dakin, cikin muryar kuka Na'im ya cigaba da cewa "Abba ka kwantar da hankalinka ya yafe maka na tabbatar ya yafe maka amma bashi da lafiyane shiyasa bazai taho yanzuba, amma Abba inason idan zaka iya yanzu Abbie ya siyo muku ticket na Nigeria kano ko Lagos ku taho idan ya ganka kazo da kanka zai dawo gida kaji Abba zaka iya?" nan da nan Abba yace "me zai hana tunda a jirgine ko a motane zanzo indai wajen kabirne" nan da nan suka Fara shiryawa amma sai sagir Wanda yanzu ba karamin laushi yayiba yace shikam bazaizoba kunyar Kabir din yakeji idan ya dawo gida sa hadu, a daren gaba dayansu suka shirya yan biyu ma anso su zauna sukaki dan haka suka dunguma a motoci gaba daya sai Niamey babban birnin Niger republic suna zuwa kuwa da la'asar suka yi sa'a suka sami jirgin da zaizo Lagos karfe 7:00pm suka hau wani daga Lagos zuwa kano wajen karfe 9 na dare Na'im ya daukosu a airport ya wuce dash masaukinsa sai da suka huta sukaci abinci Abba ya kafa rigimar shifa sai an kaishi wajen Kabir dinsa babu yadda basuyi dashiba akan ya hakura sai da safe amma ganin da gaske yake dole suka daukoshi zuwa gidan su fadimatu a wannan daren.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...