Sun taso cikin gata da kulawa ta iyaye babu abinda suka nema suka rasa, ta fannin karatu ma iyayensu sun tsaya musu boko da islamiyya kuma alhmdulillah yaran suna da kokari sosai kamar su sukayi kansu aji daya suke tafiya tamkar twins dama kuma gasu Kansu daya
Akwai soyayya da shakuwa sosai tsakanin yaran da iyayensu musamman dady yana ji dasu sosai wannan yasa duk inda yake indai yana kasar to la'asar a gida takeyi masa sannan baya zuwa ko Ina da weekends yakance wannan lokacin iyalinsane zai zauna suyi kallo tare suci abinci tare suyi sallah tare wani lokacin har baccin rana tare sukeyi shi da yaransa idan momy tayi magana sai yace" haba kubra bayan ke , Halifa da Fadima wa nake dashi kaf duniya? Idan ban so ku ba ai nayiwa Allah butulci" idan ya fadi haka shikenan ya kashe Mata jiki baka kuma Kara wata magana kenan.
Shekarar Halifa sha biyu Fadima sha daya suka kammala primary school tare da saukar alqur'ani mai girma Fadima ce mafi kankantar shekaru a cikin wadanda sukayi saukar dan haka da ta fito ta rera karatu gaban dubban jama'ar da suka halarci saukar ta samu kyaututtuka da yawa saboda ta birge mutane da yawa haka iyayensu sunyi alfari da ita sosai tare da dan uwanta. Bayan sun koma gida suna zaune ana duba kyautututukan sai dady yace " to alhmdulillah yanzu dai primary ta kare kuma kun fito da sakamako mai kyau kamar yadda mukayi tsammani ga wani abin farin cikin na sauka da kukayi dan haka inaso kowa ya fadamin abinda yakeso nayi masa a matsayin gift na sauka da graduation" cikin farin ciki suka hada baki wajen cewa "study abroad dady" momy dake yanka fruits cikin dan plate ta dago tana kallonsu da mamaki tace "abroad kuma sweathearts?" Suka sake hada baki da cewa "yes momy" dariya dady yayi yace wannan dai da alama kun gama hada plan dinku tun daga daki KO? To wacce kasa kukeso?" Again a tare suka amsa " Korea dady" nan da nan momy ta hade rai " bazai yiyuba wannan shirin fadima ne kuma ba karatun zataje ba wata manufa can ke gareta dan haka ban yaddaba" tana kaiwa nan ta mike tabar falon, da sagaggiyar gwiwa suke kallonta har ta bacewa ganinsu sannan suka juyo suna kallon dadynsu dan jin mai zai ce amma ga mamakinsu sai kawai ya daga kafada alamar ba ruwansa ai kuwa tamkar zasu zunduma ihu karma fuskar Fadima taji lbr dan har ta fara hawaye Halifa kuwa ganin hawayen sister dinsane ya tayar masa da hankali nan da nan ya rarrafa zuwa wajen dady yana rokonsa "dady dan girman Allah kayiwa momy magana nasan indai ka amince itama zata amince wlh Fadima na son zuwa kasar plss dady do something" dady yana mikewa yace "gaskiya Halifa abin nakune yayi yawa Korea a wannan shekarun naku? Kunyi kankanta nima bazan yaddaba sai dai idan kun yadda ku fara secondary anan idan kuka kammala junior sai akaiku can din ok?" Halifa da dama tafiyar ba tasa bace ya juya ya kalli Fadima kallon Neman shawara kai ta daga masa alamar ta yadda sannan yace da dady "shikenan mun yadda amma dady Ina zamu Fara?" Dady na bin bayan matarsa ya bashi amsa da "Allahu aalam" ba karamin bakin ciki sukayi da wannan hukunci na iyayensuba sai dai babu yadda zasuyi dole su hakura amma duk da haka sai da Fadima Tasha kuka kamar Idonta zai tsiyaye hankalin Halifa kuwa ba karamin tashi yayiba gaba daya suka koma kamar wasu marasa lafiya sai da aka kwana biyu sannan suka ware suka koma normal.
Su Fadima suna enjoying holiday dinsu saboda momy da dady suna kaisu yawo kullum da inda zasuje Yau suna gidan zoo gobe dutsen dala jibi minjibir park haka dai babu ranar da zasu wuni gida dole akwai wani waje da zasuje duk dan a rama musu abroad din da aka hanasu zuwa kuma ba laifi hakan ba karamin dauke musu hankali yayiba yayinda shi kuma dady yake processing ci gaban karatunsu a makarantar da suka gama primary da yake akwai secondary a ciki. Bayan hutunsu ya kare suka cigaba da zuwa schl. Babu abinda ya canja daga halin Fadima sai Wanda ya karu, da yake mix school ce maza da Mata shiyasa har yanzu ajinsu daya da Halifa desk dinsu daya komai tare sukeyi ko break aka fita tare suke cin abinci haka friends dinsu zasuyi tayi musu dariya aikuwa wani na yi musu dariya to tamkar ya kunna Fadima ne zata fara masifa da kyar Halifa zai samu ya shawo kanta tayi shiru wannan yasa duk class din tsoronta suke.
Haka rayuwa ta cigaba da garawa awanni na zama kwanaki kwanaki na zama watanni watanni na zama shekaru har su fadima suka kammala jss 3 a lokacin Halifa yayi girma sosai da yake yana da manyan gabbai yana 14yrs amma idan ka ganshi zakayi tsammanin ya Kai 16 ko 17yrs inda Fadima kuma take yar mitsitsiya kullum kamar ana zuketa bata da jiki ko kadan dan wani lokacin idan shagwabarta ta tashi sai tace Halifa sai ya goyata kuma haka zai goyatan ba tare da yaji komaiba. Ana haka kwatsam rannan momy ta fara ciwo ana zuwa asibiti doctor ya tabbatar da shigar ciki na wata biyu nan fa aka fara murna kaf gidan ba Wanda baya murna da wannan ciki shiri suka fara tamkar ance gobe za'ayi haihuwar karewar hutunsu na gabatowa suka tunawa dady alkawarin da yayi musu dan haka yace su bari zai kara tuntubar momy ko zata yadda ai kuwa ba karamin ruwa akakai rana da itaba kafin ta yadda tace ita batason kawai ta dauki yarinyarta mace takai wata kasa can da ba Allah suka saniba gwara ma namiji amma ba karamin risk bane akai mace wata kasa duba da shekarunta da yanayin jikinta sannan kuma Fadima tana da passion sosai akan Korean celebrities dan haka ba karatunne a gabantaba haka dai yayi ta lallabata akan zasu samu wanda zai saka musu ido akan yaran sannan daga nan zasu rinka musu addu'a yadda ya kamata duk term kuma zasuje musu hutu da kyar dai ta yadda nan aka shiryasu sai Korea.
Suna zuwa akayi musu komai dama sun gama duk wasu formalities da school din ta internet dan haka suna zuwa tare da rakiyar momy da dady aka basu komai daya kamata da class da hostel da komai. Sai da sukazo yin sallama da iyayen sannan Fadima ta saka kuka bataso su tafi su barta momy kuwa mota kawai ta koma KO rarrashinta bata tsayayiba domin itama tana bukatar wanda zai rarrasheta wani irin feeling takeji na taso mata abinda ya faru shekaru da yawa ya fara dawowa kanta tamkar yanzu yake faruwa dan haka ta sha kuka har numfashinta nayin kamar zai dauke. Dady ma dakyar ya samu ya rarrashi yaran nasa shima da jan idonsa sannan ya taho ya barsu rungume da juna suna ci gaba da kukansu gwanin tausayi bayan sun daina ganinsu Halifa ya kama hannun kanwarsa har kofar dakinsu yayi ta rarrashinta sai da yaga tayi dariya sannan ya rabu da ita zuwa nashi dakin.
Bayan tafiyar su fadimatu da watanni bakwai momy ta haihu mace kyakykyawa kamarsu daya da Fadima babu kuma Wanda yasan da Wanda suke kama domin basa Kama da dady basa kama da momy gasunan dai halifane kawai ke Kama da dady kamar an tsaga Kara har girman jikin. Fadima har da kuka saboda an hanasu zuwa ganin baby sai pics kawai suka gani, sai da babyn tayi kwari sannan sukaje har Korean suka kai musu babyn mai suna Safeena. Aikuwa Safeena taga soyayya tamkar zasu hadiyeta haka sukeji da zasu tafima kamar kar su rabu da ita haka dai suka hakura. To da yake dama Fadima ba karatunne ya kaita Korea ba sai yazamana gaba daya kokarin nata yaja baya akwai wani dan ajinsu Lee yoo shing da halinsu yazo kusan daya babu abinda sukeso irin suje ganin celebrities yau suna kofar wannan company gobe suna kofar wancan studio ita dai kawai burinta taga yan film da mawakansu idan kuwa ta fara yarensu sai ka dauka da ma can yar kasarce, haka zata zauna tana mimicking abinda akai a finafinai kamar wata yar cikinsu, babu yadda Halifa baiyiba dan ya rabata da wannan muguwar halayyar tata amma taki dainawa idan ma ya takurata sai tace ta daina hankalinsa na komawa wani wajen zata nemo yoo shin sai dai ya nemesu ya rasa. Ai kuwa result na fitowa sai ga fadima da daukar ta karshe da 35% average ai kuwa ranar taga bacin ran da bata taba ganiba a wajen Halifa dan har marinta yayi sannan yace da yasan abinda zatazo tayi kenan wlh da bazai goyi bayanta zuwa wannan kasar ba sannan zai gayawa dady a maidasu Nigeria.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...