Chapter 26

77 7 0
                                    

Nayi zaton Na'im fushi yayi saboda rashin kunyar da nayi masa sai daga baya Halifa yake gayamin Niger ya koma dama shi acan yake kasuwanci ke kawoshinan sannan da duba Tj dake karatu anan.
Ranar lahadi Saif yake cemin gobe zai koma wajen aiki, dama nasan goben zai koma amma wannan Karon daya gayamin sai naji tamkar na dora hannu aka nayi ta kuka, banason ya tafi zuciyata wani irin bugawa takeyi ga wani mugun tsoro daya kamani, kallonsa kawai na tsaya inayi sai daya busamin iska a fuska sannan na sauke ajiyar zuciya yace "yadai irin wannan kallo haka" marairaice fuska nayi nace "banason ka tafi" shima ajiyar zuciyar ya sauke yace "nima banason tafiya Fatima babu yadda zanyine shiyasa, ban taba danasanin aikin dana zabarwa kainaba sai dana hadu dake, nafison koyaushe na kasance tare da ke amma babu yadda zanyi" shiru mukayi duk mu biyun zuwa can ya sake wata ajiyar zuciyar sannan yace "kina ganin idan na kawowa dady maganar aurenmu zai yadda?" Da mamaki nake kallonsa nace "no Saif dady bashi da lafiya bazan taba iya tafiya na barshi ba karma ka kawo wannan maganar" tasowa yayi daga kan gadon Halifa da da yake zaune ya dawo gabana kasan kujerar da nake ya zauna tare da kafa min ido, da fari nima na kafa masa nawa jin bazan iyaba na dauke kaina sannan zaman da yayi a gabana wata kunyarsa nakeji, murmushi ya kumayi yace "dama nasan son da kikemin ko Rabin Wanda nake miki baikaiba tunda gashinan kin kasa kallona sannan kina gayamin ba zaki aureniba" da sauri nace "yaushe nace bazan aurekaba?" Yace "yanzun nan" girgiza kai nayi nace "ni ba cewa nayi bazan aurekaba kawai ba yanzuba" langwabar da kai yayi yace "to sai yaushe?" Na amsa da "sanda Allah yayi sanda dadyna ya warke" da sauri yace " sai dady ya warke?" Na daga kai " to kuma idan na mutu kafin lokacin fa?" Nan da nan na hade rai nace "zaka fara zancen mutuwar taka ko?" Murmushi yayi yace "to Fatima banda abinki danayi zancen mutuwa da banyiba duk daya sai na mutu idan lokacina yayi" nace " to ai lokacin naka baiyiba banason kana zancenta ji nake kamar mutuwar zakayi" ya daga hannunsa in defence yana cewa "na daina matata" da sauri na rufe fuskata ina dariya shima dariyar yake.
Washe gari da safe na fito zan tafi zahra muka hadu a bakin kofa yazo mana sallama dan haka na jirashi a waje ya shiga yayiwa su momy sallama sannan ya fito muka tafi tare, feena muka fara kaiwa makaranta ya fita wai zasuyi sallama tun ina jiransa na koma danna masa hon amma sai dai ya dago ya dagamin hannu ya koma bansan abinda suke cewaba, sai da yaga dai za'a rufe makarantar tasu sannan ya hakura ya kyaleta ta tafi tana tafiya yana daga mata hannu har ta shiga gate sannan ya shigo motar, a gajiye nace "wai wacce irin sallamace wannan kukeyi haka sai kace ba zaku sake haduwaba?" Yana wani murmushin gefen baki yace "kika sani ko bazamu sake haduwarba?" Kallonsa kawai nake dana gaji dan kaina na dauke kai na kyaleshi. Babu Wanda ya kuma magana har mukaje zahra, muna zuwa na bude kofar da niyyar fita amma sai ji nayi ya harde yatsun hannunsa a cikin nawa yatsun abinda bai tabayiba, da sauri na waigo ina kallonsa shima ni yake kallo he look serious nan da nan jikina yayi sanyi kawai na tsaya ina kallonsa na rasa abinda zance ma. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Fatima" na amsa "Naam" ya kuma cewa "Fatima" nace "naam" a karo na uku ya kuma cewa "Fatima" na kuma Fara tsorata da kyar nace "naam Yayana menene" kwantar da kai yayi jikin makarin kujerarsa yace "Fatima plss ki yadda idan na dawo na turo iyayena na gaji da tafiya na barki plss kinji" kallonsa nakeyi a hankali nace " Yayana ka kasa ganewane nasan kana aurata kd zaka tafi dani ni kuma bazan iya tafiya gari ya gari har kd nabar dady a halin da yake cikiba, ka bari ba yanzuba sai ya warke tukunna kaji" yace "for how long fatima? Paralyzed ba kamar kowanne ciwo bane da zai warke a dare dayaba, yakan dau shekaru kafin mutum ya warke ya koma normal rayuwarsa, bazan iyaba Fatima" hankalina ya fara tashi dan banason Saif ya nemi abu a wajena na kasa yi masa sannan bazan iya tafiya nabar dady ba, cikin rashin mafita nace "Saif bawai cewa nayi sai ya warke sarai ba amma at least ya fara tafiya da kansa, ya fara yin abubuwa da Kansa" girgiza kai yayi yace "Fatima rayuwar fa ba a hannunmu takeba idan wani abu ya sameni ko ya sameki fa? Karki manta ni sojane a koyaushe komai zai iya faruwa dani zamanki a kano bazai bawa dady lafiyaba tafiyarki Kaduna bazai hanashi warkewaba" zuwa yanzu jikina har karkarwa yake banason wannan yanayin banason wannan hirar ya kamata ta kare haka dan haka nayi dan murmushin yake nace "shikenan Yayana ka kwantar da hankalinka zanyi shawara zamuyi magana kafin lokacin kaji?" Badan yasoba yace "shikenan Allah ya kaimu dan Allah amma karki jirgani plss" nace "in sha Allah" sannan mukayi sallama na bude kofar motar na tsaya ina kallonsa shima kallona yake nace "hannuna" sai kuma yayi saurin cikamin hannun yana dariya wai " wallahi na ma manta sorry" nima ina dariyar na juya na fita ina daga masa hannu har ya fice daga harabar store din sannan na juya zan shiga ciki mukayi ido biyu da kamal, dariya ya kama yimin wata kunya naji ta kamani na rufe fuskata zan wuce yayi saurin shan gabana yana cewa "kawai to ki bishi mana irin wannan byebye kamar hannun zai tsinke" ban kulashiba na zagayeshi kawai ina dariya na shige ciki.
Tunda Saif ya tafi kullum mukayi waya sai ya tambayeni na gayawa momyn sai nace masa kunya nakeji na kasa gaya Mata, wata ranama har fadamukayi yace dama ba sonsa nakeba shiyasa dan haka bazai kuma kiranaba. Ai kuwa ranar bai kiraniba haka washe gari ni kuma nayi ta kiransa yaki dauka, ina zaune a tsakar gida na zabga uban tagumi Halifa ya shigo yayi sallama banjiba sai da ya tabani da sauri na dago ina kallonsa yace "Fadima lafiyarki kalau kuwa? Tunanin me kike haka" kawai maimakon na bashi amsa sai hawaye shar shar, da sauri ya tsugunna a gabana yana tambayar abinda akayimin cikin shehsshekar kuka nace "Halifa Saif ne, fushi yake dani yaki kirana ni kuma idan na kirashi baya dauka" zama yayi sosai a kasa yace "me kikayi masa?" Nan na fara zare ido ya marar gaskiya ina kallon dakin su momy shi kuma ya tsareni da ido, ganin irin kallon da yakemin sai na mike da sauri na kama hannunsa muka koma dakinsa yadda na tabbatar su momy bazasujiniba sannan na bashi labarin duk abinda ya faru, kallona kawai yake har na gama sannan yace "to ke meyasa bazakiyi masa abinda yakesoba? Ko bakya sonsa?" Da sauri nace " inasonsa mana Halifa kaima kasan ina sonsa" yace "then mezai hana kiyi masa abinda yakeso" baki na zumburo gaba nace "Halifa bazan iya tafiya kd nabar dady a halin da yakeba, bazan iya tafiya na barku a wannan halinba" murmushi yayi sannan yace "amma kinsan zamanki bazai bawa dady lafiyaba kuma tafiyarki bazaisa yaki warkewaba ko?" Nace "na sani Halifa amma ina ganin kamar idan na tafi banyi masa adalciba kamar ban damu da halin da yake cikiba kenan" hannuna ya kamo ya juyo dani muna fukantar juna sosai sannan yace "babu Wanda zaice baki damu da dadyba kowa yasan irin son da kikewa dady kowa kuma yasan halin da kika shiga sanadin abinda ya sami dady so ki kwantar da hankalinki na tabbatar dady mai farin ciki da farin cikinkine kin gane?" Kai kawai na gyada masa ya cigaba " yanzu abinda nakeso shine kiyi istahara duk abinda yake alkhairi Allah zai zabar miki ki bashi hakuri kice ya baki kwana bakwai na istaharar shima kuma yayi kin iya ai ko" nan ma kai da daga masa sannan nace "to ai yaki daukan wayar tawa" yana dariya yace zan kirawoshi na bashi hakuri zai dauka kinji" na amsa da "to" sannan muka taso muka dawo cikin gida yaci abinci ya koma kasuwa dama abinda ya dawo dashi kenan.
Bayan Halifa ya dawo da daddare yace yayi ta kiransa shima bai daukaba amma na kwantar da hankalina yasan Saif bazai yi fishi daniba zai kirani, dan haka yauma haka na kwanta ina faman juyi na kasa bacci tunaninsa kawai nake har wani zazzabine ke neman kamani, ina cikin tunani wayata ta fara vibrating da sauri na mike ina zaton Saif ne amma sai naga wata number nan raina ya kuma baci na jefar da wayar kawai na koma na kwanta, mai kiran bai gajiba har sai da ni na gaji na dauka da niyyar na zageshi amma sai me? Muryar Saif naji a wani waje mai hayaniya. Ina dauka yace "thank God Fatima me yasa baki daukaba tun dazu?" Wani kukane yazomin nace "ai bansan number dinba shiyasa" da sauri yace "me ya faru naji kamar kina kuka?" Ai kuwa na karasa sakin kukan ina cewa "bakaine ina ta kirankaba kayi fushi kaki dauka" yace "ayya I'm sorry love wallahi ba fushi nayiba na manta wayarne a gida dama ina ta tunaninki" ina tsaida kukan nace "kai kana ina? Karar me nakeji?" Kamar sauri yakeyi yace "wallahi wani emergency ne ya taso zamu tafi karar jirgine zamuje rescuing wasu yara da aka sace a chibok Maiduguri so kwana biyu bazaki jiniba yanzuma dakyar aka barni nayi wannan wayar kiyi min addua kinji kanwata" wani irin tsorone ya shigeni na tashi zaune ina cewa "yanzu Maiduguri zaku tafi? Yaushe zaku dawo?" Wani na yi masa magana ta background yace "kanwata ana jirana Zan tafi kicewa su dady su tayani da addu'a kinji kema kiyimin na dawo lafiya" kuka na fara kawai na kasa magana ya cigaba da cewa "kanwata ba abinda zaki fadamin naji dadi? Wallahi banason tafiyarnan ban tabajin tsoron zuwa ko inaba sai wannan karon saboda banason yin asararki" da sauri cikin muryar kuka nace "bazakayi asarataba Saif har abada ina nan ina jiranka kaje ka dawo na kuma yi maka alkawarin kana dawowa zaka tarar da maganar bikinmu zanyiwa momy maganar kaji, ina sonka yayana ina sonka sosai" dariya yake yace "there is first time for everything yau Fatima tace tana sona" nima dariyar nake naji an kara yi masa magana da alama wannan karon tsawa aka daka masa nadai ji yace "sorry sir" sannan ya kashe wayar ba tare da munyi sallamaba.

FadimatuWhere stories live. Discover now