Chapter 24

79 6 0
                                    

Muna daga dakin mama munayiwa Halifa dariya daya Fara tsaiwa muka jiyo hayaniya a harabar gidan, da sauri gaba daya mukayo waje ranar kuwa Anty Hauwa tazo yayar Kabir, muna fitowa mukaga Abba yana hankado Kabir daga dakinsa shi kuma yana kuka tamkar karamin yaro yana cewa "Abba ka tsaya nayi maka bayani wallahi banyi komaiba Abba kasan babu yadda za'a yi nayi yunkurin kasheka, dan Allah Abba ka saurareni" a zuciye ya kuma hankadoshi ya gangaro daga kan barandar wajen yana cewa " na gaji da saurararka abin naka ya isheni haka Yau ko asiri kayimin wallahi ya karye da yansanda zan hadaka wai ni zakayi yunkurin kashewa Kabir duk son danake maka, ni din dai danake kamata da laifuka ina binnewa to wallahi ka sani nine rufin asirinka kuma yau ka toneshi " kallon Ibrahim yayi da shima ya fito yanzu daga kewayensa yace " kirawomin yan sanda " da sauri yaya Ibrahim ya matso kusa da Abba yana " Abba dan girman Allah koma menene yayi maka ka tsaya ayi magana kabirne fa Abba plss karka saka yan sanda a ciki" hankadeshi Abban yayi yana cewa "ohh ashefa dan uwankane ko? Kai sagir kai kirawomin yan sandan" wani murmushi da sagir keyi sai da yaga duk an juyo ana kallonsa sannan yayi saurin gyara fuska yace " Abba ka tsaya ayi maganar kamar yadda Ibrahim yace" zuciya Abba ya kuma yi da sauri yayi daki yabar mu a tsaye a wajen Kabir na tsugunne yana wani irin kuka a wajen Wanda yasa gaba dayanmu muma kukan muke, can sai ga Abba nan da waya a kunne da alama yan sandan yake Kira da kansa ai kuwa mama ta tafi da sauri tana kuka tana rokonsa karya kirawo yansandan dan Allah ya kashe, baiji rokontaba amma Allah yaji dan wayar bata shigaba dan haka ya kuma kallon Kabir a zuciye "kayi sa'a wayar bata shigaba amma ka sani yanzu zan fita kafin na dawo ka tabbatar ka kwashe duk abinda kasan nakane ka fice daga gidannan kai daga garinnan ma gaba daya dan wallahi na kuma ganinka a gabana sai ka kare rayuwarka a prison kaji na gaya maka" yana gama fadin haka ya juya zai koma ciki da sauri yaya Ibrahim yace "wai Abba me yayi maka ne wannan hukuncin yayi tsauri" da sauri ya juyo yana kallonsa yace " yayi tsauri kace? To kasheni yayi niyyar yi guba ya zubamin a ruwan tea" gaba daya mun tsorata wani kukan muka kuma saki shi kansa yaya Ibrahim ya tsorata, jiki a sanyaye yace "Abba ka tsaya a duba maganarnan zata iya yiyuwa waninne ya zuba amma ba kabirba " Abba yace " "wai Ibrahim zanyiwa Kabir karyane? Ga wadda ta ganshinan sannan... " da sauri yayi cikin daki sai gashi da mataccen Karen gidan yana zuwa ya jefar dashi a wajen yace "gashinan lion ya sha tea din kalli abinda ya faru dashi da yanzu nine a wannan yanayin, dan haka na sallamawa duniyashi kuma soyayyata dana nuna masa Allah ya Isa, ke kuma' ya nunani' karki sake ki saka kafa ki fita a gidannan kar kuma jikana yabar gidannan kubarshi ya tafi shi kadai dan ba so kike kema ya kasheki ba wataran" yana gama fadin haka ya koma daki ya dauko key din motarsa ya fice daga gidan a zuciye.
Yaya Ibrahim ne ya kamo kabir  daga kasan da yake muka dunguma zuwa cikin dakin mama, zama yayi a kasa kawai yana wani irin kuka muma duk kukan muke hatta da Halifa da Tj dake yan yara. Bayan mun dan lafa da kukanne yaya Ibrahim ya tambayi Kabir abinda ya faru shine ya gaya mana duk yadda sukayi ya cigaba da cewa "kuma wallahi ni na zubane ganin yadda mutumin ke ta maimaita yanzunnan dan haka sai na saka da niyyar idan Abban ya fito zan tambayeshi idan yasan da maganar shikenan idan bai saniba sai a kira Dr aji me yake faruwa idan shima bai saniba sai a zubar da tea din kamar asarar tea din sai tafi sauki akan asarar magani mai amfani ban saniba ashe hakan asarar uba zai janyomin gaba daya" mama tace " to ya akayi lion yasha?" Ya bata amsa da "Na karyatane akan ni ba guba na zuba masaba shine umma tace idan karya tayi a bawa lion indai wani abu ya sameshi ta yadda karya take min shinefa Abba ya kirawoshi ya bashi, karen yanasha ya fadi yana shure shure" haka muka zauna kowa hankali a tashe babu sanin abinyi nan gaba, da alama Wanda ya shirya tuggunnan a tsanake yayi shirinsa.
Haka muka cigaba da zama a wajen har tsahon wani lokaci can muka jiyo motar Abba ya dawo kafin mu ankara Kabir yayi waje da gudu muma muka bishi yana zuwa suka hadu da abba akan baranda nan ya kama kafarsa yana kuka yana bashi hakuri akan yayi hakuri yayi masa bayani amma maimakon ya tsaya din sai ya saka kafa ya hankade shi yayi cikin daki haka Kabir yayi zaman rakuma a bakin kofar dakin yana kuka yana bawa Abba hakuri, zuwa can kawai sai jin jiniyar yansanda mukayi abakin kofa nan suka shigo Abba ma ya fito yana fadin "yauwa gashinan ku kamamin shi kasheni yayi niyyaryi" ganin abun na kuma tsamari mama ta shiga tsakanin yan sandan da Kabir tana kuka tamkar mahaukaciya tana fadin " wallahi Alh sai dai a hada hardani amma ba zasu tafimin da yaroba yace ka tsaya yayi maka bayani kaki sannan kawai kasa a kamashi wallahi sai dai su tafi dani" nan muma gaba daya muka shiga muna muma sai dai a tafi damu, ganin gaba daya mun hade masa kai sai yacewa yan sandan suyi hakuri su tafi kawai ya janye karar.
Haka muna kallo Kabir ya fice a wannan halin kuma Abba ya hanani binsa ya hana kowa binsa, a ranar ba kaina nake tausayawaba ba kuma Halifa nake tausayawaba illah mama da Abba dan sune abin tausayi yadda suka dora son duniya a kansa kamar basu da wasu 'ya'yan, kwananmu biyu a gida Abba ya hana fita yayinda yaya Ibrahim yake dubo manashi danshi kadai ke fita, ranar Monday da safe Kabir ya dawo a tunaninsa Abba ya huce zai saurareshi amma mai makon hakan sai abin ya kima yin worse inda Abba ya sakar masa wasu karnuka da bamusan daga inda ya samosuba, ba karamin ciwo karnukan suka jiwa kabirba kafin aka samu Abba ya janyesu yace kuma wallahi idan kuma ganinsa idan ya sakar masasu sai dai a dau gawarsa.
Wannan Abu ya kuma zuciya Kabir dan haka ya Kira mama a waya yace ita ta yafe masa amma zai tafi ba kuma za'a sake ganinsaba, a lokacin dakyar ta shawo kansa ya tsaya aka samu aka saida masa duk wata kadara tasa aka hada masa kudin abba na fita kasuwa muka shiga gidanmu da a lokacin shima an siyar dashi na hada mana kayanmu Na'im na makaranta dan haka na hada nasa kayan aka kai masa cikin gida mu kuma muka gudu dagani sai kabir sai Halifa, dadynku ko sallama bai samuyi da mamansa ko abbansaba haka muka baro kasar yana kuka kamar ransa zai fita,  ni dama goggo kawai nakeda ita kuma nayi mata sallama na bata hakuri akan mijina dazanbi na barta itama ta yadda nabishi saboda yanzu bashi da kowa bayan ni da Halifa, haka muka taho ba tare da sanin inda muka nufaba da mubaje tashama mota kawai muka shiga ba tare da sanin inda motar zatajeba. Katsina muka fara sauka da muka shigo Nigeria bakin cikin abinda ya faru yasa kullum kabir cikin ciwo yake tun yana dan shan magunguna har abin yakaishi ga aman jini muna zuwa asibiti suka gwada zuciyarsa nan sukace ta kumbura kuma idan bai daina saka damuwa a ransaba komai zai iya faruwa. Ranar wuni nayi ina kuka ina rokonsa da ya dauki kaddara ya cigaba da addu'a Allah zai bayyana gaskiya yanzu idan wani abu ya sameshi ni da Halifa ya zamuyi babu kowa a kasar da bamu da kowa? Nasha wahala kafin na samu ya ware dan akwai lokacinda mukayi wata guda a asibiti da oxygen mask a fuskarsa ko numfashi bayayi, bayan tashinsane yace ya hakura da rayuwarsa ta baya ya hakura da kowa zaiyi rayuwarsa shi da sabon iyalinsa kawai bazai kuma komawa bayaba bazai sake neman suba ya manta dasu. Dadynku ya yanke shawarar Fara kasuwanci ne da kudinsa tunda sunada yawa mama ma ta kara mana haka yaya Ibrahim, dalilin da yasa muka dawo kano kenan tunda itace cibiyar kasuwanci a Nigeria.
Tun daga lokacin bamu kuma komawa kasarmuba bamu kuma samun labari akan yan uwanmuba har yau, amma yau kaddara nason tuna mana da baya bayan shekaru goma sha bakwai Na'im ya samo inda muke, bansan yadda akayi ya ganomuba bansan menene hadinsa da fadimaba kawai dai na ganshi tare da ita kuma banason dadynku ya ganshi dan zai tuna masa da waccan rayuwar bayan ya manta da ita"
Fadimatu
Bansan nayi kuka mai yawaba sai da na bude baki zan basu labarin haduwata da Na'im, muryata har dashewa tayi, nan na basu labarin yadda akayi muka hadu na kara da cewa "bansan yadda akai ya san gidannanba Nima kawai ganinsa nayi sannan yace shima ba ason ransa yazoba Tj ne ya takura masa sai yazo. Sannan momy naji yana cewa gaskiya ta bayyana idan hakane momy me yasa bazamu bibiyi abinba ko gaskiyar ta bayyana?" Wani kallo momy tayimin sannan tace "wato Fadima bazaki taba girmaba ko? Bazaki taba canja haliba ko? Ban Isa na fadi abu nace ayi kiyiba sai kin nuna kamar kin fini sanin ya kamata ko?" Da sauri nake hirgiza kai ina " no momy ba haka bane Allah ya baki hakuri munyi alkawarin bazamu bari a kuma breaking zuciyar mahaifinmu ba koma me kike so shi za'ayi momy".

FadimatuWhere stories live. Discover now