Chapter 29

58 6 0
                                    

Bayan uncle ibrahim ya gama bada wannan labarin sai Na'im yace "na yanke hukuncin yiwa Abba wayane saboda na fahimci uncle bazai koma gidanba kozai koma ba yanzu ba, shiyasa naga tunda shi bazai koma gidaba to mezai hana na dauko gidan na Kawo masa? Shiyasa kawai nayi muku waya nace ku taho" ranar ma haka muka wuni hira sai da dare yayi akace wasu subi Na'im masaukinsa wasu kuma su kwana anan, anan din dai su Rumaisa kawai aka bari sai Abba da yace shifa babu inda zashi umma ma tace ba inda zata dan haka akabar umma, Abba da goggo Halifa kuma yabi Na'im da Tj da uncle Ibrahim.
Da daddare bayan mun kwanta har bacci ya fara daukata kamar a mafarki wayata ta fara vibrating ai kuwa da sauri na daga ina addu'a Allah yasa Saif ne, aikuwa Allah ya karbi addu'artawa ina dagawa naji muryarsa ya kirani da sunan da shi kadai yake fada "Fatima" wani kukane ya tahomin ai kuwa na fara banmayi kokarin rikeshiba nan da nan kuwa su Rumaisa suka mike a tsorace suna kallona, "Yayana ya kake? Kana lafiya ko ba abinda ya sameka? Kun sami yaran? Kun dawone? Yaushe zaka dawo?" Dariya ya farayi yace "kai Fatima ki bari na amsa question daya mana kafin kiyimin daya wannan jere haka, sannan ki daina wannan kukan ni inanan ina kokarin yadda zan samu na kiraki ke kuma idan na kira sai kiyimin kuka?" Da sauri na fara share hawayen idona ina cewa "na daina bazan kuma kukaba yanzu ya kake ba abinda ya sameka ko?" Ina iya jiwo murmushi a cikin muryatsa yace "ina lafiya kalau Fatima babu abinda ya sameni amma bamu dawoba mun dai dawo camp dinmu sai gobe zamu koma" cikin farin ciki nace "Allah ya kuma karemin kai Yayana" yace "amin ai kinayimin addu'a ko ?" Nace "eh inayi maka kullum haka su momy ma" yace "that's my love, yanzu meye labari" da zumudi nace " Yayana na hadu da yan uwana naga kakannina da uncle dina Saif Yau Zan kwana gado daya da cousins dina ka tayani da murna" wani hawayene mai sanyi na farin ciki ya zubomin nasa hannu ina gogeshi daga can Saif yace "alhmdulillah Fatima ya akai haka ta faru bani labari" nan fa na Fara aikin nawa wato surutu har sai da su Rufaida suka gaji suka yi kwanciyarsu sukayi bacci muna surutu, sai wajen 2am sannan yace "yanzu Fatima ki kwanta haka kiyi bacci kinji kicewa dady da momy ina tayasu murna da Halifa ma kinji?" Nace "to zan gaya musu zasuji" ajiyar zuciya yayi yace "Fatima bazaki kuma jinaba sai nan da wani lokaci ki cigaba dayimin addu'a kamar yadda kika saba kinji?" Kai na daga kamar yana ganina nace "in sha Allah Yayana kaima kayimin alkawarin bazaka bari wani abu ya samekaba ko mai zai faru bazakayi giving up ba kayimin alkawarin zaka dawo kaji?" Yace "in sha Allah Fatima nayi miki alkawarin bazan taba yin wani Abu da zai cutar daniba zanyi iya kacin kokarina na dawo gareki kema kiyimin alkawarin zaki jirani komai daren dadewa ni kuma zan dawo" ina kuka haka ya kashe wayarsa ya barni da hadiyar zuciya.
Har bacci ya daukeni ina kuka amma ga mamakina ina farkawa da safe sai naji wani irin farin ciki marar misaltuwa ina zuwa gaisheda su momy na matsa kusa da ita ina faman murmushi, kallona tayi tace "fadimatu yaya dai wannan farin cikin fa" ina dariya nace "momy Saif ya kirani jiya da daddare" nan da nan itama ta fara murmushi tana cewa "ahh lallai alhmdulillah dole kiyi farin ciki sun dawone?" Girgiza kai nayi jikina nayin sanyi nace "aa momy basu dawoba kawai break suka dawo camp dinsu shine ya kirani, yau da safennan kuma zasu koma dajin" nan da nan idona ya ciko da kwalla nace "momy inajin tsoro kar wani abu ya sameshi" hannuna ta riko tana cewa "ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abinda zai sameshi zai dawo da kafafunsa lafiya kalau kinji?" Kai kawai na daga ina goge hawayen fuskata, su mama suka tambayi momy wanene Saif tana musu bayani na taso na fito.
Na fito tsakar gida ina goge hawaye zan shiga kitchen wajen su Rumaisa sai gasu Halifa nan sun shigo, wani kallo Na'im yayimin yace "ke kuma me akayi miki?" Kafin na bashi amsa Rufaida dake bakin rariya tana wanke doya da za'a soya tace "na soyayyane" da sauri ya kalleta "na soyayya kuma" kamar wadda dama take jira nan ta Fara zuba "eh mana jiya har mun kwanta saurayinta ya kirata innajinsu ana alkawarurruka ana kuka shine kuma wancan kukan bai ishetaba shine take wani yanzu" kallona yake sai dana gama share hawayen tas sannan yace "ke yanzu har kinyi girman yin soyayya ko? Har zaki iya Kuka akan namiji ko? Gaba dayama shekararki nawa? Banajin ma kinyi candy ko?" Wani kallo nayi masa na wuce kitchen ba tare dana bashi amsaba a zuciyata ina cewa wato wannan ya fahimci shi dan uwanane zai nemi ya fara takuramin ko ina ruwansa da soyayyata?.

FadimatuWhere stories live. Discover now