chapter 46

66 7 0
                                    

Saif
Satina uku a asibiti kafin aka sallamoni na dawo gida su kuma wajen aikina suka bani hutu, tun ina asibiti kullum zancena shine fatima, babu yadda banyiba akan Abdul ya nemomin ita amma kullum sai yace zatazo amma shiru, har fushi nayi na dainayi masa magana saboda yaki hadani da fatima koda a wayane, idan kuma na dauki wayarsa na kirata bana samunta wannan yasa dole na hakura da nemanta da niyyar ina fitowa daga asibiti nemantane abu na farko da zan farayi, sai dai ina dawowar na shirya na faki idon 'yan gidanmu na tafi gidan amma wai sai na tarar sun tashi wasune daban a ciki, na tambayesu ko sunsan inda wadanda ke gidan suka koma? Sukacemin basu saniba kamar ma kasar suka bari. hankalina ya tashi sosai haka na koma gida na tarar hankalinsu mama ya tashi annemeni an rasa ga mutane sunzo dubani. Nayi hakuri na wani lokaci, zuwa sati guda da dawowata a lokacinne na tare Abdul a daki nace sai ya gayamin inda fatima take idan ba hakaba bazan bari ya fitaba, ganin bashi da yadda zaiyi dani shine yake gayamin ai family dinta sun daukesu gaba daya sun koma Niger kuma baisan garin da suka koma a Niger dinba bashi da ko phone number dinta. Nayi bakin ciki sosai da wannan labarin dan haka na dauki damarar in sha Allah abu na farko da zan farayi a rayuwata shine zan ajiye aikina duk da ba karamar wahala ne da hakanba, zan fara kasuwanci wanda zai hadani da Niger yadda zan sami damar shigowa cikin kasar nayi bincike har sai na ganosu"
" watana biyu kenan da dawowa gida har na fara hada takaddun da zan ajiye aikina, kawai jiya da yamma nayo swapping din Sim dina na siyo waya dan haka na dauki wayar Abdul da niyyar tura pics din da yake dasu da wasu apps ina shiga gallary kawai naga iv din bikin Fatima" shiru na sakeyi dan ba karamin ciwo kirjina keyiba idan na tuna wai fatimatace za'ayiwa aure. Dan mirgina kai nayi sannan na cigaba "nayi ta yiwa Abdul masifa akan me yasa ya San inda fatima take amma yaki fadamin? Shi kuma ya bani excuse da ansha wahala da ita kafin a samu tayi moving on a rayuwarta wai bayaso na kuma hargitsata, abinda bai saniba shine ina bukatar ganinta koda kuwa ta zama matar wani, ina bukatar na gaya mata na cika alkawarina, inason ganinta ko sau dayane kafin na koma ga mahaliccina, abinda bai saniba shine ba lallai sai na auri fatima zan cika soyayyata garetaba a'a as long as she is happy I'm happy koda kuwa da waninane. A ranar ba hankalin Wanda ban tayarba a gidan akan dole ne yau mu taho garinnan, ada sunyi niyyar zuwa bikin amma dawowata ta hanasu saboda basaso nazo, dole badan sunsoba yau muka sami jirgi muka taho. Muna sauka a airport nayi installing WhatsApp dina sannan nayi restoring text dina a lokacin naga dubunnan texts din Fatima Wanda ya kuma tabbatarmin Fatima bata manta daniba. Muna shigowa gidannan na hangota kan step tare da Na'im a matsayin mata da miji, hakan ya taba zuciyata sosai amma babu yadda zanyi haka kaddarata take, ina kallonsune naji an Kama hannuna da wani dan karamin hannu ina juyowa naga feena bakinta har kunne tace "saifeena?" Durkusawa nayi a gabanta ina kwallar farin ciki, ban taba tunanin wani zai kuma kirana da wannan sunanba saboda banyi tsammanin dawowa inda wadda ke kirana da hakan takeba, da sauri ta cikani tayi cikin mutane da gudu Ashe fatima zataje ta gayawa na dawo, na dago ina nemantane na hangota kusa da fatima wadda itama muka hada ido da ita" shiru nayi sannan na dago kai na kalli fatima ina murmushi duk da zafin da zuciyata keyi nace "bani da bakin dazan godewa Allah enough saboda ban taba tsammanin zaisa na kuma ganintaba ban taba tsammanin zan kuma ganin duk wadanda ke wajennan ba" na fada ina kallonsu gaba daya ina murmushin farin ciki, zuwa yanzu kowa a wajen farin ciki yakeyi kowa da murmushi a lebensa hatta da Fatima da hawaye a idonta amma kuma tana dariya wanda ganin hakan kadai yasa naji wani sanyi a raina.
Gyaran murya Abba yayi yace "to alhmdulillah muma muna godiya mai yawa ga ubangiji daya dawo mana da kai, dama anata Saif Saif ni ban taba ganin Saif ba amma yanzu na Ganshi ashe kuma jarumine 'ya fada yana murmushi wanda yasa kusan kowa a wajen darawa sannan ya cigaba "dan duk Wanda yayi wannan rayuwa dole a jinjina masa, saifuddeeni kaga rayuwa Allah ya baka ladan juriya ya kuma sakawa bayinsa da aka zalinta mu kuma ya karemu ya kare mana imaninmu ameen" duk muka amsa da ameen sannan ya cigaba yanzu sai kuje Ku huta tunda gobe da wurine daurin auren gashima har anyi sallar isha tun dazu ku samu kuyi bacci tunda kukazo baku hutaba" yunkurawa mukayi da niyyar tashi amma abinda ya fito daga bakin Na'im ya maida kowa ma zauninsa "Abba kafin ku tashi ina da magana" kallonsa Abba yayi yace "ya akai Na'im " shiru yayi na wasu seconds sannan ya hadiye yawun bakinsa dakyar yace "Abba na fasa auren Fadima" da sauri na kalleshi nace " what? Na'im! Are you out of your mind?" Kallona kawai yayi ya maida kallonsa kan Abba ya cigaba "Abba na fasa aurenta" da mamaki kowa ke kallonsa, da kyar Abba yace "Na'im menene dalilinka na wannan maganar?" Juyawa yayi ya kalli Fatima wadda ke kuka sosai yace "Abba yarjejeniya mukai da ita, koda an zauna daurin aurenmu Saif ya dawo ta fasa na kuma yadda, nima ya kamata na cika Mata alkawarinta" Da sauri na kalli Fatima, kuka takeyi sosai wanda hakan ya sosa min rai, bawai kishine na tana kuka akan waninaba bakin cikine na bana bukatar ganin hawayenta ko kadan bana son ganin bacin ranta. Kowa juyawa yayi ya kalli fatima yayinda ni kuma na maida kallona kan Na'im nace " Na'im banzo wajennan dan na bata maka sha'aniba nazone kawai na tabbatar muku ban mutuba kuma na halarci bikin fatima amma the moment naga invitation card dinta na cireta a raina, na hakura da ita" kai ya girgiza shi kuma yace "ni kuma Saif bazan auretaba alhalin kai takeso baniba, ba Zan auretaba bayan jin wannan labarin naka idan na aureta banyi muku adalciba" kafin ya gama sauke numfashi na dauka "Na'im ni dai kayimin adalci aurentane adalcin da zakayimin fatima tafi karfin haka ya zan dinga baka kanaki kai kasan tafi karfin wannan jayayyar da muke" abbane ya taremu da cewa "kunga ya isa haka mu a wajenmu gaba dayanku 'ya'yanmune bazamu tauye kowaba tunda dukkaninku kun yadda kowa zai iya sadaukarwa dan uwansa" ya juya ya kalli fadima ya cigaba "fadimatu" a hankali ta dago idonta daya koma tamkar an zuba mata attaruhu a ciki dan ja tace "naam Abba" gyara zama yayi yace "kinsan da wannan maganar da yayanki Na'im keyi ta kunyi yarjejeniya dashi?" Yawayene yazubo a idonta tace "eh Abba munyi amma ai dane an dade dayin maganar kumama ni har na manta" Abba yace "ba dane ko yanzuba kawai abinda nakesonji shine kunyi ko bakuyiba" a hankali ta gyada kai tace "munyi Abba" yace "to har yanzu kinanan akan bakanki?" Kai da girgiza ta sauke kai kasa tana cigaba da kuka a hankali, shiru Abba yayi na wasu yan seconds sannan yace "fadimatu yanzu inaso ki zaba Wanda kikeso babu wanda zai hanaki ke zaki rayu da dukkan Wanda kika zaba kuma ki tuna zaman aure zamane na har abada dan haka ki nutsu ki zaba Wanda kikeso mu kuma zamu bakishi in sha Allah" kai ta dago ta kalleni sannan ta kalli Na'im ta kuma sunkuyar da kai, zuwa can jin batayi maganaba Abba ya kuma cewa "fadimatu ke muke saurare wa kika zaba?" Muryarta a dishe tana kuma rawa alamar kuka tace "Abba duk ina sonsu na yadda Ku zabamin duk Wanda kukaga ya dace dani ni kuma nayi alkawarin yi masa biyayya da nuna masa soyayya har karshen rayuwata" tana gama fada ta yunkura ta mike, ta juya zata tafi dady yace "Fadima..." Da sauri tace ba tare da ta juyoba "dady please don't make do this ku zabamin da kanku na yadda saboda duk ina sonsu " tana gama fada ta juya ta fice daga parlon.

Fadima
Ina fitowa nayi gidan ammie ko gani banayi sosai saboda kukan da nake, ina shiga dakin na jawo hijabi ba tare da nabi takan wadanda kemin magana a dakinba nayo waje, ina fitowa nayi waje da sauri. Zanao na gudu daga wannan rikicin zanso na bude idona naga duk wannan abin mafarki nake har yanzu inanan a matsayin spoil fadimatu student din jeguk, dama ace zan iya rikida na koma namiji su kuma su koma mata da shikenan hankalina a kwance kawai na auresu duk su biyun. Tafiya nake ina kuka tamkar tababbiya ban kuma san inda zaniba bansan menene dalilin fitowar tawaba abinda kawai na sani shine ina bukatar fresh air away from Saif da Na'im. Bansan tsahon tafiyar da nayiba sai da naji kafata na neman kasa daukata sannan na sami wani dan tudun flawer kan titi na zauna. Nasan zuwa yanzu an rika an yankewa gobena hukunci, ko wa suka zabamin? Duk Wanda na hasko shi aka zabamin sai naji wani kuka ya tahomin domin zanbar dayan kenan. Ina zaune a wajen tun mutane na zuwa su kalleni su wuce har suka daina kafa ta dauke sannan na fara jin tsoro kuma, tasowa nayi na juyo gida Wanda dakyar na kawo saboda na kusa bata sannan na gaji ashe ba kyar karamar tafiya nayiba. Ina zuwa bakin gate din ana budeshi mota zata fita amma kuma sai taci wani uban birki wanda har sai da na tsorata, halifane ya fito yayo wajena da sauri ya daga hannu da niyyar kwadamin mari nayi saurin rufe fuskata sai kuma ya kasa karasa marin ya tsaya kawai yana huci, ina dagowa yace azuciye "daga gidan ubanwa kike?" Mamakine ya kamani nace "halifa me ya faru?" Bai bani amsaba ya ciro waya a jikinsa ya yi kira, bansan wa ya kiraba ana dauka yace "ta dawo" daga haka bai kuma cewa komaiba ya kashe sannan ya fuzgi hannuna muka koma ciki. Tsayawa mukayi a jikin motarsa banda tsaki da ajiyar zuciya babu abinda yake nace "wai Halifa me ya faru?" Juyowa yayi har yanzu a zuciye yake yace "ban saniba, ke bakima san abinda kikayiba ko? Kinsan kuwa karfe nawa yanzu? Kinsan hankalin mutum nawa kika tayar? Kinsan yawan mutanen da suka fita nemanki?" Kafin na bashi amsa wata mota ta shigo gidan itama a guje, ko gama tsayawa batayiba Na'im da saif suka fito daga ciki sukayo kaina, kallonsu kawai na tsayayi ina tunanin ko wa aka zabamin? Suna zuwa kowa ya fara tambayar if I'm OK. Kowa da tambayar da yakemin har bana iya fahimtar abinda suke cewa sai dai wani abu dana fahimta guda daya tare suka fita nemana tare suka dawo kowa hankalinsu a tashe ko wani abu ya sameni, tare sukemin tambayoyin amma sai kuma a hankali Saif ya fara ja da baya sannan ya juya yayi kofar gida da sauri.

Fadimatuحيث تعيش القصص. اكتشف الآن