👩👩👦👦👩👩👦👦 *Fadimatu* 👩👩👦👦👩👩👦👦
Epi. 06
ByUmmu saifeena
A ranar bayan dare yayi sai suka kama kallon dole momy dai ta gaji tace "kunga nidai na tafi bacci nakeji, Fadima karki sake ki kwana kina kallo ki barmin yarinya ita kadai kinji ko?" Fadima tace " in sha Allahu momy sai da safe" "Allah ya kaimu" Halifa ma yayi mata sai da safe. Bayan shigar momy daki suka cigaba da kallonsu dady bai dawoba sai wajen 1am yana shigowa suka mike "welcome dady" da fara'arsa ya amsa musu yana " har yanzu bakuyi bacciba?" Fadima ta kwabe fuska kamar zatayi kuka harda buga kafa a kasa tana " dady kai muke jira munyi missing dinka" zama yayi cikin daya daga kujerun falon yana zaunar da ita a kusa dashi, cikin lallashi yace "ayya sorry sweetheart na zama busy kwana biyu amma in sha Allahu i will make it up to u ok?" Ta daga kai sannan ya mike yana "yauwa yaran kirki yanzu kuje Ku kwanta gobe in sha Allah babu inda zanje sai mu zauna muyi hira kunga yanzu na gaji" a tare suka mike Fadima tace "OK dady good night" shima yace "good night sweety" haka Halifa ma yayi masa good night ya amsa sannan kowa yayi dakinsa. Komawa halifa yayi ya zauna akan kujera jiki ba kwari sannan have "what now?" "Sai mu jira sanda yace mama" Fadima ta bashi amsa bayan ta mikewa " nikam sai da safe brother dama na fara jin bacci" shima ya mike ya nufi part dinsa yana mata sai da safe.
Washe gari da wuri suka tashi sai dai abinda basu saniba tun da dady ya fita masallaci bai dawoba daga can ya wuce dan haka da sukaga sun tashi da wuri sai sukayi tsammanin bai tashi bane sai da sukaga rana tayi suka tambayi momy sannan tace musu ai ya fita tun kafin su tashi, Fadima ji tayi tamkar ta saka kuka amma kawai sai ta dauke Kai tare da hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi wai meye hakane me yake faruwa? Sunce da dady dukiyarsa sukeso? Hell no shi sukeso ba dukiyarsaba meyasa bazai ganeba ya tsaya ya fuskanceso? Tunda suka dawo daga Korea basuji dadin gidanba shi kullum bayanan momy ma batanan idan tananan ma tana daki meye hakane? Wasu zafafan hawayene suka zubo mata da bata shirya musuba tayi saurin saka bayan hannu ta gogesu sannan ta mike tayi waje da Sauri, halifa yana kula da duk abinda yake faruwa da kanwarsa dan haka tana fita ya tashi da sauri ya bita, a garden bayan gidan ya hangota ta tasa yan fararen tattabarun da feena ke kiwo tana kallo, zama yazo yayi a kusa da ita ya dafa kafadarta cikin sigar lallashi sannan yace "calm down sweetie na tabbatar dady yanada dalilinsa bawai kuma yana avoiding dinmu bane no bashi da yadda zaiyine ke kinsan yadda iyayenmu suke sonmu bazasuso bata mana hakanan ba, dan haka mu kyalesu sanda sukaga they are ready su gaya mana abinda yake faruwa zasu gaya mana OK?" Daga masa kai kawaita iyayi sannan ya cigaba "abinda nakeso dake kawai shine mu daina nuna musu mun damu mu cigaba da supporting dinsu a koma meye yake faruwa mu Nuna musu muna tare dasu a kowanne yanayi, ina ganin hakanne kawai zaisa su saki jiki su fada mana koma meye sannan su sami kwarin gwiwar cigaba da fuskantar koma meye zaki iya?" Fadima ta goge hawayen dake zubo mata tana gyada kai makar wata kadangaruwa "in sha Allah brother zanyi yadda kace tunda basuso gaya mana yanzuba zan bari har sai sanda suka shirya sa gaya mana."
Haka rayuwa ta cigaba su Fadima basu kuma nuna wa momy damuwarsuba su kuma basu fada musuba halin da ake ciki kuwa sai abinda ya kawo babu wani sauki.
Ranar wata talata ranar da su Fadima bazasu taba mantawa da itaba dady ya dawo da rana suna zaune a dinning sunacin abinci ya shigo feena ta tafi da gudu ta rungumeshi tana masa oyoyo duk suka gaisheshi sannan ya wuce ciki bayan ya ajiye feena yana gaya Mata sauri yake wata takarda ya manta, ya shiga daki Su kuma suka cigaba da cin abincinsu jimawa kadan ya fito da takardu a hannu ya shigo nan inda suke yana cewa momy " kunyi ways da wannan matar kuwa da kikace?" Kafin ta bashi amsa aka kirashi a waya dan haka ya daga phone dinsa " slm alkm Mal Bashari kana lpy?, yauwa alhmdulillah ka sameshi? What subhanallahi me yayi? Innalillahi was Inna ilaihir rajiun" iya abinda su Fadima sukaji kenan basu san da wa yake maganaba ba kuma susan me aka gaya masaba kawai sai gani sukayi ya rike kirji kafin su taso daga dinning area zuwa living room inda yake kuwa ya kai kasa sumamme. Tashin hankali da ba'a saka masa rana, gaba data gidan sun rude kowa kuka yake yana jijjigashi tare da kiran sunansa sai daga baya halifa ya fahimci asibiti fa ya kamata sukaishi ba kukaba dan haka ya Fara kokarin dagashi zuwa mota, momy ta taimaka masa suka sakashi a motar suka jashi zuwa asibitin da suke amfani dashi.
Bayan kamar wasu awanni biyu Dr Aliyu ya fito daga O.R din asibitin nasa Wanda su Fadima ke zaune dirshan suna jiransa, tun suna kukan har hawayen ya kafe, yana fitowa sukayi kansa da sauri kowanne yana son jin meya faru da babansu, kowa da irin tambayar da yake masa "doc yaya?" "ya jikin dady?" "doc ya farka? Meyake damunsa?" Daga musu hannu doc yayi tare da cewa " kunga Ku tsaya, dadynku ya farfado kuma ya fita daga dukkan risk dan haka ku kwantar da hankalinku," ajiyar zuciya suka sauke gaba daya a tare suna hamdala ga Allah sannan ya cigaba "in sha Allah zamuyi iya bakin kokarinmu komai zai koma normal Kar Ku damu kudai Ku tayamu da addu'a " nan suka kama kada kai kamar kadangaru, har ya juya zai wuce momy tace "amm doc zamu iya ganinsa?" Da murmushin karfin hali a fuskarsa ya juyo yace "aa saboda munyi masa allurar bacci bama so a tasheshi kuyi hakuri zuwa ya farka da kansa , sannan zaki iya biyoni dan akwai maganar da ya kamata muyi" yana gama fadin haka ya juya zuwa office dinsa, sai da momy ta juyo tayi musu murmushin karfin hali sannan tabi bayan doc.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...