Washe gari na tashi cikin farin ciki, ina farkawa nayi wanka na shirya sannan na sauko kasa, ina fitowa daga dakinmu naga wasu mutane a dakin dake opposite namu suna aiki bansan ko suwayeba dan haka nayi kasa na barsu, a falo na tarar da ammie na kallo na durkusa na gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayata ya gajiyarmu nace "ammie alhmdulillah tabi jini, ina su Rumaisa?" Tace " sun shiga wajensu mama tun dazu " nan na mike ina cewa nima Bari na tafi can" ammie tace "bazakici abinciba?" Ina fita nace "naci a can". Ina shiga na tarar dasu momy a falo sunata hira su Rumaisa na gefe tare dasu Halifa suma sunata surutu, bayan na gama gaishe da su momy na koma cikin yan uwana na ma manta banyi break ba sai da cikina yayi kugi sannan suka fara min dariya sannanfa na mike na tafi neman abinci.
Mun saki jiki sosai da yan uwanmu kamar dama can mun saba koda yake dama mun fara sabawa dasu Rumaisa, a ranar muna komawa kewayen su ammie muka tarar an canja mama daki, dakin da naga ana gyarawa da safe shine yanzu namu, dakine babba sosai dan yafi wancan an zuba gadaje guda uku yan madaidata irin na yan mata sai kuma wata kofa wadda kana shiga closet ne Wanda aka zagayeshi da wardrobe murfin ta full length mirror ne dan haka bama bukatar mirror, sai aka saka wani round table a tsakiya inda aka dora mana kayan kwalliya, daga gefe kuma kofar bandakine shima mai kyau, dakin yayi kyau sosai kuma zai ishemu mu ukun a wadace babu takura, nan muka fara murna tare da settling kowa ya zabi gadonsa da wardrobe dinsa muka fara debo kayanmu daga wancan dakin muna zubawa anan, dama ni banyi unpacking kayanaba dan haka direct nan na sakasu.
Haka rayuwarmu ta cigaba cikin farin ciki tare da yan uwanmu, su dady an gyara musu 2 storey daya irin nasu ammie sun koma ciki ashe dama wadannan ukun iri daya na Abbie dady da uncle Sagir ne, duk da dady bayanan amma sai da suka Gina haddashi, da Halifa da sukasan an haifa tun kafin su dadyn su bata dan ragowar ukun da aka gama shima wai na Na'im Halifa da Tj ne incomplete biyun kuma na Bashir da Yusuf ne yaran uncle sagir (dayake su yarane shiyasa ba'a karasa nasuba). Na saki jiki sosai ina rayuwata da yan uwana duk da har yanzu kullum Saif na raina, abu guda daya dake ragemin kewarsa shine maganar da nake masa ta WhatsApp, nasan baya gani tunda shi kansa account din nasa ya nunamin texts Dina basa shiga wayarsa amma still inajin kamar yanajina dan haka kullum sai na tura masa labarin duk abinda ya faru kamar ibada, bani da hotonsa ko daya wannan abin ba karamin ciwo yakeminba akoda yaushe nayi iyakacin yina kuma Abdul ya turomin yaki dole na hakura, a zuciyata kawai nakeda hotunansa wadanda bazasu taba gogewaba as long as ina numfashi a doron kasa. Ba karamin shakuwa mukayi yanzu da Na'im ba duk da most of the time yana wajen aiki ko baya kasar ma gaba daya amma still kullum muna tare a waya, jikin dady kullum sauki sai cigaba da samuwa yake dan yanzu yana iya tafiya da kansa da tallafin sandan asibiti, hakan ba karamin farin ciki ya sakamuba dan ranar har da kukanmu dan murna.
Wata ranar Monday mun tashi da safe yan makaranta na ta shiri zasu wuce, suma su Rumaisa sun fara university wannan shekarar dan haka har dasu za'a tafi, mun tashi tare bayan sun shirya nima nayi wanka muka sauko kasa tare mukaci abinci sannan muka fito na rakosu waje ni kuma zan shiga wajensu momy, a harabar wajen muka hadu dasu Na'im muka gaisheshi sannan suka shiga mota mu kuma mukayi wajensu momy tare, muna shiga muka tarar da momy da dady a falo suna shirin fitowa zasuje gaisheda su Abba dan haka muka juya muka bisu zuwa gidan Abban, a falo muka tarar dasu Abba mama da goggo suna cin abinci (kafin rasuwar umma Abba ya auri goggo sun zauna su uku) muma kan dining din muka karasa, bayan mun gama gaisawa su Abbie ma suka shigo aka gaggaisa sannan abbie ya yunkura zai fita yana cewa Na'im "Kai ba yanzu zaka fitabane?" Kai Na'im din ya sosa da mukullin motar hannunsa yace "eh Zan fita amma inason yin magana da Fadima da Halifa ne akan maganar makarantarsu " da sauri na kalleshi shi kuma yaki kallona balle yaga irin kallon da nake masa, nan fa kowa ya fara cewa "ahh lallai kam kayi tunani ya kamata su koma makaranta" kada kai mama ta farayi tace "dandai idan ma na fada ba yadda zakuyiba kamar yadda kukaki yadda lokacin da za'a sakasu Rufaida a makaranta, amma wadannan yaran aure ya kamata dasu ba wata makarantaba duk Wanda zai cigaba da karatun ya cigaba a dakin mijinsa, nidai tawa shawarar kenan" shiru kowa yayi zuwa can Abba yace "to yanzu banda abinki mama fadimatu gaba daya nawa take? Yarinyace sannan a yanzu bata da wani tsayayye da zakice ya fito a daura musu aure amma idan kika bari ta fara karatun kamar yadda yan uwanta suka fara sai kiga Allah ya kawo mijin" da sauri tace "aa alhaji babu batun bata da tsayayye baga dan uwantananba? Koba soyayya sukeba?" Da sauri a tare ni da Na'im mukace "aa mama ba soyayya mukeba" sai da muka fada kuma kowa ya sunkuyar da kai, Abba ne ya kuma cewa "kinjiba ni a iya Sanina ma fada suke bansan sanda suka fara shirin da har zakiyi tunanin soyayya sukeba" da sauri nace "ni ina ma da wanda nakeso" nan idon kowa ya dawo kaina aikuwa tace "yauwa kajiba ba? wayeshi yar albarka? Ni dama nafison auren da wannan karatun da baya karewa" ba tare da fargabar komaiba ko wata kunya nace "Saif " shiru sukayi gaba daya ba wanda ya kuma magana sai zuwa can goggo tace "Fadima " na dago kai na kalleta tare da amsawa da "naam" tace "Fadima yaushe zaki karbi kaddararki ki yadda Saif ya koma ga mahaliccinsa? Fadima sai kace ba musulmaba? Shima da kike wannan abin dominsa da zai dawo duniyar bazaiji dadiba domin kina raunata imaninki akan abinda kinsan gaskiyarsa, yanzu tsakaninki da Saif addu'ace kawai amma wannan gaddamar da kikeyi babu inda zata kaiki dan Allah ki sakawa zuciyarki hakuri kinji?" Kai nake girgizawa tun da ta fara magana hawaye nabin fuskata tana direwa kuwa na dauka da cewa "wallahi mama Saif bai mutuba ku daina cewa ya mutu ku daina kasheshi alhalin yana raye yayimin alkawarin zai dawo kuma na tabbata zai dawo din" kuka na fara sosai dan nasan Saif na raye amma mutane sunki yadda dani, sunayimin kallon abin tausayi wadda kanta ya tabu ko wadda ta kasa yadda da kaddararta.
A ranar dai tamkar wadda aka famamin ciwon rashin Saif wuni nayi ina kuka har su Rumaisa suka dawo suka kasa gane kaina, rarrashin duniya naki hakura nan da nan kaina kuwa ya fara ciwo, har magriba ina kwance akan gado da kyar nake tashi ma nayi sallah dan haka yanzu ma dana yunkura zanyo alwalar sallar magriba ina tashi jiri ya debeni na zube a wajen, ai kuwa nan da nan hankalin su Rumaisa ya tashi sukayi waje da gudu sai gasu tare da ammie da Na'im, suna shigowa Na'im ya daukeni daga kasan dana fadi zuwa kan Gado ya kwantar dani sannan ya kira family doctor din gidan Allah yasa yana kusa zuwa wasu yan mintuna sai gashi, bayan ya dubani yayi yan rubuce rubucensa sannan ya kalli Na'im yace "dama tanada hawan jinine?" Kai kawai Na'im ya daga masa kana iya karantar tashin hankali da tsoro karara a fuskarsa, Dr ya cigaba da cewa "da alama tana cikin damuwa dan haka jininta ya fara hawa amma ba sosaiba sannan tana tare da yunwa abinda yasa ta jiri kenan dan haka yanzu ga wannan maganin a siyo mata taci abinci sai tashashi sannan a guji bata mata rai ko barinta cikin damuwa in sha Allah bawata matsala, idan ta sha maganin ta samu tayi bacci" yana gama fada ya mike tsaye nan Na'im ya bishi yana masa godiya suna ci gaba da tattaunawa. Kallona ammie tayi tace "yanzu Fadima daga fada miki gaskiya sai ya zama laifi har kina neman salwantar da rayuwarki? Shikenan bazaki karbi gaskiyaba ki cigaba da rayuwarki ko? Haka zaki zauna jiran Wanda baya raye kice dashi zakiyi rayuwa?.." Ban bari ta cigaba ba nayi saurin toshe kunnena ina kuka tare da cewa "ammie yana raye zai dawo nasan yana Raye" a zuciye ta mike tace "sai kiyi gaskiyace sai an fasa miki idan kinso ki bishi lahirar kuje can kuyi rayuwar tare marar jin magana kawai dan kinga ana lallabakine kikewa mutane taurin kai" tana gama fadar haka tayi waje ta barmu su Rufaida na kokarin rarrashina.
YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...