Bonus Chapter

121 6 0
                                        

Eagle square abuja dankare take da mutane wadanda sukazo daga ciki da wajen Nigeria, president Abubakar Sanusi Sayyadi tare da manyan yan majalissa na mazauninsu na musamman gefe ga manya manyan sojoji na kasa, ruwa da sama kowa yaci kwalliya iya kwalliya cikin kakinsu mai tafiya da zuciyar yan mata, daga dama kuma ga wasu manyan da kananan sojojinnan da akeyin taron dansu, sojojin da suka murkushe kungiyar boko haram suka kawo madauwamin zaman lafiya ga alummar Nigeria, daga gaba gaba na hango air vice marshal Saifuddeen Abubakar Wanda yayi tsallalen badake ya koma air chief marshal ba tare da yayi air marshal ba saboda kwazonsa da sadaukarwar da ya nuna a hanyar data bulle zuwa ga murkushe yan ta'addan da suka addabi Nigeria da makotanta.
Jin dadin abinda wadannan sojoji sukayi na sama kasa dana ruwa yasa aka zabi hazikan ciki domin a karramasu tare da basu awards da kuma promotion.
Daga can cikin yan kallo kuma yan uwane da abokan arziki fadimatu an zama hajiya cikakiyar yar jarida da kasa keji da ita mai bede gaskiya komai dacinta da bin kwakwkwafi. Zagaye da ita yarantane su shidda Na'im, huda, hasna, husna, Halifa sai auta Aliyu dan shekaru biyar, kusan kafatanin danginsu sunzo, hatta da yan Niger ba'a barsu a bayaba kwansu da kwarkwatarsu suna wajen domin taya dansu kuma surikinsu murna.
Taro na gudana yadda ya kamata har akazo gabar bayadda awards tare da promotion a lokacinne sojojin suka fara tashi suna zuwa karbar nasu direct daga hannun maigirma president. Saif ya karbo nasa an kumayi musu hotuna sosai da shugaban kasa sannan ya dawo mazauninsa ya zauna sai da aka gama taron gaba daya sannan a karshe aka gabatar da sababbin yayayyon sojoji dan dama hadeshi akai bikin karrama tsofaffi da na yaye sababbi. Aliyune ya fara ihu yana "yaya! Yaya!!" Yana nuna daya daga cikin sojojin wadanda suka kame tamkar ba mutaneba, duk nisan dake tsakaninsu sai da Aliyu ya hangoshi shi kuma sai da ya jiyo ihunsa, idonsa kawai ya juyar sashen da ya jiyo ihun ya kuwa hango dan kaninsa. Nawal saifuddeen kenan sabon sojan kasa mai jini a jika ga kyau da sanin ya kamata san yan uwa da kaunar kasarsa.
Bayan tashi daga wannan babban tarone direct wannan iyali suka wuce wani babban hall a cikin 3star hotel domin walimar murnar abinda ya samesu, anci ansha anyi murna sosai, murjan Halifa ma tazo da yaranta guda uku Fadima (Adda), amir da Aisha. Bayan an cin kwalam da makulashene Saif ya tashi domin yin jawabin godiya "assalamu alaikum yan uwana da abokan arziki, alhmdulillah alhmdulillah alhmdulillah ina mai matukar godiya ga Allah da dunbin rahamarsa da ni'imarsa gareni da iyalina baki daya, salati da aminci su kara tabbata ga annabin rahama annabi Muhammad (SAW) ina godiya sosai da taruwarku anan domin ku tayani murnar abin alkhairin da ya samu iyalina, na gode sosai Allah ya kara mana kaunar juna ya tsaremu daga sharrin mugun iri, na gode matata da taimakonkine nazo inda nake ina alfahari dake ina alfahari daku gaba daya. Na gode" tafi aka dauka gaba daya kafin ya dawo kusa da Fadima ya zauna, wani kallo suka yiwa juna mai cike da farin ciki da kaunar juna.
     ******     ******   ****** ******
AUTHOR'S NOTE
Assalamu alaikum yan uwa maza da mata na gode sosai da lokacinku da komai naku da kukayi hakurin bina a wannan tafiyar har mukazo karshe Allah ya saka muku da alkhairi, alkhairin dake cikin wannan littafi na fadimatu Allah ya hadamu a ladan sharrin dake cikinsa ubangiji ya yafe mana. 
Abin tambayarma anan shine wai takamaimai menene darussan da nakeso isarwa a wannan labarin? Wannan novel na fadimatu yana dauke da manyan darussa guda biyu na farko yadda da kaddara na biyu rikon alkawari. 
Da fari Fadima ta taso a matsayin tantiriyar yar masu kudi dakeyin yadda taso amma da rayuwa ta juya sai da ya zamana abinda zatacinma sai da ya gagareta amma sukayi hakuri suka jure, Ada Fadima yar gatan uwa da ubace wadda sai abinda ta fada akeyi a gidansu amma sai da ya zamana ta dawo yar kanta saboda babu uwar ba uban amma ta jure ta dau kaddara tayi koyi da hadisai da ayoyin kur'ani, ubangiji da kansa yace yana tausayin Wanda ya jarabta da kaddara da karayar arziki kunga kuwa tabbas su Fadima sunga rayuwa kenan. Lesson na biyu a littafin fadimatu shine rikon alkawari: Fadima ta rike alkawarin Saif duk da iyayensama sun yadda ya mutu amma a kullum tana ganin cewar da alkawarinsa a kanta ta kuma jajirce taki ci, haka shima taku daya zaiyi a dauke miserably rayuwar da yayi da yan boko haram amma ya jure saboda yayi Mata alkawarin bazaiyi duk wani abu zai janyo ya rasa rayuwarsaba sai dai idan kaddararsace hakan. Ya kamata mu rinka daukan alkawari da muhimmanci saboda shi kayane inji bahaushe.
Nayi maganganu akan abubuwan da yan kungiyar boko haram keyi, ina fatan masu karatu zaku fahimci wani abu guda daya: novels fiction ne, ban taba ganin dan boko haram ba ban taba ganin garin da suka kwaceba ban kuma taba ganin camp din yan gudun hijiraba sai dai hasashe dan haka duk abinda na rubuta kirkirane bani da tabbas na sunayi ko basayi. Kar Wanda ya karanta labarin fadimatu ya dauka da gaske yan boko haram na raping 'ya'yan mutane publicly, nasan dai suna kisa nasan suna kwace gari amma maganar raping karinane bani da tabbas dan haka ko a lahira na sanar daku karinane.
Idan nayi bincike Wanda na gamsu dashi ina raye kuma cikin koshin lafiya in sha Allah Zan Kawo muku labarin murja nan bada jimawaba.
Nagode sosai da time dinku da soyayyarku Allah ya barmu tare sai kunjini a sabon littafina MUGUWAR UWA under Taskar Intelligent, MARAICINE SILA.

FadimatuDove le storie prendono vita. Scoprilo ora