Wannan abin alkhairi da ya samemu ba karamin faranta ran kowa yayiba, Allah sarki Saif Allah yasa ya kuma kirana na bashi wannan labarin na tabbatar zai yi farin ciki ba kadanba, wannan dalilin yasa aka daga tafiyarmu diffa hardai an gama komai sannan za'a kuma saka rana. Tunda naji an daga tafiyar nake faman addu'ar Allah yasa saif ya dawo kafin lokacin.
Bayan kwana biyu da daga tafiyarmu su dady sunata harkar dawo da kudinsu da yake kudin da yawa yasa process din ma yake mai tsaho, kasancewar dady ba lafiya yasa Halifa da Na'im ne akan harkar su sukeyin komai sai dai suzo su gaya masa yadda akayi ko kuma a kirashi a waya ace ga yadda akeso ayi. Ranar ina zaune a falo ina kallon wani Korean film mirror of the witch sai ga Na'im ya shigo, kamar yadda ya saba neman magana da takurawa rayuwata haka yanzuma yana shigowa kawai ya dau remote ya canza ya koma kallon labarai, kallonsa kawai nayi na dauke kai sai mamanshice tace " wallahi Na'im dai kaji kunya ka rasa wadda zaka rinka ja sai kanwarka" kallona yayi yana wani murmushin mugunta yace "to kawai mutum ya zauna yana kallon abinda ba fahimta yakeba kwarama ta kalli labaran taji halin da kasarta take ciki amma kawai mutum ya zauna yayi ta kallon wasu mutane masu idanuwa a ciki" ina jinsa ko kallonsa banyiba na cigaba da danna wayata ina turawa Saif text ta WhatsApp saboda tunda ya tafi duk abinda ya faru sai na bashi labari ta WhatsApp duk da ba shiga wayar tasa yakeba yanzuma labari nake bashi ina kallo Na'im ya canjamin tasha. Ina danna wayata kunnena ya jiyomin wani tashin hankali wanda ban taba jinsaba banda lokacin da dady da momy suka fadi, mai gabatar da labaraine na NTA news yake wata magana ana kuma nuna abinda yake fada din "ayaune kuma muna shirin kammala hada wannan shiri muka sami labarin jirgin dake dauke da sojojin sama da sukakai taimakon gaggawa cikin rundunar da ta tafi kwato 'yan matan chibok ya fado sanadiyyar harboshi da 'yan kungiyar ta boko haram sukayi daga maboyarsu da wani abin fashewa, jirgindai yana dauke da sojojin Nigeria na sama wato air force guda goma a yanzu dai an sami gawar mutum biyar daga cikinsu jami'ai na cigaba da neman ragowar biyar din ga hotunansu kamar haka..." Nan aka fara nuno hotunansu tare da sunansu da mukamansu, wadanda aka samo gawarsu aka fara nunawa, tun da aka fara wannan rahoton na mike zaune zuciyata kamar zata fashe wani irin jirine yake dibana, cikin tashin hankali nake kallon TV din numfashina na neman daukewa, har aka gama saka hotunan wadanda suka mutu babu na Saif sannan aka fara na wadanda ba'agansuba an saka mutum hudu na biyar din hoton Saif dinane yana murmushi da complete uniform dinsa, wani ihu na saka na mike tsaye tare da dora hannu aka ina salati, nan da nan su momy dasu Rufaida dake tsakar gida sukayo ciki da gudu suna tambayar abinda ya faru, na dai san momy ta rikeni tana tambayata abinda ya faru Na'im na daga bayana shima yana tambayata amma ban kuma sanin abinda ke faruwaba daganan.
Ahankali na fara bude idona dishi-dishi nake gani daga baya kuma idona ya washe a tsakar gida nake a kwance kan katifa kafatanin yan gidan suna zagaye dani sunyi jigum jigum Halifa na rike da hannuna da alama kuka yayi dan idonsa yayi ja ya kuma kumbura. A hankali kaina ya fara booting ina tuna abinda ya faru 'in sha Allah Fatima nayi miki alkawarin bazan taba yin wani Abu da zai cutar daniba zanyi iya kacin kokarina na dawo gareki kema kiyimin alkawarin zaki jirani komai daren dadewa ni kuma zan dawo' abinda ya fara dawowa kaina kenan nan na saki wani irin kuka da ya sanar da yan uwana na farka da sauri gaba daya sukayo kaina sunayimin sannu "makaryaci mayaudari bayan yace zai dawo Halifa yayimin alkawarin zai dawo kuma ya karya alkawarinsa Halifa na shiga uku sun kasheminshi shikenan sun kasheshi wayyo Allah dady banason ya mutu idan ya mutu nima mutuwa zanyi na shiga ukuna " kuka kawai nake ina sambatu da alama suma sunji labarin dan jana kawai Halifa yayi jikinsa ya rungumeni shima yana kuka momy Rumaisa, Rufaida da dadyma kuka suke yayinda sauran yan gidan gaba daya jikinsu yayi sanyi.
Da sauri na dago daga jikin Halifa ina goge hawayen fuskata nace "Halifa ina wayata?" Da muryar kuka yace "me zakiyi da ita" nace "Abdul zan kira watakil ba Saif na ganiba ba shi bane sabodashi yayimin alkawarin bazai bari komai ya sameshiba zai dawo nasan kuma bazai karya alkawarinsaba maybe wanine daban ko?" Halifa kuka yake sosai ya sunkuyar da kai yaki ko kallon idona, ganin bazai min maganaba yasa na mike da sauri har ina neman faduwa da niyyar na nemo wayata, wani hannu naji ya rikeni na juyo a fusace da niyyar kwacewa dan nayi zaton halifane amma ga mamakina Na'im ne kuma bawai rikenin da yayinne ya bani mamakiba illa tashin hankalin dake cikin fuskarsa, a hankali ya juyo dani muna fuskantar juna yace "Fatima Halifa ya Kira Abdul ya kuma tabbatar masa saifne dan yanzuma suna kadunan karbo gawarsa" nayi niyyar ja masa kunne akan babu mai kirana da Fatima illa Saif dan haka kar ya Kara amma wani tashin hankalin ya danne wanna wai gawarsa to ai bai mutunba tukunna balle ya zama gawa, da sauri na ture hannunsa daya dafa kafadata dashi nace "mallam bai mutuba kar ka wani gayamin gawarsa ai ko a wadanda akace sun mutum babushi ko ce maka akayi ya mutu?" Kai kawai ya kada tare da juyawa ya fice da sauri daga gidan maybe kuka yake shirinyi baya kumaso mu gani.
Haka na rinkabi daki by daki ina Neman wayata su kuma su momy na zaune babu wanda yayi kokarin hanani illah kuka da sukeyi, ayanzu kusan gaba daya matan dake gidan kuka suke. Da kyar na samota sai dai ta fashe sai yanzu na tuna dazu ita nake dannawa na kumayi jifa da ita da naga hoton Saif dina, da sauri na fito waje na fara caje Halifa ina cewa "mallam nace ka bani waya kana wani abu bai mutuba fa inasone na tabbatar muku na san bai mutuba inaji a jikina" da kansa ya dauko wayar ya mikomin na karba da sauri tare da Neman number din Abdul na kirashi, kiran farko bai daukaba sai da na kuma kira sannan ya daga muryarsa kawai naji naji wani sabon tashin hankali ya dokeni tabbas kuka yake Abdul ma kuka yake na shiga uku, yana dauka ya fara magana "Halifa Wanda suka kawodin ashe ba shineba ba Saif bane amma shi har yanzu basu ga tasa gawarba sunce ma mu tafi gida sai gobe idan an ganshi jirginsu na gobe zai taho dashi" da sauri nace "wai wayace maka ya mutune kake maganar idan anga gawarsa? Dama so kake ya mutu ko? Dama ba sonsa kakeba shiyasa kakeso ya mutu ko?" Ba karamin rauni muryarsa ta kumayiba jin muryata yace "Fadima kiyi hakuri amma an samo mutum takwas cikin goma duk sun mutu kuma mutuwa ta tashin hankali ta yaya zakiyi tunanin Saif zai tsira? Shima fa mutumne sannan ba film bane gaskiyace wannan balle kiyi tsammanin zai tsira. Fadima sai dai muyi hakuri muyi masa addu'a Allah ya gafarta masa" a hankali na mikawa Halifa wayarsa nayi daki, ban kuma yiwa kowa maganaba naje na kwanta.
Kaina wani irin ciwo yake zuciyata na zafi wannan mugun mafarki Allah kayi gaggawar tashina dagashi bazan iyaba zuciyata bazata iya daukaba, me yasa yayimin alkawari idan yasan bazai cikaba? meyasa ya shigo cikin rayuwata idan yasan bazai zaunaba? Shikenan ya tafi ya barni ni kadai a duniya. Kukanma yaki zuwa juyi kawai nake tun ina fahimtar abinda ke faruwa har na daina.
A hankali na bude ido kaina na wani mugun sarawa kamar zai fashe, da ido na fara kallon wajen dakin dai kamar na asibiti, yaushe nazo asibiti? Me kuma ya kawoni? Sarawa kaina ya kumayi na dafeshi da sauri wani hawaye mai zafi na fitowa daga idona. Can kuma na tuna da mugun mafarkin da nayi wai Saif ya mutu, wani murmushi nayi silly me na rasa mafarkin da zanyi sai na mutuwar Saif?. Turo kofar dakin akayi aka shigo Rumaisace da Na'im da kwanukan abinci a hannunsu, tana ganin na farka ta taho da sauri tana cewa "sannu Fadima kin tashi?" Kai kawai na daga mata tace "akwai inda yake miki ciwo?" Na'im na kalla da shimaya kuramin ido a zuciyata nace nasan da mafarkina zai zama gaskiya da sai yafi kowa murna saboda tsanarsa da yayi, kan Rumaisa na maida ido sannan nace "kaina ke ciwo kamar zai fashe" na fada idona na cikowa da kwalla, juyawa tayi ta kalli Na'im dake tsaye a bayanta kamar gunki tace "yaya ko zaka kirawo likitan?" Kamar Wanda ya farka daga bacci haka yayi firgigit yace "naam?" Tace "Dr nace" sai kuma ya yi waje da sauri.
Rumaisa na kalla nace "zansha ruwa" da sauri ta daukomin wani a cikin ledojin da sukazo dashi ta kamani na tashi zaune sannan ta mikomin nasha, bayan na gamashane Na'im ya dawo tare da wani Dr ya dan dubani sannan yayimim tambayoyi tare da gwada BP na sannan ya juya ya fice. Bayan fitar Dr Rumaisa ta zubomin abinci da yake yace a bani abinci naci, na karba ina cewa "wai Rumaisa me ya samenine?" Tana rufe flask din data zubamin abincin tace "kawai bayan shigarki daki mun biki muka tarar kina ta juye juye akan gado mukayi miki magana bakyaji sai da yaya Na'im yazo ya fahimci bama a cikin hayyacinki kikeba shine aka kawoki asibiti kwananki biyu kenan sai yau kika farka" da mamaki nake kallonta nace "to meya sameni har kwana biyu? A iya sanina lafiyata kalau" ta gama rufe flask din ta zauna kusa da Na'im akan two sitter din dake dakin tana cewa "jininkine yayi mugun hawa a lokaci daya" nayi loma sannan na kalleta nace "hmm ba dole jinina ya hauba kinsan mafarkin me nayi?" Kai kawai ta girgiza nace "mafarki nayi wai Saif ya mutu" na fada ina dariya sannan na cigaba da cewa "ai Allah ma dai ya kiyaye amma nasan idan har hakan ta kasance to da yanzu nima ina nawa kabarin banajin zan iya rayuwa babushi yanzuma da bama tare ji nake kamar na bishi wallahi" kai kawai Rumaisa ta kifa akan kafarta ta fara kukan da bansan dalilinsaba dan haka kawai na saki baki ina kallonta.
A hankali Na'im ya taso daga mazauninsa inda yake Danna waya yazo gaban gadon da nake yaja kujerar gaban gadon ya zauna muna kallon juna sannan ya fara cewa " Fatima.." Da sauri na katseshi "sunana Fadima Saif kawai ke cewa Fatima so call me Fadima plss" kallona yayi yace "OK naji Fadima shikenan?" Da sauri na daga kai sannan ya cigaba "Fadima nasan ke musulmace mai yadda da kaddara na yadda da hakan saboda yadda kikayi lokacin da abubuwa da yawa suka faru daku babu mai taimako sai Allah amma kukayi tawakkali kuka jure harkuka cinye jarabawar, inaso ki dauko waccan fadimatun ki dawo da ita, yanzuma kiyi tawakkali kiyi hakuri kamar yadda kikayi Ada, Fadima kinsan ubangiji yace kullu nafsin za'ikatul maut' bayannan akwai hadisai da ayoyi da yawa da sukayi magana akan yadda da kaddara Wanda saboda muhimmancinta sai da ya zama idan mutum bai yadda da kaddaba to imaninsa bai cikaba, fadimatu inaso kiyi kokari ki cika imaninki ta hanyar yadda da kaddara kowacce irice mai kyau ko marar kyau" shiru yayi ya sunkuyar da kansa kasa tashin hankali rubuce a fuskarsa, kallonsa kawai nake kirjina na dukan uku uku dan nasan dole akwai wani mummunan labari dazai biyo bayan wanna doguwar nasihar, jin bazai cigababa kuma zuciyata na neman daina aiki nayi kundunbalar cewa "Na'im menene ya faru?" Ahankali ya dago kai yana kallona idonsa yayi ja sosai jijiyoyin kansa gaba daya sun fito waje yace "fadimatu ba mafarki kikayiba Allah yayiwa Saif rasuwa kwanaki biyu kenan da suka wuce amma har yanzu ba'a samo gawarsaba amma an samo gawar mutum takwas cikin goman dake cikin jirgin" karkarwa jikina ya fara nan da nan hawaye mai zafi ya fara zuba a idona, plate din dake hannuna na mika masa ya karba sannan na juya masa baya na kwanata tare da cewa "then shi bai mutuba kenan dan daya mutu shima da sun gano tashi gawar" yace "fadimatu..." Da sauri na daga masa hannu nace "ya isheni haka Na'im Saif bai mutuba I'm sure da ya mutu zanji a jikina dan haka bai mutuba".
Ni kaina nasan cewa ina fadane kawai saboda na bawa kaina hope na cewar maybe yana raye amma na gama saddakarwa Saif ya mutu ya tafi ya barni bai cika alkawarinsaba na dawowa. Shikenan dama ya gayamin mutuwa zaiyi kafin muyi aure ni nayi ta ja masa rai naki nayiwa momy magana gashinan ya mutun ya barni sai na jika kaina nasha. Tura kaina nayi a cikin fillo din da nake kwance tare da sakin wani irin kuka mai shake numfashi, ni kaina bansan dadewar da nayi ina kukanba amma nasan na dade inayi sai dasu momy suka shigo suna faman rarrashina amma naki ganin numfashina na neman daukewa suka kira Dr ya kuma yimin allurar bacci.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...