Nakanyi tunanin irin farin cikin da zanyi a duk ranar da Fadima ta karbi soyayyata, tunanin hakan zai kasance kawai na sakani farin ciki amma abinda yaban mamaki gashi yanzu ta karba bama soyayyata kawaiba ta yadda zata aureni amma ko kadan banji wani farin ciki na azo a ganiba. Har ta mike daga wajen tayi hanyar fita daga garden din ina zaune banyi wata maganaba, sai da ta kusa fita sannan na kirata "Fadima " tsayawa tayi sannan ta juyo ta kalleni, na mike tsaye na karasa kusa da ita nace "Fadima banason na zama da rashin uwa dan zuciyata ba zata iya daukaba gwara na hakura na cigaba da addu'a ranar da kika fara sona ma bayyanawa duniya amma banason aurenki alhalin ke bakya farin ciki dani bakya sona kin aurenine saboda Wanda kikeso bayanan" hawayen idonta ta goge tace "yaya Na'im ba da rashin uwa zanyi dakaiba na kafa wannan sharadinne saboda kamar yadda ka fada inason samawa zuciyata excuse wanda bazata cigaba dayimin kallon mayaudariyaba, idan na amshi soyayyarka haka zanga kamar na karya alkawari amma idan na saka wannan sharadin zan rinka bawa kaina excuse na naso na cika alkawarin Allah ne baiyiba" shiru tayi tana kuma goge hawayen fuskarta zuwa can tacigaba da cewa "inasonka kamar yadda nakeson Saif dan har nakanyi mamaki idan akace so dayane dan nidai nawa biyune dan haka ka saka a ranka ba da rashin uwa zanyi dakaiba ina sonka" dan baya naja sannan na sunkuya yadda zan iya hango fuskarta nace "da gaske kina sona? Kinasona kamar yadda kike son Saif da gaske ko kuwa dai fada kawai kikai?" Ido itama ta dago ta kalleni ganin na kafa mata ido Sai kuma ta Kama dariya ta rufe fuskarta da mayafin kanta ta juya ta karasa ficewa daga wajen. Ba karamin farin ciki najiba dama ina zargin tana sona amma yanzu da naji daga bakinta na tabbata tana sona nayi farin ciki sosai dan a wajen na durkusa nayiwa ubangiji sujjadar godiya dan shi kadai yasan irin son da nakewa Fadima shi kadai yasan yawansa shi kadai da yasakamin shi.
Aranar haka na wuni cikin farin ciki duk yan gidan sai da sukasan ina cikin farin ciki, bayan na dawo daga sallar isha na shiga wajen ammie ina zuwa na tarar dasu zaune a parlor fadimace kawai babu nan na yi wajen dining ina cewa ammie yunwa nakeji me zan samu a gidannan?" Ina bude kular abincin naga tuwon alkama na bude ta miyar ita kuma miyar kubewa danyace wadda taji nama ai kuwa nan naji yawuna ya tsinke inason tuwon alkama miyar kubewa, zama nayi akan kujerar dining din na jawo plate na fara zubawa, daga living room najiwo ammie na cewa Rumaisa" Rumaisa dan Allah kirawomin Fadima yanzunnan zata fara wannan zaman dakin nata na hanata taki hanuwa ba dole lafiya ta kasa samuwa a wajentaba kullum tana daki tana tunani, dama bacci take da da sauki amma koyaushe kaje dakin idonta biyu tana faman tunani" ina jiyosu amma ban tamkaba ina zuba loma har suka sauko ita da Rumaisa. Tunda ta fara saukowa na kafa Mata ido ta canja kaya da alama wanka tayi ta saka wata doguwar Riga tayi mata kyau sosai amma babu kwalliya ko kadan a fuskarta banda kwalli da wet lips da nake iya ganin kyallinsa, sarkar da na bata ranar birthday dintace a wuyanta, kyan da sarkar tayi mata har yafi yadda ada nake zaton zatayi mata, bansan na kafa mata ido har yadda za'a ganeba sai da Rufaida ta taba hannuna na waigo da sauri kawai sai ji nayi sun saka dariya gaba dayansu. Kallonsu na tsayayi ina tunanin me sukewa dariya sai kuma na hade rai ina kallon Rufaida dake kusa dani nace "dariyar me kukeyi wai?" Tana kunshe dariyarta tace "yaya wai cewa mukayi ka fara cinye lomar hannunka sannan sai ka cigaba da kallon nata ba inda zata idan ba hakaba kuwa zata fadi kasa ita lomar" ta karasa fada tana kwashewa da dariya tana nuna hannuna, hannunnawa na kalla na debo loma da niyyar kaita baki su Fadima suka sauko dan haka hannun ya makale shi baikai bakinaba shi bai koma cikin plate dinba, dariya nima na kamayi kawai na cigaba da cin abincina ban kuma kulasuba.
Inajin ammie na yiwa Fadima fada akan zaman da tayi a daki can kasa na jiyo muryarta tana cewa "ammie ban dade da hawa samanba fa wanka nayi kuma ba kwanciya nayiba dama yanzu zan sauko" amsa ammie ta bata da "yauwa ai gwara ki daina wannan zaman kadaicin bashi da kyau kwata kwata". Ban kuma bi ta kansuba na cigaba da cin abincina har ammie ta tashi ta hau sama sannan Rumaisa ta dawo kusa dani tace "yaya" kai na dago na kalleta ba tare da na amsaba ta cigaba "ammie ta tashi" gira na hade alamar rashin fahimta tace "wai kallon nace ammie ta hau sama ko zaka cigaba" kallonta kawai na tsayayi sannan na dauko cup din dake kan table din na daga zan kwada mata ai kuwa tayi parlor da gudu tana dariya, kallon Fadima nayi tana kwance cikin kujera tana kallon TV da alama ta fahimci abinda muke cewa shiyasa ko dago kai batayi ba balle ta kallemu.
Ina gamawa na fita waje gidan uncle sagir na nufa ada banyi niyyar yin magana yanzuba amma tunda ta saka sarkannan na kuma tabbatarwa ta yadda dani dan haka da kwarin gwiwata na shiga bangaren uncle sagir, ina shiga na tarar da Bashir yana rubutu akan dining table ina shigowa ya gaisheni na amsa ina murmushi nace "Bashir ya dai rubutu ake?" Yace "eh yaya ina aikin makarantane" nace "yauwa Allah ya taimaka ina uncle" yace "yana daki na kirawo makashi?" Nace "yauwa yaron arziki maza idan ba abinda yake kace ina parlor" da sauri ya diro daga kujerar yayi sama ni kuma na zauna akan kujerar cikin parlon.
Bayan uncle sagir ya fito na gaisheshi ya amsa cikin fara'a yace "ya dai malam Na'im ya akayi kaninka yace kana nemana" wata kunya kuma naji ta dabaibayeni na fara susar keya ina cewa "eh uncle dama..am..cewa nayi" hannu ya dagamin sannan ya taso daga kwanciyar da yayi cikin kujera ya zauna sosai yana kallona yace "kaga Na'im ni mahaifinkane babu wani boye boye tsakaninmu ka fadamin abinda yake ranka babu damuwa ka gane?" Ajiyar zuciya na sauke sannan nace "akan maganar dama da kukayimin rannanne na matar da Zan aura shine nace bari nazo na gaya maka" na karasa fada ina sosa keya, dan dariya yayi yace "alhmdulillah ai haka mukeso dama aure ai shine cikar bawa duk kamalarsa duk arzikinsa idan bashi da aure bai cika kamili ba har addininsa ma bai cikaba idan har bashi da aure dan haka muna farin ciki sosai yanzu wacece yar gidan waye" dan shiru nayi ina tunanin yadda zai karbi maganar, kallona ya kumayi yana murmushi yace "Na'im " na amsa da "naam" yace "karkaji komai ka fadi ko wacece indai har tanada hali na gari ta fito daga babban gida baka da matsala sannan idan nace babban gida ba ina nufin wai gidan masu kudiba aa ina nufin gida na mutunci ka gane?" Kai na kadaya cigaba "ina jinka fadamin wacece" nace "amm uncle Fadima ce ta nan gidan" da sauri yace "Fadima dai tamu?" Kai na daga ina kallonsa ina kokarin karantar abinda ke ransa amma ga mamakina sai naga ya fara fara'a yana cewa "ahh alhmdulillah kai amma abu yayi dadi sai dai wani hanzari ba guduba ita fadiman ta yaddada kai?" Da kwarin gwiwata nace "eh uncle ta yadda da yardarta na Kawo maganar wajenka" ya kuma fadada fara'arsa yace "gaskiya naji dadin wannan maganar dama duk hankalinmu na kanta saboda maganar Saif dinnan data saka a ranta amma alhmdulillah tunda yanzu ta hakura ai haka akeso, dan haka yanzu ka barmin wannan maganar Zan sami su yaya Ibrahim zamuyi magana in sha Allah" nan nayi godiya na tashi na fito yau kam ko zan iya bacci?.
Washe gari uncle sagir ya yiwa su dady maganar nan da nan kuwa Abbie yace ya bayar dama ai 'yarsace shi kuma uncle sagir ya bada sadaki dubu dari aka saka rana tare da nasu Rufaida nan da watanni biyu kenan. Duk yadda nayi tsammanin abin ba haka yazoba alhmdulillah komai yazo cikin sauki ita kanta fadiman tamkar wadda aka canjamin ita tabbas yanzu soyayya muke ba yaya da kanwaba, a yanzu na kuma tabbatarwa Fadima na sona ba da rashin uwa zatayi daniba.
Shirye shiryen biki ya kankama Halifa kamar zaiyi hauka saboda bayanan za'ayi amma yace wallahi ko week end ne sai yazo dan bazaayi babushi ba Anty Rayya matar uncle sagir itace mai hadamin lefe sai dai kawai ace na Kawo kudi yayinda ammie da momy suka bazama had a kayan furnitures da kayan kitchen shima tun suna cewa na dauko kudi bankin gidan har na Kawo musu ATM card din gaba daya nace suyi yadda sukeso dan na gaji.

KAMU SEDANG MEMBACA
Fadimatu
Fiksi PenggemarLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...