Fadima
Shirye shiryen biki fa ya kankama kowa da abinda yake shiryawa, tun ana saura wata guda Anty zainab (yayar dady) ta hado kan gidanta gaba daga suka taho dama a Maiduguri take aure dan haka tace ta dauki nauyin gyaran jikin amare da duk abinda ya shafi wannan fannin, tunda da tazo din kuwa kullum idan ba'a mulkemu da wannan abinba za'a jikamu a wannan ko a dirka mana wannan. Tun ina mita ina guduwa har yanzu da kaina nake zama ayimin duk abinda za'ayi saboda ni kaina a yanzu ina iya zama na shafe wasu lokuta kawai ina kallon fatar jikina, ba dan karamin kyau mukayiba duk mu ukun kamar wadanda aka sake. Akwai 'yayanta su biyu humaira da hamida, humaira sa'a tace hamida kuma su Rumaisa ma sun girmeta amma da yake tana da girman jiki kuma ba wasu kawayene damuba sai kawai ta shige cikinmu, sune manyan kawayen amare sune akan komai sometimes nakanyi mitar da ace an bari na gama karatuna ai da bamuzo muna neman wanda zai tsaya mana kan harkarba.
Ana saura sati biyu biki ina zaune a daki na fito wanka ina shiryawa hamida tace "yaya Fadima kinsan ana bawa kanne gado idan za'ayi aure ko?" Dariya na fara dan na tabbata wani abun zatace na bata nace "ana bayarwa hamida me kikeso na baki?" Tace "sarkar wuyanki" sarkar yaya Na'im na shafa a wuyana tun ranar da na sakata haryau ban taba ciretaba nace "ayya hamida banda wannan fadi dai wani abun amma wannan ta alkawarice ba'a cirewa" dan hade rai tayi kamar mai shagwaba tace "to waye ya baki sai in tambayeshi da kaina" humaira dake gefe tana cin abinci tace "kai hamida naci da ba'asan asaliba" baki hamida ta kuma zunburowa tace "dadinta ma dai uwa daya ta haifemu indai ni mayyace kema mayyarce" tashi nayi ina saka kayana ina dariya, na tuna lokacin da yaya Na'im yacemin masifa kamar rainon titi ni kuma nace masa dadintama mace daya ta rainemu indan ni rainan titice shima haka, bayan na saka kayana najiyo wayata na vibrating a hannun hamida dake dannawa ta mikomin tana cewa "gaskiya a canja mana suna wanne irin yaya Na'im ana zaune kalau?" Karba ni dai kawai nayi ina girgiza kai hamida ta fiya barkwanci, ina dauka yace "zan iya ganin matata?" Murmushi nayi nace "me zai hana? Kana ina?" Yace "garden ki tahomin da ruwa please" ina neman hijabi nace "ruwa as in ruwa ko lemo?" A hankali kamar mai shirin bacci yace "kishirwa nakeji so ruwa as in ruwa" ya karasa fada yana kwaikwayar muryata, dariya na fara jin yadda yake nace "ni dai ba haka nake maganaba" makale murya ya sakeyi ya kwaikwayeni da cewa "to yaya kike magana" dariya nake yanzu sosai harda hawaye nace "wallahi kaima kasan ba haka nake maganaba" yace "shikenan kizo sai a dauki muryar kowa aji idan ba dai dai nakeba" nace "naji Bari nazo din" na kashe wayata na zira katon hijabin da yanzu aka sakamu sakawa har kasa da nikab wai ba'aso rana ta tabamu, amma dayake ba waje zaniba bansa nikab dinba. Kitchen na shiga na dauko masa ruwa mai dan rangwamen sanyi dan an fara kada sanyi, har na juyo zan fito sai kuma na koma na debo mana fruits na dora akan flate da wuka na dora akan tray sannan na dora masa ruwansa na fice zuwa garden.
Ina shiga na hangoshi karkashin wata bishiya can loko yana kwance akan grass carpet din wajen, can na bishi ina zuwa na ajiye tray din hannuna shi kuma ya tashi zaune yana min wani kallo sai da na zauna yace "wai wannan hijabin na magani da menene kuke fama dashi?" Zama nayi ina cewa "na kwalliyane" sai daya gama shan ruwansa sannan yace "kwalliya kuma da wannan uban hijabin a cikin gida? Dama fita zakuyi da sauki amma wannan ai aikine" wayata na dauko ina dannawa ban bashi amsaba ya zareta daga hannuna yace "tsakani da Allah fadamin hijabin menene saboda I'm curious da ace ke kadai kike sakawa sai nace saboda nine amma har su Rumaisa na furkanci yanzu abinda suke fama dashi kenan" dariya na farayi masa nace "to kai menene ruwanka da hijabinmu?" Da sauri yace "nikam nakeda ruwa dashi saboda an hanani ganin kwalliyar matata" dariya nayi nace "to sai dai ka tambayi Anty zainab ita ta sakamu sakawa nima ban san daliliba" komawa kawai yayi ya kwanta bai kuma wata maganarba sai ido daya kafamin kamar sabon warkewar makanta, ganin kallon nasa ba mai karewa bane na juya masa baya ai kuwa yayi saurin mikewa yana cewa "wallahi baki isaba ai dama cewa nayi kizo zan kalli matata ba cewa nayi ki juyamin bayaba" mikewa nayi ina cewa "ka bari sai na zama matar taka tukunna sai kai ta kalla" mikewa shima yayi zai kamoni ai kuwa nayi waje da gudu ina dariya shi kuma dole ya koma bai biyoniba.
Biki ya kankama sosai su hamida yan rawar kai an shirya events Kala Kala ranar talata za'ayi bridal shower da bachelor's night, laraba da daddare kuma dinner na family/friends, alhamis mother eve da arabian night, juma'a kamu, sabar kuma za'ayi normal wuni da safe a daura aure ranar lahadi kuma kai amare. Komai sukeso suna zuwa wajen yaya Na'im babu bincike zai cire ya bayar nikam mita nayi tayi events din sunyi yawa ya akeso muyi da gajiya bayan bikin. Ana saura sati daya daurin aure aka Kawo lefen su Rumaisa nan Anty Rayya ta fito da nawa itama ai kuwa aka yi ta kalla, lefen kowa kam alhmdulillah yayi kyau banda kar ace nayi sonkai da sai nace amma fa nawa yafi na kowa kyau dan kowa yazo kallo sai ya fada su Anty Rayya an iya zabe su yaya Na'im kuma an iya neman kudi da kashesu. Ranar da aka fara bikin a garden mukayi namu bridal shower din su yaya Na'im kam bansan inda sukayi nasuba shi dasu muazzam da abokanansu, bayan mun gama komai mun koma daki bajewa kawai nayi akan gado ina maida numfashi dan ba karamar rawa mukayiba idan nace bazanyiba sai suce wai wannan ne kawai zan iya rawa ragowar event din duk da iyaye inayin aure kuwa za'ace na girma bazan dinga rawaba, dan haka dole na saki jiki mukasha rawarmu, ina kwance akayi knocking kofar dakinmu hamidace ta amsa ya dan bude kofar kadan yace "in shigo?" Ai kuwa da sauri na mike zaune nace "Halifa?" Sai kuma ya turo kai kadan ciki yana dariya, da sauri nayi wajensa da gudu ina zuwa na rungumeshi sai kuka, dariya ya fara yimin yana cewa "wai Fadima bazaki girma da kukaba? Menene abin kukan kuma?" Sakinsa nayi ina goge fuskata nace "I was surprised ne banyi tsammaninka yau ba kuma nayi missing dinka sosai" jana yayi waje yana cewa "ina zan iya zama bikin kanwata da Yayana ina wani wajen? Nima sai juma'a nayi niyyar zuwa sai kuma naga kamar zuwa juma'a ai an gama bikin" fitowa mukayi waje kan ginin flowers muka zauna muna ta hira ya kara girma ga wani uban gashi daya tara kai da fuska sai dai na fuskar an gyara yayi dan siriri, kana ganinsa kasan yaji gyara dan sai daukar ido yake ya kwanta luf a jikinsa, kallonsa nayi nace "kai Halifa ka Kara wani girma wallahi kamar ba kaiba harda wani ajiye kasimba irin ka zama namiji dinnan" baki ya rike yana dariya yace "wallahi fadima ba karamin rainani kikayiba wato da ba namiji bane kenan?" Da sauri nace "tabbas muna namiji dai" dunguremin kai yayi yana cewa "ba zaki taba canjawaba" ji mukayi yaya Na'im yace "uhm uhm Halifa banda dungure kai fa? Kasan yanzu matar wanice" dariya muka saka gaba daya Halifa ya mike yana mika masa hannu suka gaisa yace "ashe kazo?" Halifa yace "ai kasan bazan iya zamaba kuma wallahi lectures muke amma bikin best kanwata ai is worth skipping class" Na'im yace "lallai kam to barka da zuwa bari naje na samawa bakina makwanci tukunna" yana gama fada ya sunkuyo dai dai kunnena yace "kinyi kyau" dariya na fara ina rufe kunne saboda iskar bakinsa da huramin yayin yin magana sannan kuma na rufe fuska, baibi ta kainaba ya wuce Halifa kuma ya zauna yana cewa "tab waya taba tsammanin yaya Na'im da Fadima zasu zauna a waje daya, fada balle har su fara soyayya?" Murmushi kawai nayi ban bashi amsaba, fuskarsa kuma ya maida serious yace "Fadima" nutsuwa nima nayi ina kallonsa na amsa da "naam" yace "tun a waya nasha tambayarki kinki tsayawa muyi magana Fadima da gaske kinason Na'im ko kuwa wani daliline yasa kika yadda zaki aureshi?" Shiru nayi na wasu seconds sannan nace "Halifa da gaske inason Na'im na yadda Zan aureshine saboda ina sonsa babu takurawa babu tilastawa, sannan ban yadda da auren Na'im saboda wani daliliba sai don na yadda ina sonsa kuma shima yana sona zai kuma iya bani duk wani farin ciki da 'ya mace ke bukata a gidan aurenta" ajiyar zuciya yayi yace "kin hakura da Saif kenan?" Nan da nan jikina yayi sanyi, jin sunansa kawai ya isa saka jikina yayi sanyi dan haka ban hakura dashiba kenan, a hankali idona na fara tara ruwa nace "Halifa ban hakura da Saif ba bakuma zan taba hakura da Saif ba amma kamar yadda kowa ke cewa na hakuran ina ganin is high time da ya kamata nai moving on, ya kamata na karbi kaddarar Allah ya daukeshi kamar yadda kowa ya dauka" na karasa fada ina goge furkata, ajiyar zuciya Halifa ya kumayi yace "kiyi hakuri Fadima ki cigaba dayi masa addu'a insha Allah bazakiyi dana sanin hukuncin kiba" haka mukayi ta hira dashi har can dare sosai kafa ta dauke sannan mukayi sallama na koma gida shima ya shiga gida.
Biki ya cigaba da tafiya yadda ya kamata,washe gari laraba magriba nayi yan mata aka fara shirin dinner dama su amatullah duk sunzo da su Sumayya roommate din su Rufaida, Allah ma ya taimakemu dagani har Rufaida bama sallah sai Rumaisace ake fada da ita akan wanke kwalliya, wanka kawai mukayi aka kumayi mana wata kwalliyar muka koma wajen dinner, wata gown muka saka ta milk din lace mai dan banzan kyau sai head, takalmi da clutch coffee color su kuma angwaye coffee shadda da aiki milk. Munyi kyau sosai sai tubarkallah kowa ke fada ana ta Masha Allah. An yi dinner an gama lafiya sai wajen 12am muka koma gida. Ranar alhamis akayi mothers eve a wani hall din shima a waje.
Ranar juma'a tunda na tashi da safe gabana ke faduwa dan haka nayi kwanciyata naki tashi har saida Anty zainab tazo kawo mana wani magani ta ganni kwance, tace "ke kuma Fadima lafiyar ki kike kwance har yanzu" dan tsaki nayi ina mikewa zaune nace "wallahi Anty banjin dadin jikina wani iri gabana sai faduwa yake" dan murmuahi tayi tace "banda abinki wannan uban hidima dama ai dole jiki ya fada sai ma an gama tukunna, faduwar gaba kuma dama kowacce amarya nayi sai ma gobe idan za'a daura aure, Allah dai ya sanya alkhairi" babu Wanda ya sami damar amsa mata dan dama dagani sai Rufaida ke saurararta ragowar nacan suna uwar magana babu maijin kan wani. Karba kawai nayi na shanye abinda take bani sannan na mike nayi toilet nayo wanka da ruwa mai matukar zafi ko jikin nawa zai saki naji dadi. Karfe hudu an gama decorating harabar estate din gaba daya an zuba kujeru da tebura daga can kuma an saka kujerun amarya da ango guda uku, wajen yayi kyau sosai mutane harsun fara cika yayinda mu kuma muke daki anayi mana kwalliya kamar za'a sake mana fuska, zuwa yanzu jikina har karkarwa yake ba karamin faduwa gabana yakeba bandama ina salati nonstop ai inajin da tuni na fadi. Bayan an gama komai wajen hudu da rabi amare suka fito muka taro angwayenmu daga bakin get kowacce ta jero da nata feena da suwaiba (kanwarsu Yusuf sa'ar feena) suna gaba suma sunci ado sai ni da yayi Na'im sai Rumaisa da muazzam sai Rufaida da Abdullahi sannan su hamida da sukasha anko na bakin kayan buzaye suma sun jeru a baya haka har mukakai wajen zaman mu. Muna zaune anata al'amura shagali yayi dadi yaya Na'im yace "Fadima menene naga jikinki na rawa" ido na dago da yayi narai narai kamar zan kuka nace "nima ban saniba tun dazu gabana ke faduwa jikina na rawa na rasa dalili" murmushin kwarin gwiwa yayimin yace "karki damu babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki kinji ko?" Kai kawai na kada na kuma maida kaina kasa, wayata na dauko na shiga WhatsApp na bude account din Saif na kura masa ido, shikenan yanzu dole na daina magana da Saif kenan? Tunda dai duk son da yaya Na'im yakemin dole na hakura da tunanin Saif idan ba so nake mu rinka samun matsalaba, hotonsa ma dole na hakura dashi amma Zan lallabashi idan ya yadda Zan tafi dashi ko boyewane nayi ba lallai sai na kafaba. Ina cikin wannan tunanin kawai naga duk text din dana taba turawa Saif yana double ticking kafin na gama tantance abinda ke faruwa ya koma blue tick alamar an bude text dina, wayarce ta zame daga hannuna ta fadi kasa sannan jikina ya kuma daukan rawa wadda har saida yaya Na'im ya jawoni jikinsa ya rike yanamin addu'a a kunne, numfashina kamar zai dauke da kyar nake fuzgarsa da sauri Halifa ya dauko jarkar ruwa yazo ya tsugunna a gabana yana bani, dan kadan nasha hawaye ya fara zuba a ido ina rike da Halifa bakina na rawa na kasa magana, hankalin kowa na wajen ya dawo kaina hatta dasu Rufaida hankalinsu na kaina a hankali kuma na fara dawowa dai dai duk da na kasa magana har yanzu. Feenace ta hawo dan step din da gudu tazo kusa dani su Halifa na tambayar if I'm OK ita kuma tayimin rada a kunne "yaya Fadima naga saifeena ya dawo" a zabure na kalleta tana faman washe baki sannan na juya na fara kalle kalle a wajen tare da kwacewa daga rikon da yaya Na'im yayimin na mike, can na hangoshi shima yana waige waige sai kuma muka hada ido nan muka kafawa juna ido tabbas shine Saif dinane ya dawo bai mutuba kamar yadda nayi tsammani, bakina na rufe da hannuna na fara kuka kowa hankalinsa ya koma kallon abinda nake kallo, da gudu natattare uban siket din jikina dage jan kasa na kwasa da gudu ba tare da tunanin aurena akeba, ba tare da tunanin yawan mutanen wajenba, ba tare da tunanin abinda zai iya zuwa ya dawoba ina kaiwa gareshi na rungumeshi ga mamakina shima rungumenin yayi.Tofa🙆🏻 munga bani yaya kenan? Na'im kana ruwa 😏😏.
Theory and thought.
CZYTASZ
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...