chapter 45

61 8 0
                                    

Saif's POV
A lokacin da na tafi Kaduna na tafine kawai badan nasoba, ganinake tamkar bazan dawoba ko kuma idan na dawo zan tarar wani abu ya sami Fatima, ina kaunarta da yawan da banajin zan iya jurar rashinta ko wani abu ya sameta. Washe garin dana koma kaduna yan kungiyar ta'addanci na  Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihad wadda akafi sani da boko haram sukakai farmaki makarantar 'yammata ta chibok dake Maiduguri suka kuma kwashe yara masu matukar yawa, a ranar muka tafi emergency rescue dajin da ake kyautata zaton yan ta'addan na amfani dashi a matsayin maboya, munyi ta faman nema amma bamu samu maboyar tasuba dan haka muka dawo camp da niyyar sai munyi amfani da satelite imagery munyi bincike sosai akan dajin kafin mu sake shiga, a lokacinne na samu na kira fadima, ba karamin dadi najiba da labarurrukan da ta bani na bayyanar ahalinta domin hakan na Kara kusantata danine idan dady ya koma cikin danginsa bazataji wahalar yadda da aurenaba ba zata kuma jinkirtamin mallakartaba"
"Haka muka cigaba da ayyukanmu har wata rana aka turamu da nufin muyo surveying dajin ta sama, mun shiga jirgin mu goma biyu na tuki yayinda mu takwas ke ayyukanmu da na'urori, bayan mun gama komai muka juya da nufin komawa camp a lokacin wani cikin comrades dina mai suna captain Idris Musa yake tambayata yadda ake amfani da wata sabuwar parachute da bai taba ganiba. Mun Riga da munsanta da yawanmu a jirgin dan haka na dauka na fara gwada masa yadda take, a ka'ida tare zamuyi dan ya fi fahimta hakan yasa shimaya saka daya ina gwada masa, mun gama kenan muna shirin cirewa kawai na hango tahowar wani abu ta window kafin na gama tantance abinda ke faruwa abin ya daki jirginmu nan da nan kuwa ya tarwatse. Har yanzu ina iya tuna tsokanar da sauran sojojin kewa idris muna dariya gaba daya, ina iya tuna fuskar kowanne daya daga cikinsu tamkar yanzu hakan yake faruwa, ina iya tuna yadda jirgin yayi pieces in seconds tare da tarwatsa dukkan ma'aikatan dake cikin. Bawai tarwatsewar jirginne ya kashe min comrades ba a'a nisan fadowar da kuma inda suka fadone saboda gaba daya wajen dajine kuma irin thick daji dinnan mai manyan bishiyu, parachute din jikinmu ni da idris ita ta taimakemu sai dai wata rashin sa'a da mukayi bai iyaba sosai dan haka da mukaje sauka sai lemar jikin nasa ta makale a jikin bishiya shi kuma ya zamana shi bai saukoba ba kuma ya sama yana reto, bayan na samu na sauka na dawo da niyyar taimakonsa amma kafin nakai gayin wani abu ya yanke igiyar da ta rikeshi ya fado kasa abinda yayi sanadiyyar karyewar kafafunsa dukka biyun banda ciyuka da yaji."
"Anan muka zauna jiran taimako ko za'azo taimakonmu amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kwananmu biyu idris na cin bakar wahala kafarsa tayi tsami cikin dare haka zai yi ta ihu saboda azaba babu yadda zanyi dashi. Kwananmu hudu a wajen kafarsa ta fara tsutsa saboda ciwokan da yaji a wajen karayar, a ranar da naga wannan abu ba karamin tashin hankali na shigaba idris comrade dinane tun lokacin da muke training muke tare dashi shine babban abokina a airforce amma gashi jikinsa na tsutsa amma babu yadda zanyi babu abinda zan iyayi masa. Ranar nayi kuka kamar zanyi menene saboda na zama marar amfani bani da amfani a wajen abokina a lokacin da ya fi bukatata. Kwanan mu goma a wajen na tashi da asuba na tarar yana bacci, ba karamar murna nayiba domin rabonda yayi bacci har na manta kullum kwana muke yana ihu ni kuma na zuba masa ido saboda babu abinda zan iyayi masa, tashi nayi nayi taimama kamar yadda na saba nayi sallar asuba, ina zaune ina azkar na jiyo karar jirgi a samanmu a razane na mike ina ihu da daga musu hannu amma bazasu jiyoniba ba zasu ganoniba sunyi nisa da yawa sannan bani da abinda zan amfani dashi ya zama signal ina kallo suka gama zagayensu suka wuce basu ganoniba, cike da bakin ciki na koma wajensa ina cewa "I'm sorry idris basu ganoniba basusan munananba naso su ganmu ko ka sami saukin wannan wahalar" magana nake ina kallon sama kamar Wanda zan kuma ganosu, jin bai amsaminba na kalleshi, sai a lokacin na fahimci something strange yanayin kwanciyarsa baiyi min kama da Wanda ke bacciba, sannan da bacci yake da tuni ya farka kodan ihun da na rinkayi. Da sauri na Isa wajensa ina jijjigashi ina ihun kiran sunansa amma ina! Ta Allah ta kasance ya mutu a wahale a kaskance. Nayi kuka tamkar yaro a wannnan lokacin saboda shi kadai nakeda yanzu zan koma ni kadai, kadaicima kawai sai ya kasheni banda wahala ga yunwa dan tunda mukazo bamuci wani abin arziki ba 'ya'yan itatuwane suma ba isarmu sukeba. Da hannu da itace na haka rami na dauki idris na saka a ciki ba wanna ba likkafani ni kadai na sallaceshi ina kuka ina komai na binneshi. A lokacin na fara tunanin mafita dama bazan iya zuwa ko ina da idris a halin da yakeba shiyasa na zauna a wajen, amma yanzu da babushi kuma alhmdulillah ina da isashshiyar lafiya dai dai gwargwado, dan haka na tashi na cire uniform dina na haka wani ramin kusa da kabarin idris na binne kayana tare da duk wani abu da zai nuna ni sojane domin idan aka gane hakan sai nafi shan wahala."
" tafiya nayi tayi ina tafe a hanya ina samun dan abinda zanci da kuma ruwan da zansha saboda a wancan dajin da muka fada da farko ko ruwa babu sai dai mu bula bishiya mu dan sami Wanda zamu jika makoshinmu, kwanana uku ina tafiya ban hadu da kowaba ban hadu da gariba sai kananan namun daji wadansu muyi fada wadansu na buya saboda bani da wani makami da zanyi fada dasu dashi, idan kuma dare yayi na sami bishiya mai duhu nahau na kwanta da safe na cigaba da tafiya. A rana ta hudune na kai matuka wajen galabaita saboda hatta da takalmana na ciresu a wancan wajen, ga sanyi dagani sai singlet da gajeran Wando suma dan Allah ya taimakeni ba na uniform bane, ina cikin tafiya har na fara daina gani na hango alamar gari dishi dishi saboda hayaki da na gano amma ban kai ga zuwa garinba na fadi a hanya ban kuma sanin inda kaina yakeba sai washe gari. Ina farkawa na ganni gidan wani tsoho da matarsa da 'ya'yansa yace shima yaje yin itace ya tsinceni" shiru Saif yayi na wani lokaci yana goge hawayen idonsa a hankali nan Abba yacewa Rumaisa ta dauko masa ruwa mai sanyi, bayan ya gamasha ya cigaba.
"Anan gidan baba nayi jinya har na samu karfina ya dawo sannan nayi niyyar tafiya dana sanar dashi sai yace "gaskiya dana bazaka iya tafiya da kankaba a halin da muke ciki domin kaga dajinnan a zagaye yake da yan boko haram idan kuwa ka sake suka kamaka to kasheka zasuyi, amma ka bari ranar juma'a dai dai lokacin sallar juma'a akwai hanyar da zan bi dakai idan sun tafi sallah sai ka gudu" na amince da baba na cigaba da zama tare dasu sai dai kaddara ta riga fata ranar alhamis din juma'ar da zai fito dani yan ta'addan suka shigo garin sukayi mana kacha kacha suka kashe na kashewa suka kwashi na kwasa Wanda har dani da baba da iyalinsa, a cikin garin suka hademu a waje daya suka kulle su kuma suka maye gidajen yan garin ya zama nasu suka cigaba da harkarsu. Bayan wasu satittika na wannan azaba, bazasu bamu abincin da zai ishemuba ba zakaje ko inaba wannan bandaki sai dai kun hadu da yawanku sannan zasu kaiku kuyi abinda zakuyi su dawo daku wannan wajen, babu maganar wanka kuwa sai da suka mila dan Kansu sannan suka sakemu amma babu Wanda zai fita daga garin ba kuma Wanda zai shigo. Abinda yafi komai tashin hankali shine dan laifi kalilan wani zaiyi musu zasu daga bindiga su harbeshi tamkar kiyashi, zasuzo cikin gida su hado kan iyalin gidan su zabi matan ciki suyi musu abinda sukeso babu kuma Wanda ya isa ya hanasu kuma a gaban yan uwansu, Mata a gaban mijinta 'ya a gaban ubanta har uwa dattijuwa zasu iya yiwa a gaban 'ya'yanta sai dai ku hadiyi zuciya ku mutu. Akwai wata yarinya wadda dama tun asalin garin na cikin kwanciyar hankali ansan yarinyar irin kyakykyawace sosai, tun zuwan mutanen garin ubanta ya boyeta a wani waje a kasan gidansa dan haka basu taba sanin da itaba sai tsautsayi kawai wani an kamo yarsa sai cewa yayi idan suka saketa zai fada musu inda zasu sami yarinya karama kuma mai kyau nan suka saketa shi kuma suka tisashi a gaba da alkawarin idan bai kaisuba zasu kasheshi kisan wulakanci, haka mutumin ya daukesu ya kaisu gidansu yarinyar suka bircikeshi da kyar suka ganota, ransu ya baci da abinda babanta yayi musu dan haka suka tara gaba daya garin.." Shiru yayi ya kasa ci gaba sai wata irin ajiyar zuciya da yakeyi hawaye na zuba a idonsa, jikinsa banda karkarwa babu abinda yake gaba daya jijiyoyin jikinsa sun tashi, ba karamin abin tsoro ya komaba dan babu Wanda yayi tsammanin Saif na da zuciya irin haka kaf wajen, kansa kawai ya kifa kan gwiyoyinsa ya saki wani irin kuka tamkar yaro, babu wanda yayi kokarin dakatar dashi sai da yayi mai isarsa sannan ya cigaba "dan zalinci irin na mutanennan haka suka yi raping yarinyar repeatedly a tsakiyar garin cikin dunbin mutanen dake wajen kuma sukace duk Wanda ya dauke kansa sai sun harbeshi, a gaban ubanta harda mai rike masa kai dan karya dauke kai ko wani abu suka gama suka harbe ta suka harbe baban nata. A lokacin nayi niyyar ko zasu kasheni sai nakashe ogansu na wajen amma babane ya rikeni yana kuka yana rokona dole na fasa zuwa, nayi danasanin saka parachute dinnan da nasan tashin hankalin da zan tarar kenan idan na rayun da na bari na mutu kawai nima na huta, naji na tsani kaina rayuwata bata da amfani tunda bazan iya kare masu rauni daga alummar annabi kuma yan kasataba, abu daya ke hanani nuna musu ni sojane saboda nasan the moment sukasan koni waye zasu kasheni" dago kai yayi ya kalli Fadima dake kuka a gefe ya cigaba "alkawarin da nayiwa Fatima, bazan iya karyashiba saboda nasan bazata taba karya nawaba tayimin alkawarin zata jirani komai daren dadewa ni kuma nayi mata alkawarin bazanyi wani abu da zai jawomin asarar rayuwataba. Abinda ya rikeni kenan tsahon wannan shekarun, na zana hoton fatima jikin abubuwa da yawa a duk inda nake zama saboda aduk lokacin da zuciya ta ciwoni zan kalla na tuna cewar tananan tana jirana ya kamata na jure koma menene na dawo gida. A wannan rayuwar nayi wannan shekarun uku cikin tsanani da tashin hankali, mu zamuje muyi noma amma idan mun girbe amfanin su zamu kaiwa matanmu kuma su dafa amma abinda ake bamu ko yan yara baya Isa kuma haka za'a tasamu mu kuma wani noman ba ruwansu da rashin karfi da yunwar dake tare damu, a lokacin da na shekara biyu a garinne sukazo gidanmu suka dauki 'yar autar Baba yarinyar gaba daya shekararta goma, abin ya tada mana hankali ainun nan Baba ya fara kokawa da wanda ke jan murja yana rokonsa ya sake masa yarinya tayi kankanta da yawa da wannan rayuwar, ina rike da ragowar matan dake kuka kawai wani yana shigowa ya daga bindiga ya harbe Baba ya fadi a wajen, bansan na Saki matanna doshesuba su hudune amma da yake a zuciye nake ba karamar illah nayi musuba, na sami nasarar kashe biyu da makaman hannunsu biyu kuma na barsu nan unconscious nayi wajen Baba amma ina! Ya rigamu gidan gaskiya" shiru ya kumayi yana hadiyar zuciyar tamkar zai hadiyeta gaba daya, kowa ka kalla a dakin cikin tashin hankali yake babu mai magana sai sheshekar kuka da matan keyi mazan kuma na kada kai kamar kadangaru.lol
"A ranar kuwa da ragowar yan uwansu suka fahimci abinda ya faru sukazo gidan, a ranar mun azabtu ba kadanba Wanda har saida nayi danasanin abinda nayi, bawai dan kainaba aa dansu murja da ragowar iyalin Baba da suke mata, sun wahala ba kadanba a wajen matar baban itama ta cika saboda azaba. Ganin irin dauriyar da na nuna a wannan lokacin yasa suka kyaleni amma da sharadin zan koma cikinsu tunda sunga ina da karfi da training. Shekara gudar da na kumayi babu Baba itace worse abinda ya faru dani a rayuwata, zasu sakani abu idan nakiyi su dauko murja suce zasu kasheta kawai saboda sunga na damu da ita, ni kuma a lokacin ita nake gani a matsayin Fatima duk da shekarunsu ba iri daya bane amma kawai kama take min da ita sannan Baba ma yanaji da ita matuka sanda yana raye. A haka na cigaba da rayuwa dasu akwai sanda sukace sai na kashe wani saurayi ni kuma naki babu yadda basuyi daniba naki wani acikinsu ya daga tashi bindigar zai harbi yaron ni kuma na harbeshi sukayo kaina nan na fara harbinsu duk wanda ya tasomin har bullet dina ya kare shine suka harbeni a ciki, Allah ya taimakeni batayimin illaba sunkayi zaton na mutu shi kuma yaron ya daukeni zuwa gida suka ciremin bullet din, amma da yake babu kayan aiki sai ya zamana na wahala ba kadanba har na zama unconscious bansan yadda akayi ba kawai na farka na ganni a asibiti, sai daga baya akacemin ai ina kwance sojoji suka kawo hari wajen suka kashe na kashewa suka Kama na kamawa mu kuma suka kawomu camp na yan gudun hijira. A wajen na fada musu koni waye sukayi contacting base dina suka tabbatar dani sannan suka yi transferring dina zuwa base dina dake Kaduna su kuma sukayi contacting family na"

Allah sarki Saif ansha wahala😭😭😭😭 akwai Allah karka damu zai saka mana.

Allah ya karemu da mugunji da mugun gani ya tsare mana ahali ameen🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾

FadimatuWhere stories live. Discover now