Chapter 10

103 10 0
                                    

Ranar haka na kwana kuka banyi bacciba sai da asuba bayan na idar da sallah dan gyangyadi ya daukeni a wajen, can cikin bacci naji motsi ina bude naga ashe halifane ya shigo duba momy, a tsorace yake kallona ai kuwa na mike da sauri ina kallonsa "meya faru?" "Ke zanyiwa wannan tambayar Fadima kukan me kikayi? Kinga idonki kuwa?" Ahankali na sauke ajiyar zuciya na zata wani abunne ya kuma faruwa, matsawa nayi kusa da momy na dafa hannunta hawaye na zubowa daga idona nace "Halifa sai dai addu'a amma wani mugun abu ya sami momy, bansan takamaimai menene ba amma tabbas wani abu ya sami momy" cike da neman karin bayani ya juyo dani muna fuskantar juna yace"Fadima yagamin abinda ya faru, Kodan kinga bata tashiba har yanzu? Kinga ki kwantar da hankalinki zata tashi in sha Allah kinji?" Kafin na bashi labarin abinda ya faru mukaga momyn ta kuma farkawa danhaka mukayi kanta da sauri, nikam tsoroma naji na kasa yi mata magana dan ina tsoron ta kuma yimin irin kallon da tayimin jiya, halifane ya fara cewa "sannu momy" itama tace "sannu momy" ya fara murmushi " akwai abinda yake miki ciwo? Ko na kira Dr?" Kallonsa kawai tayi sannan ta juyo da idonta zuwa kaina, nan da nan fuskarta ta canja daga emotionless kamar jiya zuwa murna sannnan tace"momy?" Jikina na karkarwa na kamo hannun Halifa yana juyowa na saka kuka "ka gani ko? Abinda takeyi kenan tun cikin dare is like bata sanniba bata taba ganinaba, Halifa kacemin ba abinda ya sami momy I can't take it anymore" cikin tashin hankali ya kalli momy ya juyo ya kalleni sannan juya ya kuma kallon momyn sai kuma ya kamo hannunta a hankali ai kuwa nayi saurin kwacewa ta takure jikinta a jikin gado tana ihu, da sauri na matso kusa da ita ina "momy halifane fa ba abinda zaiyi miki baki ganeshiba?" ai kuwa ta kankameni har wani ajiyar zuciya take tamkar wadda take a tsorace, da sauri Halifa yayi waje zuwa zan sai gasu da Dr na darenne dan haka yana shigowa yace "ashe ta tashin?" Na amsa masa da eh har yanzu tana kankame dani dan haka daga jikina yayi mata allura ta kuma komawa wani baccin sannan yace "yanzu zan turo nurses zasu daukarmin ita zamuyi mata test na kwakwalwa dan muga abinda ya sameta kar ki damu kinji insha Allah komai zaizo da sauki" kai kawai na iya gyada masa ya juya ya fita zuwa anjima nurses sukazo suka dorata akan wani karamin gado suka fita da ita, ahankali na sauke ajiyar zuciya hawaye na biyo fuskata na kalli Halifa ina kokarin gogewa nace "brother ka koma wajen dady kar yaga ka dade kasan hankalinsa zai tashine" shima ajiyar zuciyar ya saki sannan yace "Fadima bazan iya barinki on your own a wannan situation dinba ba kuma zan iya barin dady shi kadaiba" shiru yayi na yan seconds sannan yace "amma nasan yadda za'ai bari na koma dakin nasan yanzu zai koma bacci sai na dawo OK?" Kai kawai shima na daga masa dan banajin ayanzu zan iya magana ya juya ya fice, ni kuma na koma kusa da feena na zauna, baccinta takeyi tsakani da Allah yarinya babu ruwanta inama nice a yadda take? Koda yake da nice a yadda take bazan iya taimakon dady, momy ko halifaba.
Zuwa wani lokaci Halifa ya dawo mukayi jugum jugum muna jira, basu suka dawo da momyba sai da suka dauki wajen 2hrs sannnan suka shigo da ita, nurses ne suka kawota tana bacci kamar yadda suka fita da ita, sannan suka sanar mana Dr na office yana son ganinmu, Halifa ne ya tura kofar ya fara shiga bayan yayi knocking an amsa mana, muna shiga ya bamu wajen zama ya kuma cigaba da rubutun da yake a wani fayil sai bayan ya gama ya dago kai yana kallonmu, gaba dayanmu a tsorace muke da jiran me Dr zaice mana akan momy, sai da ya kallemu daya bayan daya sannan yace "wato abinda ya sami momynku abune wanda yake rare ba'a fiya samunsaba eto sai dai ko a cikin Fina finai ko littattafan hikaya amma duk da haka karkuji tsoro in sha Allah komai zaizo da sauki, abinda ya sameta a likitance muna kiransa da traumatic amnesia, shi traumatic amnesia ciwone da yake faruwa as a result of hard blow to the head, kamar abinda ya faru da momynku kanta ya bugu sosai dan haka jini ya taba wasu rukunin jijiyoyi da ake Kira da limbic system Wanda shine yake controlling memory na dukkan animals.." Halifane ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu sannan yace "I'm sorry to interrupt but wannan medical jagoon din naku ba fahimtarsa mukeba abinda kawai mukeso shine musan menene ya sami momy me kuma take bugaka?" Ga mamakina murmushi kawai Dr yayi sannan yace "kuyi hakuri na yankeshi, amm kamar yadda kuka bukata in brief abinda ya faru shine momynku ta samu ciwon traumatic amnesia wato memory loss, tayi losing memory dinta gaba daya as a result of that accident, yanzu bazata iya tuna ko da sunantaba, babu abinda zata iya tunawa har daku 'ya'yanta" da sauri na saka hannayena na toshe bakina gudun kar na saka musu ihu, innalillahi wa innailaihir rajiun shikenan dama abinda nake zargi kenan gashinan kuwa ya tabbata "innalillahi wa innailaihir rajiun yanzu Dr ya kake ganin za'ayi menene abinyi yanzu ya kamata ta dawo cikin hayyacinta domin muna bukatarta?" Halifane yayiwa Dr wannan tambayar shi kuma Dr ya bashi ansa da "idan har gaskiya kukeso na fada muku ba kamar yadda akai ta damfararku akan dadynkuba to ku kyaleta ku cigaba da yi mata addu'a Allah zai Kawo mata sauki amma gaskiya banajin anayin aikin traumatic amnesia a kasarnan indai kuma ba fita zakuyi waje da itaba, shima kuma a wajen idan anyi mata to babu tabbas din zata warke sannan akwai possibility na tabuwar brain nata idan bata warke dinba, advisible kawai ku maida ita gida, zan hada mata magunguna Wanda zasu taimaka mata kuma sai ku dinga yi mata abinda kukasan zai tuna Mata baya, kamar wuraren da kuke zuwa, maganganun da kukai da sauransu, ku kuma cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya" nidai ban sami bakin amsawaba amma naji kamar Halifa ya amsa da ameen" sannan ya kuma cewa Dr "yanxu kamar kwana nawa kake ganin zai dauka kafin ta dawo daidai?" Dr ya bashi amsa da "gaskiya Halifa babu specific time da zan iya baku kawai addu'a take bukata kamar yadda na fada muku" gyada kai kawai Halifa yayi sannan ya kamo hannuna muka fito daga office din zuwa dakin da momy take inda muka tarar feena ta farka tana ta faman kuka, muna shiga ta taho da gudu ta rungumeni, rungumar feena sai ta zama kamar fami akan ciwon dake cikin zuciyata dan haka nima na fashe da wani kuka mai ban tausayi, wannan wacce irin rayuwace? Daga wannan sai wannan? Yanzu ya zamuyi da dady idan yaji abinda ya samu momy? Me kuma zai sameshi? Yanzu ya zamuyi da rayuwarnan mu kadai ba dangi ba iyaye?, ranar nayi kuka kamar idona zai tsiyaye tun halifa na rarrashina har yayi shiru haka feena tun tana tayani har ta hakura tayi shiru sai ajiyar zuciya kawai da takeyi akai akai.
Sai wajen 12 feena tace "sister Fadima yunwa nakeji" wannanne ya sakamu farkawa daga tunanin da muke nayi saurin mikewa ina cewa "oh my God Halifa dady baici abinciba mun barshi shi kadai" shima da alama ya manta dan da sauri ya mike kamar wanda ya farka a bacci, abinci yaje ya siyo mana ya siyowa dadyma Wanda zai iyaci, dan haka muka dunguma zuwa dakin dadyn ai kuwa idonsa biyu shi kadai ba bakin magana ba kafar tafiya, Halifa yayi masa komai da ya kamata sannan ya bashi abincinsa muma muka zauna cin namu, kamar yadda mukayi tsammani dady kincin komai yayi kofa kawai yake kallo mu kuma muka maze tamkar bamusan me yake nufiba sai halifa dake ta kokarin ya karbi abincin, sai dayaga da gaske dai bazamuyi maganaba sannan a hankali yace "Fadima ina momynku take ko har yanzu ciwon kanne?" Da kyar na kakalo wani bushashshen murmushi nace "no dady ta warke yanzu zaka ganta in sha Allah tana hanya" har ajiyar zuciya sai da najiyo yayi jin cewa lafiyarta kalau baisan abinda yafi ciwon kaine ya sametaba.

FadimatuWhere stories live. Discover now