Chapter 5: what's going on

114 12 0
                                    

👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👦‍👦 *Fadimatu* 👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👦‍👦

By
Ummu saifeena

Ep5

Haka dai suka wuni suna juya maganar amma basu sami answer ba da momyn ma ta fito sai ta basar kamar babu abinda ya faru dan haka suma sai suka bar maganar. To a kwana biyun nan dai sun fahimci dole akwai abinda yake faruwa saboda al'adun gidan gaba daya sun canja dady ya daina dawowa da wuri wani lokacin ma sai sunyi bacci yake dawowa sannan walwalarsa da ta momy gaba data ta canja, wani abun mamaki kuma rannan suna zaune a harabar gidan kawai sukaga wasu mutane sunzo suna fita da motocin gidan kuma a wajen momy suka karbi keys din balle suce barayine dama motocin gidan hudune biyu na dady data ta momy daya ta su Fadima ta zuwa makaranta KO wani like, dan haka mutanen da sukazo sai suka hada ta momy, ta dady guda daya da tasu Fadima dama dady kuma ya fita da tasa guda daya, wannan Abu ba karamin dagawa su Fadima hankali yayiba dan haka suka je suka tasa momy a gaba da tambayoyi Halifa yace "wai momy me yake faruwa a gidannanne?" Dama sun tarar da ita tana shirya kaya a cikin sif ne kawai sai ta cigaba da abinda take tana cewa" kamar me fa? me ka gani?" "Momy tunda muka dawo muka fahimci wani Abu yana faruwa a gidannan gaba daya gidan ya canja kuma ke da dady kun canja ba haka muka Saba dakuba, sannan rannan mun tarar da ke kina kuka yau wasu mutane sunzo sun dauke motocin gidannan menene take faruwa" Fadima da sai yanzu tayi magana tace " first of all ma momy su waye wadannan mutanen? Momy yanzu dady ya daina dawowa muyi hira mustly ma sai munyi bacci yake shigowa gidannan gaba daya ya rame ya kare dole wani Abu yana faruwa momy mun girma zamu iya daukan komai a yanzu idan baku gaya mana matsalarku ba momy wa zaku gayawa ban taba ganin wani kunce dan uwanku bane KO abokinku balle kuce zaku gaya masa mudin dai mu kadai kuke da plss momy tell us what is going on uhmm?" Zuwa yanzu momy ta daina abinda take amma bata juyoba ba kuma tayi maganaba sai da ta dauki wasu seconds sannan tayi murmushi mai sauti tace " lallai yarannan har yanzu da sauranku tunda hakanan zaku fara zargi irin wannan to babu abinda yake faruwa yaune farko da kuka taba ganin anzo an dau motoci? Service za'ayi musu, dady kuma aiyukane sukayi masa yawa jiyama sai da yayi maganarku kwana biyu baya samun lokacin da zakuyi hira babu abinda yake faruwa dan haka banason irin wadannan tunane tunanen na banza kunaji ko?" Halifa ya daga kai da sauri duk da ba kallonsa takeba danshi ya yadda da abinda momy ta fada dama can ana zuwa yiwa motocinsu service sannan it's possible dady ya zama busy tunda dan kasuwane. Amma ga Fadima abin ba haka yakeba batasan daliliba amma bata yadda da abinda momy taceba, a hankali ta daga Kai ta kalli bayan momy da har yanzu bata juyoba a hankali tace " amma momy indai abinda kika fada hakane ba so kike ki rife mana wani abuba me yasa kika kasa juyowa ki kallemu?" A zuciye momyn ta juyo "saboda ku iyayenane Ina tsoronku shiyasa na kasa kallonku, Ashe Fadima baki da kunya? Me kike nufi? Karya nake muku KO me? Dallah Malama tashi ki ficemin daga daki fitsararriya marar kunya" ta fada tana nuna musu kofar fita "idan kuma dakin ma ban Isa dashi ba tunda uwata Fadima na ciki sai ni na fita nabar miki shi" haka jiki ba laka suka fito daga dakin, direct waje suka fita inda aka jera wasu kujerun karfe akan balcony din gidan (dama nanne wajen gulmarsu) suka zauna. kallon Fadima Halifa yayi sannan yace " haba sister why? Meyasa zaki nunawa momy tamkar baki yadda da itaba? Kema kin sani it's true dady yana zama busy sometimes tun kafin mu tafi Korea sannan ana zuwa yiwa motoci service dan haka ya kamata mu yadda da abinda ta fada beside idan wani abune yake faruwa tsakaninsu yanzune suke bukatarmu the most mu kwantar musu da hankali sannan mu daidaita ko wannne misunderstanding suka samu ba wai mu kuma tunzurasuba" ido Fadima ta dago tana kallon Halifa sannan tayi wani murmushi mai Kama da yake tace " brother kenan wlh abinda momy ta fada ba haka bane sannan nafi zargin wani abune ya faru amma ba fada sukeyiba nafi zargin financial crisis dady ke fama da, saboda jiya inajin momy tana cewa dady yayi hakuri wanda ya bashi waccan shi zai kuma bashi wata ya maida komai ba komaiba yasan bashi da lpy kar ciwonsa ya tashi" tayi saurin tasowa daga kujerar da ta jingina ta zauna sosai tana kallon Halifa sannan tace "yauwa dama dady yanada wani ciwone? Nidai ban tabaji ko  da tarihi ance yana da wani ciwoba " wani kallo Halifa ya bita dashi "yaushe kikaji suna wannan maganar?" Da sauri tace "jiya bayan mun kwanta sai na fito daukar fresh milk (al'adar yarance idan zasuyi karatu suna shan fresh milk ko chocolate) dan zanyi karatu shine najisu suna maganar suna hawa sama" shiru Halifa yayi alamar tunani sai can ya numfasa yace " tabbas duk Wanda kikaji ana yiwa irin wannan maganar to cikin biyu ya rasa daya ko 'ya'ya ko dukiya to mudai gamunan babu Wanda suka rasa it's probable dukiya amma kuma itama idan da ace abinda kike zargine kina ganin da zamu iya ci gaba da karatu a wata kasar a makaranta irin jeguk high school? Banajin that will be possible kuma ki duba gidanmu ki duba partyn da suka shiryamin na candy duk kina tsammanin wanda yake facing bankruptcy zai iya" murmushi Fadima tayi "brother u know dady wallahi zai iya koma menene saboda farin cikinmu amma ga shawara" ta fada tana kallon fuskarsa yace "fadi muji" ta kara matsowa "why not yau mu jira ko karfe nawa zaikai yau mu jirashi har ya dawo sannan mu zauna muyi masa magana maybe shi zai iya gaya mana" to idan yaki fada fa ko kuma shima ransa ya baci kamar na momy yanzu" ta kuma yin shiru zuwa can tace "muyi masa wayo da farko mu kawo wani abu na kudi mai yawa mu ce yayi mana sai mu kalli reaction dinsa ai munsan yadda yake mana da idan mun tambayi wani abu kaga daganan zamu samu kwarin gwiwar cigaba da wannan zargin ko barinsa" Halifa da har yanzu hankalinsa bai kwanta da wannan shawarar ba yace "to kuma idan muka gaya masa abinda bashi dashi muka sakashi cikin tashin hankalin yadda zaiyi kuma fa kinga mun dau alhakinsa" tana dariyar tace " kajika brother ai acikin reaction dinsa zamu gane indai bashi dashi sai muce kawai ma mun fasa kaga shikenan" Halifa ya gingina kai yanzu kam ya fara yadda da shawarar kanwar tasa sannan yace "to nima ga shawara why not muyi masa maganar komawarki makaranta? kinga idan yanadashi shikenan dama abinda zaiyine idan kuma bashi dashi sai asan yadda za'ayi ko?" Da sauri tace "yauwa bro ka Kawo shawara haka za'ayi" nan suka kwashe da dariya suka tafa.

A ranar bayan dare yayi sai suka kama kallon dole momy dai ta gaji tace "kunga nidai na tafi bacci nakeji, Fadima karki sake ki kwana kina kallo ki barmin yarinya ita kadai kinji ko?" Fadima tace " in sha Allahu momy sai da safe" "Allah ya kaimu" Halifa ma yayi mata sai da safe. Bayan shigar momy daki suka cigaba da kallonsu dady bai dawoba sai wajen 1am yana shigowa suka mike "welcome dady" da fara'arsa ya amsa musu yana " har yanzu bakuyi bacciba?" Fadima ta kwabe fuska kamar zatayi kuka harda buga kafa a kasa tana " dady kai muke jira munyi missing dinka" zama yayi cikin daya daga kujerun falon yana zaunar da ita a kusa dashi, cikin lallashi yace "ayya sorry sweetheart na zama busy kwana biyu amma in sha Allahu i will make it up to u ok?" Ta daga kai sannan ya mike yana "yauwa yaran kirki yanzu kuje Ku kwanta gobe in sha Allah babu inda zanje sai mu zauna muyi hira kunga yanzu na gaji" a tare suka mike Fadima tace "OK dady good night" shima yace "good night sweety" haka Halifa ma yayi masa good night ya amsa sannan kowa yayi dakinsa.

Ina fatan anyi sallah lafiya yan uwa ya gajiyar suya da fatan dai ba'aci anyi zuwa toilet ba. Ina fatan Allah ya maimaita mana ameen.
Kuyi hakuri dani banyi posting ba kwana biyu aiyukane sukayimin yawa ku cigaba da bina labarin fadimatu yana da tsaho da ban tausayi kuma in sha Allah zaku karu dashi dan yana da ma'ana da darussa

FadimatuDonde viven las historias. Descúbrelo ahora