Ba karamin tashin hankali muka shigaba ganin abinda ya sami dady dan haka muka daukoshi muka canja masa asibiti tare da fatan samun nasara amma nan dinma kudinmu kawai sukaci babu wani ci gaba da aka samu, a haka sai da mukaje asibiti hudu babu ci gaba, wani Dr dai ya bamu shawara akan mu hakura kawai mu maidashi gida idan yaso mu rinka kaishi gashi in sha Allah komai zai daidaita amma duk inda zamuje kudinmu kawai zasuci.
Wannan abu daya samemu yasa gaba daya momy ta fita hayyacinta ta rame ta kare kullum cikin tunani, lokaci da dama ma munsha kamata tana kuka amma sai tace ita ba kuka takeba, kullum cikin ciwon kai da jiri dama asalin momy nasan tana fama da low blood pressure dan haka yawan damuwar sai ya Kara worsening abin, haka dai zamu zauna muyi ta faman bata hakuri muna lallashinta tare da kwantar Mata da hankali.
Na dawo daga gida yammar wata alhamis nayo mana abinci, Ina shigowa asibitin zan hau stares kawai sai ganin momy nayi tana saukowa ina kallonta gabana ya fadi saboda ramar da take jikinta da bakin da tayi, a hankali na kakalo murmushi dan na bata kwarin gwaiwa amma sai na fahimcima sam hankalinta baya jikinta dan bata kula daniba, kafin nayi wani yunkuri kuwa kafarta ta zame dan da alama batasan tazo wajen steps dinba sai ganinta kawai nayi tana gangarowa kasa, wani mahaukacin ihu na saki tare da zubar da kayan hannuna ina kokarin tareta amma na kasa har saida ta kawo kasan benen ta cigaba kuma da mirginawa, unfortunately kuma nurses sun turo wani patient da gudu akan gado nan kanta ya daki tayar gadon ta kuma juyawa ta daki bango sannan ta tsaya, saboda tashin hankalima na kame ko motsi na kasa numfashina ma daukewa yayi dan gani nake tamkar ina ja zan janye da nata shikenan itama ta mutu, nan da nan wasu nurses suka kawo gado itama aka dorata suka turata zuwa wani daki. Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun kawai nake maimaitawa a zuciyata a hankali na fara dawowa cikin hayyacina, aikuwa na saka wani wahalallen kuka nayi dakin da dady yake da gudu, ina shiga Halifa na shirin fitowa dan haka muna yin Karo a bakin kofa yaga a halin da nake kawai ya jawoni mukayo waje, sai da ya mayar da kofar ya rife yadda dady bazai jiyo abinda muke fadaba sannan ya fara tambayata abinda ya faru " Halifa mun shiga uku momy ta mutu shikenan rayuwarmu tazo karshe dady ba lafiya ba momy shikenan bamu da sauran masoya a duniya babu sauran wadanda zasu taimaki rayuwarmu shikenan mun zama marayu momy ta tafi ta barmu" a rikice nake wannan maganar dan haka banajin ma yana fahimtar me nake fada sai da naji yana jijjigani tare da cewa "Fadima ki nutsu ki fadamin abinda ya faru Ina momyn me ya sameta?" Ina share hawayen fuskata wani na zuba na bashi labarin abinda ya faru, aikuwa kafin na gama fada ya yi kasa da gudu nima na rufa masa baya zuwa dakin da suka shiga da ita, muna shiga mukaga likitoci akanta nan da nan wasu nurses suka fito damu waje tare da bamu hakurin mu jirasu anan, kuka kawai nakeyi yayinda Halifa yayi zaman dirshan a kasa ya rike kansa da hannayensa tashin hankali karara a fuskarsa, sun fi awa guda ana shiga ana fita a dakin kafin suka fito, Dr yana fitowa muka mike muna kallonsa cike da neman karin bayani murmushi yayi mana sannan ya dafa kafadar Halifa yana cewa "ku kwantar da hankalinku in sha Allah babu abinda zai sameta zansa a maidata dakin dadyn naku idan ta farka zata dawo dai dai in sha Allah" da sauri Halifa ya girgiza kai yana "no Dr Kar ka hadasu a daki daya hankalinsa zai tashi idan yaga abinda ya sameta indai kana ganin zata farka da wuri kawai a barta a wani dakin idan yaso sai muce masa taje gida" Dr yayi murmushi tare da jinjina kai " hakanma yayi kanka yana ja, saboda idan ya ganta a haka hankalinsa zai tashi amma idan akace masa taje gida ba lallaine ya damuba"
Jin cewa babu abinda ya samu momy sai hankalina ya kwanta dan haka daga office din Dr direct dakin dady muka tafi na dubashi muka danyi hira duk da ba fiya fahimtar me yake cewa mukeba amma muna zama muyi hira dashi sosai, bayan wani lokaci nace masa zan koma gida idan an jima zamu dawo tare da momy yace to bayan na fito daga dakinsa na koma dakin da aka kwantar da momy, su biyune a dakin da wata tsohuwa na gaisheta tare da tambayarta jiki sannan na karasa kusa da momy tana nan yadda aka kwantar da ita , anan na cigaba da zama ina mammatsa mata jikinta har akayi sallar magriba akayi isha shiru bata farkaba, dan haka na yanke shawarar komawa wajen dady dan nasan karyar dazan hada masa sannan na dauko feena daga wajen Halifa mu dawo nan a zuwan mun koma gida. Ina shiga na tarar Halifa na yiwa dady tausa feena kuma na bashi labarin sabon school din da aka maidata, Dan haka nima naje na zauna kan kujerar kusa da dadyn ina tambayarsa jikin ido kawai ya limshe ya bude alamar da sauki sai kuma ya bini da kallon sannan ya kalli kofa, ko ba'a fadaba nasan momy yake nema dan haka na kakalo murmushi nace " kasan dady me ya faru?" Bai bani amsaba sai cigaba da kallona da yayi dan haka na cigaba " ina zuwa gida na tarar da momy wai kanta yana ciwo, kuma nasan rashin hutune da bacci dan haka na faki idonta nasa mata maganin bacci cikin abinci tana gamaci sai bacci, tana can na barota sai baccinta take" duk mukayi dariya a tare duk da tawa har da wani hawaye daya biyota nayi saurin sharewa dan kar dady ya gani sannan na cigaba "kasan dady matarnan taka she is so stubborn da cewa nayi ta kwanta ta lallami tayi baccin ba zatayiba amma yanzu gashinan tanayi" da murmushin yake Halifa yace " kinsan indai ba ganinta tayi gata ga dadyba hankalinta baya kwanciya shiyasa, yanzuma dan batasan me kikayi mataba" ahankali dady na genuine murmushi yace " saina gaya mata duk abinda kukace" feena ma tayi caraf tace" idan ka mantama dady zan tuna maka" nan na dungure mata kai tace "Dady" murmushi kawai yayi mata saboda bai fiya magana sosaiba, ko yaya yadanyi sai kaga jikinsa har karkarwa yake yana gumi kamar Wanda yayi wani aikin wahala.
Zuwa karfe tara na mike tare da cewa "dady Bari na koma wajen momy sai Halifa ya kwana anan idan ta farka gobe da safe ta zo" nan ya limshe ido ya bude alamar amsawa, na durkusa na dauki feena da ta fara bacci na saba a kafada sannan nace "good night dady" ya sake yi min murmushi lebensa na furta "good night". Tare da Halifa muka fito kamar zai rakamu sai da mukaje har dakin da momy take ya kuma dubata still dai bata farkaba amma daga dukkan alamu bacci take dan kana iya ganin saukar numfashinta, ya kalleni fuskarsa gwanin ban tausayi yace" yanzu kina ganin zaki iya kwana da ita ke kadai?" Da mamaki na kalleshi "kajika da wani abu brother me zai hana? Beside ba wani abu za'ayi mataba kawai dai karta farka da ganta ita kadaine" yana murmushi yace "cool down sister ba wai nace bazaki iya bane kawai naga harda feenane shiyasa amma" ya daga babban danyatsansa sama alamar thumb up yace " I know you can do it" sannan ya juya ya fita yana daga mana hannu.
Cikin dare na farka saboda dama baccin nawa rabi da rabine ina farkawa na duba momy, ina dubawa kuwa naga ta farka da murnata nace "momy?" Ta juyo kawai tana kallona, na fara murmushin dake hade da dariya ina cewa "thank momy kin farka I was so scared kar gari ya waye baki farkaba dady ya tambayi inda kike dama yanzuma karya nayi masa" still momy batace komaiba kallona kawai take emotionless hakan kuma bai dameniba Dan ni murna gaba daya ta gama cikamin ciki, a hankali na kamota ta tashi zaune na saka mata filo yadda zataji dadin kwanciya ina ci gaba da surutu "wallahi momy bakiga yadda na tdorataba haka halifama mun zata wani abinne ya sameki, amma Dr dama yace mana kina tashi shikenan dan ko targade bakiyiba, kai gaskiya mun gode Allah kinga tsahon stairs din da kika gangaro kuwa?" Na karasa maganar ina zama kusa da ita a kan gadon, still fa har yanzu kallona take, kallon kuma ya fara bani tsoro babu alamar sani a kwayar idonta tamkar bata taba ganinaba, ahankali na dafa hannunta nace "momy?" Ga mamakina itama sai tace "momy?" Na danji dadin maganar da tayi dan haka nace "zakisha ruwa? Ko tea zakisha?" Ahankali itama tace "zakisha" ba karamin faduwa gabana yayiba me kenan? Tashi nayi tsaye sosai nace " momy ya sunana?" Tace "momy?" Ai kuwa da gudu nayi waje sai office din Dr, wannan ba ma shine mai duty din dazuba amma ina zuwa ya biyoni dan nayi masa bayanin abinda ya faru, yazo yayi mata tambayoyi ya binkice sai dai duk abinda ya fada shi zata maimaita idan sentence din yayi mata tsaho kuma ta fadi wata word daga ciki ko guda dayace, ganin haka na fara kuka gashi babu halin na kira Halifa dady zai gane ina asibitin, da gwarin gwiwa Dr ya Fara lallashina "kinga kiyi shiru ki kwantar da hankalinki yanzu zanyi mata allurar bacci zuwa bayewar gari idan ta dawo dai dai shikenan idan kuma bata dawoba zamuyi mata tests muga abinda ya sameta kinji? Ki kwantar da hankalinki" yana gama fada ya juya ya fice zuwa can wata nurse ta shigo tayi Mata allurar ai kuwa kafin ta fita tayi bacci, haka na zauna na tasata a gaba na ringa kuka tamkar tababbiya me yake shirin faruwane? Me yake shirin samun momy? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.
YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...