Chapter 17

78 7 0
                                    

Washe gari da safe yazo yi mana sallama, bayan ya shiga wajen su momy yayi musu sukayi sallama da Halifa da feena suka wuce dama Halifa zai kai feena school ne shi kuma ya wuce waken aiki, bayan fitarsu na rakoshi har soro mukayi shiru dagani harshi kowa ya kasa magana, wani irin zafi nakeji zuciyata nayimin, munfi minti talatin a haka ba Wanda yayiwa wani magana kowa sai hadiyar zuciya yake ganin dai da gaske zai makara idan bai tafiba yasashi katse shurun da "kanwata Zan tafi" dagowa nayi kawai ina kallonsa shima ni yake kallo idonsa yayi ja nace "yaushe zaka dawo?" Sai daya hadiye wani abu sannan yace "bansaniba Fatima nima ban saniba abinda kawai na sani shine bazan dadeba zan dawo saboda bazan iya jurar rashinkuba ko na wuni dayane zan dawo" wani abu ya mikomin a leda na karba ina budewa naga kwalin waya ya cigaba da cewa "ki riketa a hannunki, na saka miki sim da komai zan rinka kiranki saboda bazan iya jurar rashin ji da ganinkiba dole na ragewa kaina wani abun, maganar aikinku kuma munje wajen jiya da Halifa idan ya dawo zaiyi miki bayani, dan Allah kiyi alkawarin zaki rike mutuncinki bazaki kula kowaba, ba karamin cutarda su dady zaiyiba idan har a halin da suke kika aikata wani abun, na yadda dake dan Allah karki bani kunya kinji?" Kai kawai na daga masa ina kuka, shima shiru yayi zuwa can yace "na tafi Fatima ina makara sai na dawo" nan ma kai kawai na daga masa ya juya ya fita ni kuma na zame na zauna a wajen ina kuka. sai da nayi mai isata sannan na tashi na koma cikin gida, akan gado kawai na kwanta banyi komai a gidanba har azahar sannan na fara yiwa kaina fada shin wai kukan me nakeyine? a Kaduna yake aiki ba wata uwa duniyaba dan haka zai dinga dawowa da wuri basai yayi shekaruba, sannan gaba daya yaushe muka hadu dashi da dan zai koma aiki zanyi kuka? Kawai na mike na girgije na shiga harkata, ammafa a kasan zuciyata ba karamin missing dinsa nayiba already.
Da yamma bayan Halifa ya dawo ya yimin bayanin wajen aikin, babu nisa daga gidanmu dan a kafama zamu iya zuwa sannan wai zasu rinka biyanmu 20k duk wata (Wanda nayi mamakin hakan sosai) sun kuma yadda zamu rinka shift na safe da yamma kamar yadda muka tsara da saif, zakuma mu fara ranar Monday yau kuma Wednesday munada 4days kenan nan gaba, sunada uniform wanda rigace me kamada jacket red da yellow rubutu sun bamu kowa bibbiyu dan haka a take na yanke shawarar zan dinga saka dogayen riguna ina dora rigar akai.
Tun daga ranar kullum muna tare da Halifa a gida ya daina zuwa aiki kafin ranar da zamu fara a zahra, wai shima hutawa zaiyi tunda muna da kayan abinci kuma muna da kudin motar kai dady gashi ranar friday, kwana biyu har min manta da matsalar motar gashi saboda da motar saif ake kaishi a dawo dashi amma yanzu babu.
Tunda saif ya tafi kullum da safe zai kirani mu gaisa na kaiwa dady da momy ya gaishesu su gaisa da Halifa da feena shikenan sai kuma da daddarre zai kirani muyi ta hira kamar ba zamu dainaba dama abinka da aku ya hadu da suda. Ranar Monday da safe muka shirya zamu tafi tare idan yaso ni ko shi wani sai ya dawo ya koma da yamma, na gama shirya feena nima da shirya cikin bakin doguwar riga nayi rolling mayafin rigar na rike rigar uniform din store din a hannuna in case ni zan zauna, bayan min gama shiryawa munci abinci sai muka tafi dakin su dady muka gaya masa zamu tafi wajen aikin, yayi mana addu'a sosai tare da nasihohi akan rike amana da kuma rike mutuncin kanmu, bayan ya gama na matsa kusa da momy na ce "momy kinga yanzu zamu fita waje ni da Halifa da feena zamu barku ke da dady, ki kula dashi kinji karkice zaki fita waje yanzu zan dawo kinji?" Kai kawai ta daga min yanzu ta zama wata irin shiru shiru, Halifa ya Dora dady akan wheelchair dinsa tunda tanada buttons zai iya tukata dan haka muka dorashi akai na kuma rife kitchen kar momy tace zatayi girki.
A kan bypass dinmu store din yake babbane sosai da katon parking space, bayan mun shiga ciki Halifa ya jani har zuwa office din manager dan muyi reporting muna shiga naga Abdul wannan dan uwan na saif mai shegen girman kai, bayan mun gama gaisawa yace "kuje ku nemi office din staff officer shine zai assigning naku duty din ku, office din yana kasa kusa da customer service kuce masa nine na turoku wadanda nayi masa magana jiya" to kawai mukace mukayo waje, muna saukowa kasa nace "Halifa" ya ansa da "naam" nace "kamar girman kan mutuminnan ya ragu ko?" Yana murmushi yace "dama can ba girman kan gareshiba kawai miskilancine amma yana da kirki" fuska kawai na yamutsa ina tuna zuwanshi gidanmu, wallahi girman kai gareshi.
Bayan munje aka bamu aikin da zamuyi, kasancewata mace yasa aka sakani a matsayin cashier saboda bazan iya aikin wahala ba sannan da sanayya idan ma na daukar musu kudi sunsan inda zasu nemoni, Halifa kuma aka sakashi cikin labourers. Sannan an raba mana duty Yau Halifa zai fara da morning 7am to 2pm ni kuma nayi afternoon 2pm to 9pm bayan sati kuma sai na koma morning shi kuma ya koma afternoon sannan za'a rinka biyanmu 20k per month. Bayan mun fito nayi masa sallama na koma gida shi kuma ya shiga cikin ma'aikata.
1:30pm na fita daga gida na bar gidan a hannun dady da feena ina zuwa Halifa ya taho ni kuma na koma office din staff officer muka taho tare dashi yayi introducing Dina a wajen ragowar ma'aikatan. Na fara aiki alhmdulillah babu wani wahala tunda wajen a cikine babu rana ga a.c ta koina sannan co workers sun kula dani sosai musamman Wanda aka hadani dashi ya koyamin aikin mai suna kamal, ya koyamin komai alhmdulillah na iya sannan na cigaba da aikina da kaina.
Yau satinmu biyu da fara aiki a zahra store kuma bamu sami wata matsalaba daga wajen aiki ko daga gida, tunda na Fara aiki ban taba haduwa da Abdul ba dama shi nake zaton zai zamemin matsala, sometimes dai nakanga wucewarsa amma bamu taba maganaba, kamal na kula dani sosai dan satin Dana koma afternoon ma shima ya koma ashe haka tsarin wajen yake sati sati kowa yake a kowanne shift. Yauma kamar kullum ina cikin aiki akayi sallar la'asar, to a ka'ida idan akayi kiran salla maza zasu tafi suyi sallah idan suka dawo sai mata suje da wadanda basa sallah kamar Christians suma su dan huta, bayan mazan sun dawo nima na tafi common room dinmu nayi sallah ina fitowa naga giftawar wani kamar Halifa azuciyata nace me Halifa yakeyi anan? Kar dai ace bai tafi gidaba tun tuni? Dan haka na bishi da sauri amma ban ganshiba sai bayan na hakura na taho kenan zan koma post dina kawai na hangoshi zai fita ai kuwa na bishi da dan guduna ina kiran "Halifa" ban sameshiba har ya bude wata mota haka na Kara sauri ina zuwa na rufe murfin motar ba tare da tunanin bamu fa da motaba, na tsugunna ina haki "dama tun dazu baka tafiba? Su momy fa?" Na fada ina dagowa daga tsugunnon da nayi, kamewa kawai nayi a wajen ina kallon halittar dake gabana, tabbas ba Halifa bane dan wannan ya girmi Halifa sosai at least zai bashi wasu shekaru bakwai haka amma fa carbon copy ne na Halifa ko kuma halifanne carbon copy nasa ban saniba, ina dai nufin kamar ta baci kamar da wannan bawan Allahn yake da Halifa tafi wadda dady yake dashi. Gaba daya na tafi tunani da mamaki bansan na saki baki ina kallonsaba sai jinai ya hankadeni tare da Jan wani uban tsaki, nan da nan na dawo hayyacina nace "oh my god I'm so sorry wallahi nayi zaton..." Bai Bari na karasaba ya daka min wata tsawa data firgita 'ya'yan hanjina ta kuma jawo hankalin mutane kanmu "dallah Malama matsa a wajen banzaye marasa kamun kai baku da aiki kudai kuga namiji kuce kunaso bansan inda yan matan zamani suka koyo rashin kunyaba wallahi har da gudu dan kar na bace ba aji ba komai" ba karamin ciwo maganarsa tayiminba naji ciwon abin sosai amma sai kawai nayi murmushi iron maiden ciwonnan kafin na bada amsa naji wani yayi magana a daya side din motar da alama tare suke bankula dashiba sai yanzu "haba yaya ya haka ka sani ko wani abin zata gaya maka? Wannan be kamataba bakaganta da uniform ba?" Tsaki ya kuma ja yace "babu abinda zata gayamin illa tace nayi Kama da wani dan uwanta ko abokinta excuse din nasu kenan kullum kaga dai sunyi getting attention dinka kansu, idan kuma ka musa tambayeta kaji" da kulawa wancan yace "baiwar Allah lafiya dai ko? Kin tsayar damu muna kan hanyane?" Wani hawayene mai zafi ya zubo daga fuskata ahankali na fara girgiza kai ina ja da baya nace "babu komai kuyi hakuri" sannan da sauri na juya zuwa cikin store din na barsu a wajen, ina shiga common room na koma sai da naci kukana mai isata sannan na wanke fuskata na fito ai kuwa idona yayi ja ya kumbura dan haka duk Wanda ya ganni sai ya tambayi abinda ya sameni sai kawai nayi murmushi nace "babu komai" ina cikin tafiya naji ana kirana da sauri na juya ga mamakina Abdul na gani yana tahowa yana zuwa ya karemin kallo yace "lafiya menene kike kuka?" Kasancewarsa jinin saif sai naji tamkar saif dinne kemin magana nan da man zuciyata ta karye wani kukan ya kuma tahowa dan haka yace muje office dinsa. Bayan min shiga ya bani wajen zama na zauna sai da nayi kukana mai isata sannan ya mikomin handkerchief dinsa na goge fuskata sannan ya zauna kujerar da take kallon wadda nake yace "uhmm ina jinki waya tabaki? Kinsan amana aka bani ke dan haka gayamin me akayi miki" da banyi niyyar gaya masaba saboda kar shima yayi zaton da gaske zubar da kimar na tafi yi amma sai naga maybe shi ya fahimceni kuma idan na gaya masa at least zan ji sanyin da Zan iya karasa aikin yau dan haka na zage na gaya masa duk abinda ya faru da dalilina nabin mutumin. Bayan na gama gaya masa ya zauna sosai yana kallona yace "kinsan wani Abu?" Na girgiza kai ya cigaba " you are so pure bakisan me duniya take cikiba da bazakibishiba saboda da kinsan duniya zakisan kallon da zaiyi miki kenan musamman ma da yake mota zai shiga zai tsammanin u are just like those gold diggers dake bin masu kudi, amma yanzu kiyi hakuri ki share hawayenki karki Bari hawayenki ya kuma zuba akan can wani banza kin gane kije ki cigaba da aikinki ki manta dashi kinji?" Kai kawai na daga na kuma goge idona sannna na mike nayi masa godiya na koma wajen aikina da gaske kuma naji sanyin had cikin zuciyata.
Tunda na koma gida dady da Halifa suka gane nayi kuka tambayar duniya nace musu ba kuka nayiba to haka saif ma yana kirana da daddare ina dauka sallamarsa kawai na amsa ya fara tambayar me ya sameni nace masa babu komai wai wallahi yaji bacin rai cikin muryata kamar ma nayi kuka, haka shima na shashantar da maganar kawai mukasha hirarmu kamar babu abinda ya faru ammafa deep down har yanzu inajin zuciyata na zafi.

FadimatuKde žijí příběhy. Začni objevovat