Kwanana biyu bayan faruwar wannan abin ban wareba, na dai hakura na daina kukan amma fa ban Saki jikiba sannan kullum sai nayi kuka kafin nayi bacci.
Ina kwance a daki akayi knocking sai da na tashi zaune sannan na amsa, Na'im ne ya turo kofar dakin ya shigo fuskarsa dauke da murmushi ya zauna kan gadon Rumaisa dake kusa da nawa yana kallona, nima kallonsa nake sannan na sunkuyar da kai na gaisheshi ya amsa still fuskarsa da murmushi yace "mi sœur kinga yadda kika rame kuwa dan kwana biyunnan?" Hannu na kai ina shafa wuyana nace "da gaske? Nikam banjiba" yace "dama bazakijiba mana tunda kinsan laifinkine, yanzu dai ba wannan ba taso muje wani abu Zan nuna miki" kallonsa kawai na tsayayi sai da ya mike ya kuma cewa "taso mana" sannan na mike, na dauko hijabina na biyoshi. A falo muka tarar da ammie ta fito daga kitchen da food flask a hannunta, kallonmu tayi fuskarta a sake tace "lallai ka ciri tuta tunda ka iya tasota daga kan wannan gadon nata" dariya yayi yace "dama ammie yayantane fa bazatayi min gaddama ba ko kanwata?" Ni dai murmushi kawai nake kaina a sunkuye ammie tace "to sai ina kuma " yana yin gaba yace "garden" ganin yayi waje Nima na bishi da sauri, bayan gidan Abba muka zagaya kamar yadda nayi tsammani kuwa farkon zuwanmu gardenne wajen mai kyau sosai, wajen a zagaye yake da godayen bishiyoyi Wanda suka hade suka bada kamar katanga ta zagaye wajen, ciki kuma bishiyoyine kalakala da masu 'yaya da marasa 'yaya wanin sha'awa, kasan wajen kuma grass carpet ne gaba daga sai daga tsakiyar wajen wani water fountain ne mai siffar mace da kwarya kamar tana shika ruwan kuma na zubowa daga cikin kwaryar zuwa ramin dake kasan fountain din, abinda yafi komai birgeni a wajen shine wasu yan kananan kifaye dake shawagi a cikin ruwan masu matukar kyau. Da sauri na karasa kusa da ruwan ina kallon kifayen, Na'im ma matsowa yayi ya tsugunna a kusa dani shima yana murmushi yace "sunyi miki kyau?" Da sauri na daga kai ina cewa "eh wallahi sunyi kyau sosai nawaye?" Wani gwangwani ya dauko ya zubo abin cikinsa abin kamar surfaffen gero amma baki ya fara zubawa a hankali a ciki yana cewa "nawane kinaso ne?" Hannu na mika masa nima ya zubomin abin ganin duk inda ya zuba kifayen na tahowa wajen sunaci nace "eh wallahi inasonsu sunyi kyau sosai, amma da yaya ake kiwonsu?" Yace "ba wahala kawai duk sati ana canja musu ruwa bayan an wanke wajen sannan ana kwashe wadanda suka girma abar kananan da aka Haifa kinsan manyan na cinye kanananne, sannan sai abinci da ake basu da measurement dinsa saboda idan yayi musu yawa ko yayi kadan zasu mutune " ina kallonsa nace "shikenan abinda ake musu?" Yace "sai mafi mahimmancin" dasauri na tamabayeshi "me kenan" yace "soyayya!" Mikewa yayi tsaye ni kuma na bishi da kallo daga inda nake tsugunne, sai da ya karewa wajen kallo sannan ya juyo muka hada ido nace "kamar ya soyayya" ya maida fuskarsa serious sannan yace "kaf wajennan an ginashine da soyayya da farin ciki, kifaye tsuntsaye da bishiyoyi abubuwane da suke fahimtar soyayya da farin cikin mai kula dasu idan har basu samun wadannan abubuwan zakiga suna mutuwane, duk wanda yake shigowa wajennan yana shigowane cikin farin ciki ya fita da annushuwa shiyasa kullum wajen yake kara habaka, saboda haka idan har kinsan bazaki karbi kaddararki kiyi farin ciki a cikin yan uwankiba to kar kiyi tsammanin Zan barki ki rinka shigowa nan, bawai ina nufin garden dinnan kawaiba a wannan maganar da nake miki a'a estate dinnan gaba daya familyn nan gaba daya" hannuna ya kamo saboda gaba daya jikina ya gama yin sanyi, muka zauna a kan wasu kujerun roba dake wajen sannan ya cigaba "fadima family dinki ba karamin sonki mukeba ko yaya wani abu ya saneki to kamar ya sami kowane a cikinmu dan wannan depression din da kika samu na kwana biyu wallahi sai da gidannan gaba daya ya canja, mu mutane muna iya danne damuwarmu domin farin cikin yan uwanmu me yasa ke bazakiyi hakan ba? Wannan abin fa da kikeyi bazai taba dawo mini da Saif ba munsan waye Saif a rayuwarki bakeba muma gaba daya bazamu taba mantawa dashiba saboda haka ki kwantar da hankalinki ki shiga cikin yan uwanki ki nuna mana soyaya da farin cikinki kamar yadda nayi imanin muma zamu nuna miki shi kuma Saifullahi kicigaba dayi masa addu'a idan yana raye Allah ya bayyana shi idan kuma baya raye Allah ya jikansa ya gafarta masa kinji ko?" Hannu nasa ina goge hawayen fuskata sannan nace masa "shikenan nayi alkawarin in sha Allah bazan kuma nuna tashin tankalinaba zan hakura na cigaba da addu'a kamar yadda ka fada babu abinda zai faru in sha Allah" sai yanzu ya saki fuskarsa yace "yauwa kokefa yar kanwata sannan kiyimin alkawarin duk abinda yake damunki zaki gayamin ba zaki barshi a zuciyarki ke kadai ba saboda dan nace ki daina nuna damuwarki hakan baya nufin idan wani abu na damunki bazaki fadawa waniba saboda mu lafiyarki muke bukatar ta dore kinji" nan kam kai kawai na daga masa yace "bakice kinyi alkawarin ba?" Nace "nayi alkawari" ya mikomin dan karamin dan yatsansa yace "pinki promise" nan na fara dariya ina goge hawayen fuskata nace "wai sai kace wata yar yarinya?" Shima yana dariya yace "ba zakiyimin wayoba fa oya pinki promise" ina dariya dole na sakala nawa yatsan cikin nasa.
Tun daga ranar na tattara komai na mikawa ubangiji na maida hankalina kan farantawa family na suma kuma babu mai yimin maganar da ta shafi Saif balle wata maganar aure wadda dama rigimace irinta tsohuwa mama, tsakanina da Saif kam sai addu'a kullum zan tashi karfe uku na dare bazan komaba sai nayi asuba ina yi masa addu'a tare da dukkan masoyana.
Hakan da nayi ba karamin faranta ran yan uwana yayiba sun nunamin jin dadinsu sosai nima kuma hakan yayimin dadi, tun daga wannan lokacin Na'im ma ya kuma ninka kyautatamin din da yakeyi kullum da inda zai kaini ko kuma da abinda zai tahomin dashi idan ya fita, gidajen yan uwanmu ba inda bai kaimuba ni da Halifa da feena dangin goggo da dangin Abba duk ya kaimu mun gaisa, haka wuraren tarihi na garin da wuraren shaatawa ba inda bamujeba.
Bayan komai ya lafa Na'im ya kuma tada maganar karatunmu dan haka su dady sukace yayi yadda ya kamata sun dorashi akan harkar, nan ya tambayi Halifa tunda shi ya kammala secondary school ina yakeson tafiya? Nan da nan yace shanghai jiao tong university china (university ta 8 mafi kyau a duniya mai shekaru 123 da kafuwa). Ni kuma tunda ban karasaba tawa ba dole sai na koma school dan haka yace zaiyimin register da wata school nan unguwarmu ai kuwa na tubure nace wallahi ban yaddaba da mamaki Na'im yace "to me kikeso ayi miki?" Cikin shagwaba na turo baki nace "kawai nima a maidani jeguk high " yamutsa fuska yayi yace "inane kuma jeguk high?" Nace "Korea inda muka Fara" dariya kawai Na'im ya Fara har da fadowa daga kujerar da yake zaune, nan da nan na hade rai ganin da gaske yaki dainawa kawai na saka kuka, da sauri ya daina dariyar ya taso yana cewa "ayya mi sœur ya hakuri menene na kuka kuma?" Still maganar yake amma kana kallonsa kasan danne dariyar yake dan haka na mike nayi wajen ammie da sauri ya bini yana bani hakuri. Ina zuwa kitchen wajen ammie tace "fadimatu lafiya? Ke dawa?" Kafin ta rufe bakinta Na'im ya shigo dan haka tace "dama nasan sai kai yayan kwabo, me yayi miki" ina kukan nace "ammie ya tambayi Halifa school din da yakeso ya fada dan nima na fadi wadda nakeso shine yakemin dariya" kallonsa ammie tayi har yanzu da alamar dariya a fuskarsa tace "menene abin dariyar a ciki?" Gyara fuska yayi ya hadiye dariyar sannan yace "ni ammie ba ita kadai nakewa dariyaba har shi halifan shi yace shonghai jiao tong China ita tace jeguk high Korea kuma ni tsakani da Allah daga ita har halifan ban gansu da kananan idanuwaba" yana kaiwa nan ya kuma kwashewa da dariya, ammie ma dariyar ta fara sai da kaina yayi booting sannan na fahimci me yake nufi nima kawai na saka dariya. Wato duk mun dauko kasashen masu kananan ido kenan alhalin mu ba kananan idoba balle ace Kama muke dasu.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...