Chapter 35

61 7 0
                                    

Babu yadda banyiba akan abarni na koma Korea na karasa karatuna amma anki yadda, momy ta tubure tace bazan komaba. Rannan na shiga wajenta da niyyar sake gwada sa'ata kozan iya lallabata ta hakura na koma, ina shiga nagansu zaune ita da Na'im suna hira naje na zauna kusa da ita na gaisheta ta amsa cikin sakin fuska sannan shima na gaisheshi sannan nace "momy dama akan maganar makarantane kinga ga yaya Na'im ma a zaune momy plss momy kinsan bazan iya yin exam a kasarnanba indai ba asarar wata shekarar zan kumayiba, tunda ban iya France ba dan Allah kinji?" Kallona tayi sannan tace "Fadima sai yaushe zaki gane abinda nake nufi? Na fada na kuma bazaki koma koreaba idan kuwa kikaga kin koma to magabatanane sukafi karfina tunda ni inajin maganarsu ke kuwa bakyaji kuma nasan ba zasu taba goyon bayankiba, sannan wannan nacin da kikemin shi yakesa nake kuma kafewa akan tawa maganar babu inda zaki kingane?" Hawaye ya fara taruwa a idona nace "momy to ya kikeso nayi dan Allah" ba tare da nuna kulawaba tace " ki shiga lessons kafin wata shekarar kin iya France din sai ki zana exam din anan" nan da nan kuwa hawayen da nake rikewa ya zubo nace "momy na girmi su Rufaida fa already a level 1 suke yanzu kuma na sake zaman jiran wata shekarar sannan na zauna jiran exams din ta fito kafin na Fara karatun? Momy sai yaushe zan gama kenan? " Na'im da tun da muka fara maganar baiyi maganaba sai yanzu yace " to momy ga shawara me zai hana ta koma Nigeria tayi exam din tunda Korean ne bakyaso?" Gaba dayanmu ni da momy muka fara girgiza kai momy tace "ai nisane banaso tayi idan ta koma Nigeria a wajen wa zata zauna? kaga andai gudu ba'a tsiraba kenan dashi da Korean duk daya" tana rufe baki nima na dauka da cewa "ni bama zan koma Nigeria ba sai Saif ya dawo" kallona kawai sukayi amma ba wanda ya tanka, zuwa can Na'im yace "amma gaskiya momy nima na fahimci inda Fadima ta dosa, karatunta anan bazai yiyuba ina ganin hakura zakiyi taje Nigerian ai ina zuwa sannan Tj yana can zamu saka mata ido idan yaso sai ayi mata registration na lessons anan ta fara zuwa kafin lokacin exam din nasu idan taje tayo ma ta cigaba da zuwa kafin result dinsu ya fiyo nasan ta iya France din kawai sai a sama mata admission a makarantarsu Rufaida kinga an rage asarar shekarun maimakon biyu anyi asarar daya amma ya kike gani?" Shiru tayi tana tunani zuwa can tace "hakan yayi kaga iya lokacin exams kawai zataje kenan sannan zata iya zama gidansu Saif suma kaga zasu rinka kula da ita ko bayan idonku" a firgice nake kallon momy nace "momy gidan su Saif fa kikace?" Tace "eh dama ai kin saba dasu Abdul da maryam kinga baki da matsala sannan mamansu na sonki zataji dadi idan kika zauna acan din" wani hawayene ya fara taruwa a idona nace "momy ita zataji dadi ni kuma fa? Ni baki damu da nawa jin dadinba? Momy karatu kikeson naje nayi ko mutuwa? Da yaya na danne zuciyata akan Saif anan ma balle akaini gidansu nayi rayuwa cikin gidan da ya rayu alhalin bayanan haba momy, na yadda zanyi asarar shekaru biyun amma bazan taba zama gidansu Saif ba" ina gama fadin hakan na tashi nayi waje da gudu ina kuka, garden na tafi na sami wata bishiya can a loko na takure jikinta ina kuka, zuwa can naji alamar zaman mutum kusa Dani amma ban dago kaiba sai dana yi dan kaina nayi shiru ina ajiyar zuciya, hannuna naji an taba na dago kai Na'im ne zaune a gabana da lemon tangerine a hannunsa ya mikomin daya wanda ya bare, kallonsa kawai na tsaya yi yace "karbi mana kina wani kallona" hannu na mika masa na karba shi kuma ya fara bare dayan, mun Dade a haka babu wanda yayi magana sai zuwa can yayi gyaran murya na dago ina kallonsa yace " fadimatu kiyi hakuri nasan abinda kika fada hakane bazaki taba jin dadin zama gidansu Saif ba amma abinda momy ta fasa shi kadaine solution, ba dadewa zakiyiba gaba daya bazaki wuce 2-3 month ba acan zaki dawo kiyi hakuri ki daure kinsan dai bazaki taba zama ke kadai a gida ba sannan bazaki iya zama tare da Tj ba tunda da abokanansa a gidan dan haka kiyi hakuri ki zauna gidansu Saif din, idan kuma kince kin fasa zuwa Nigeria baki da inda zaki, shekaru biyu ba wasa bane rayuwar ba a hannunmu takeba dan haka ki daure ki yadda da abinda momy ta fada kinji?" Bansan me yasa yanzu Na'im ke da tasiri a kainaba duk abinda ya fada sai na yadda dashi koda kuwa da ban yadda da abinba, ayanzu duk shawarar da ya bani sai naga kamar haka dama ya kamata nayi babu ja wannan yasa nan take naji zan iya zama a Nigeria Zan iya zama a gidansu Saif. Na amsa masa na yadda zan zauna nan ya cigaba da yimin nasihohi daga baya muka koma hira har sai da aka fara kiran sallar margiba wani kwaro ya cijeni a wajen sannan muka gudo.
Kamar yadda aka yanke Na'im yayimin register da wani wajen lesson na fara zuwa bayan wata biyu kuma yayi min registration na waec da neco a tsohuwar makarantarmu, inda Allah ya taimakeni suna boarding senior dan haka ya lallabasu da bayani da cin hanci suka daukeni a boarding din, wannan abin da Na'im yayimin ba karamin dadi yayiminba dan har wata rama nayi ta fargabar zaman gidansu Saif.
Lokacin da zan koma Nigeria har da masu kuka su Rufaida kamar bazasu barniba har airport suka rakoni suna kuka ina kuka, bayan mun sauka a kano gidansu Saif Na'im ya kaini ina shiga da sallama muka hadu da maryam dama na gaya mata zanzo, da gudu ta taho ta rungumeni tana murna kawai sai kuka tana fara kuka nima na saka kukan dama a gwiwa nake, mamansu ta fito daga daki da sauri tana tambayar "kai lafiya su waye ke kuka haka me ya faru?" Amma itama tana ganina jikinta yayi sanyi kawai ta juya ta koma daki. A ranar dai gidan kusan ba Wanda baiyi kukan tunawa da Saif ba kuma wani abin mamaki duk kira suke 'Allah ya jikansa ya gafarta masa' isata sukayi nace "wai Ku wayace muku ya mutune? Addu'a zakuyi Allah ya bayyanashi amma bai mutuba" mamansu tace "Fatima nasan kinason Saif amma muma duk muna sonsa tunda kikaga mun hakura mun dauki kaddarar Allah ya dauke Saif kema kawai ki hakura, Fatima idan yana raye yana ina? Anyi nema har an gaji ba'a samuba dan haka dole mu hakura"ina goge hawayen fuskata nace "mama idan kun hakura nidai ban hakuraba bazan taba hakuraba sai naga gawarsa ko na zama gawar ni amma bazan taba cire rai da dawowarsaba " ajiyar zuciya mama tayi tace "to Fatima Allah ya zaba mafi alkhairi ya zama gatansa idan yana rayen ko yana macen" duk mukace ameen.
Nan gidansu Saif na zauna har aka gama komai na registration dina sannan Na'im yazo ya daukeni da rakiyar su maryam ya kaini makaranta, da zasu tafi sai da nayi kuka kam na rike hannun Na'im banason ya tafi, idan ya tafi na zama ni kadai kenan a Nigeria bani da kowa, da kyar ya lallasheni sannan na cikashi suka tafi su maryam na tayimin dariya wai katuwa dani ina kuka dan an kawoni makaranta.
Da yake ba wasu shekarun kirki gareniba sannan bani da jiki sai ban zama ta daban cikin sauran students ba, banyi kawa ko dayaba na maida hankalina kan karatu ina yin na exams ina yin na France lessons dina ta online saboda banaso a wuceni. Watana biyu da sati biyu muka kammala exams duk sati dama sai maryam da Abdul sunzo min munsha hira, lokacin da na gama exams dinma Na'im baya kasar dan haka Abdul ne yazo ya daukeni, gidansu na koma na zauna sai Na'im yazo tukunna zamu tafi tare.
A wannan zaman da nayine bamu da hira sai ta Saif kullum da sabon labarin da za'a bani akansa, yarintarsa, barkwancinsa, jarumtarsa, da soyayyarsa ga ahalinsa komai kullum cikin maganarsa wannan yasa ba karamin jin dadin zaman gidan nayiba na sati biyu kafin Na'im ya shigo Nigeria. Ana washe gari zamu tafi ina dakin maryam ina hada kayana mamansu ta shigo, na gaisheta tace "oh ni su Fatima sai wani zumudi kike zaki tafi gida ko? Yanzu ba zaki zauna damuba kenan?" Dariya nayi nace "tab mama dan baki san da yadda momy ta barni na taho ba, shima sai da taji anan zan zauna tukunna" hannuna ta kamo  tace "zo muje kiga wani Abu" ba musu nabi bayanta har wani daki dake kusa dana Abdul, tana bude kofar hotonane ya fara yimin maraba, ban san dashiba dan da alama bansan sanda aka daukeniba, sai dana kura masa ido sannan na fahimci zanene bawai nidin bace na tuna ranar da Saif ya bayyanamin soyayyarsa na kashe masa waya washe gari da safe ya zo kofar gidanmu, tabbas murmushin da nayi masane a lokacin har kayan da lokon komai an saka banda feena da ke rike a hannuna a wancan lokacin. Bayanshi akwai zaninnikana da yawa a dakin wadanda suka zama tamkar hoto saboda duk na tuna lokutan da ya dauka. Wani hotonsane guda daya kan TV da uniform ajikinsa hoton yayi kyau sosai ya cire hular kansa ya sakata a hammata daya hannun kuma yayi salute dashi, hoyon na dauko na kurawa ido murmushin da yake tamkar Zan Kira sunansa ya amsa sai dai bashi din bane hotone kawai, dafani akayi ta baya hakan ya dawo dani daga tunanin da na tafi sai a lokacin na fahimci kuka nakeyi sosai, ahankali mama taja hannuna zuwa kan gadon dake dakin muka zauna itama kukan take tace "wannan mutane da suka rabamu da dan uwanmu masoyinmu Allah ka saka mana ka bi mana hakkinmu ba mu kadaiba har ragowar wadanda aka raba da masoyansu saboda zalinci Allah kasaka wa bayinka" a zuciya na amsa da ameen dan babu bakin amsawar. Haka mukasha kukanmu muka share hawaye sannan ta kalleni tace "Fatima idan da abinda kikeso a dakinnan ki dauka dan muma zamu share dakinne" kai na fara girgizawa ina cewa "no mama dan Allah karkuyiwa Saif haka bai mutuba karku share dakinsa dan Allah " kafadata ta dafa tace "shikenan mun fasa amma idan da abinda kikeso ki dauka ba zamu shareba" hoton hannuna na kalla nace "mama wannan kawai nakeso" tace "shikenan Fatima Allah ya Kara mana hakurin rashinsa" nace "ameen".

FadimatuWhere stories live. Discover now