Chapter 13

69 6 0
                                    

Ganin magariba na shirin yi sai kuma na fara jin tsoro kodai wani abun ya sami Halifa ne? Ya kamata ace ya dawo gida haka koda kuwa bai sami komaiba amma mu Ganshi idan yaso ya koma, fara wannan tunanin sai hankalina ya tsashi na taso na fito, ina fitowa na jiyo sheshshekar kuka a falo inda su momy ke bacci dan haka na leka sai naga momy na juyi ta rike cikinta tana kuka kuma da alama har yanzu bacci take cikin baccin take kukan, hankalina ya kuma tashi yanzu idan suka farka ya zanyi dasu nasan ci gaba zasuyi da kukan da sukayi bacci sunayi dan haka kawai na juya nayi waje koma ina zani dole cikin biyu nayi daya ko na nemo Halifa ko kuma na nemo abinda zamuci.
Ina fitowa na fara tafiya ba tare da nasan inda zaniba jefa kafa kawai nake ina hawaye ko ganin gabana banayi, bansan iya kacin tsahon tafiyar da nayiba nasan nadaiji ana kiran sallar magriba banyi auneba sai ji nayi wani abu mai karfi da dauri ya dakeni da karfinda sai da najini a cikin iska kafin na fado kan abinda ya dakenin sannan na gangaro kasa daganan kuma komai ya dauke ban kuma sanin inda nakeba.
Ahankali na fara bude idona bana ganin komai sai duhu sai daga baya duhun ya Fara washewa zuwa haske, bin dakin nake da kallo daga dukkan alamu dakin asibitine dan dan karamine mai farin fenti da karamin farin gado irin na asibiti sai loka irin ta asibiti da kujerar roba guda daya wadda wani mutum da bana iya ganin fuskarsa yake zaune yana karanta jarida, daga dukkan alamu darene dan na hango duhu ta window din dakin, wannan mutumin na kafawa ido inason sanin waye? Ina halifa? Nan da nan kaina yayi booting fitowa nayi neman Halifa nabaro momy, dady da feena najin yunwa gashi yanzu har dare yayi bansan me suke cikiba, kamar a cikin kaina naji feena ta kwadamin kira dan haka nayi zimbir na mike zaune tare da dafe kaina dake sarawa kamar zai fashe, da sauri mutumin dake zaunen ya ajiye jaridar hannunsa yayo wajena yana fadin "sannu kin tashi? Akwai inda yake miki ciwo?" Ban kula duk abinda take fadaba burina kawai na cire karin ruwan da akemin na fita, ina bukatar zuwa gida, ina bukatar nasan halinda su feena ke ciki. Da sauri ya rike hannuna yana"subhanallahi tsaya karki jiwa kanki ciwo, bari na kira likita ya dubaki" a fusace nace "bana bukatar wani likita, idan naji ciwonma ai ba jikinka bane ni kawai ka kyaleni, ina bukatar zuwa gida ina bukatar sanin halinda Halifa yake ciki ka kyaleni" jikinsa a sanyaye yace "kinga ki kwantar da hankalinki zaki tafi gida amma kin bugu sosai ya kamata kiga likita, duk da dai yace babu abinda ya sameki amma kiyi hakuri ki zauna yanzu zanje na kirawoshi sai ya sallameki" da kyar ya samu na zauna shi kuma ya fita zuwa can suka dawo da Dr ya dubani sannan yace bana bukatar komai zan iya tafiya amma na tabbatar idan naji wani abu na dawo. Bayan mun fito daga asibitin wannan mutumin yace " ga motatacan kizo muje sai na kaiki gida dan naga kina jan kafar bazaki iya tafiya da kankiba" da sauri nace "no thank you zan iya da kaina" tsayawa yayi kawai yana kallona bansan me yasaba kawai naji bakina na furta "shikenan muje" da murmushi yace "yauwa kokefa". Bayan na shiga motar yace yana zuwa, zuwa wani lokaci ya dawo ya bude seat din baya ya ajiye wata Leda sannan ya shigo mazaunan driver yana "yauwa ga maganinki nan idan mukaje sai kici abinci kisha magani, sannan kuma ko yaya kikaji kafar nayi miki wani abu ki dawo asibitin kinjiko?" Kai kawai na daga masa sannan ya cigaba bayan mun fito bakin titi "ina zamu dosa a ina kike?" Tunda na shiga motar sai yanzu nayi magana nace "hotoro bypass" dariya yayi sannan yace "to bypass wajen ina?" A hankali na kuma cewa "yan dodo opposite chula" ya kada kai sannan ya juya motar muka nufi inda nayi masa kwatance, da alama yana da surutu dan baiyi shiruba kuma cewa yayi "amma me ya kaiki depot?" Kallonsa kawai nayi na dauke kai sai dana mila dan kaina nace "depot kuma?" Da dauri yace "eh acan na kadeki kan titin da zakayi mariri dinnan" a raina nace lallai na tafiyu, a fili kuwa mirgina kai kawai nayi ban kuma maganaba. Zuwa wasu yan seconds ya kuma cewa "kodai wani wajen na miki ciwone?" Cikin gajiya nace "a'a" baiyi shiruba fa ci gaba yayi "alhmdulillah Allah yasa karshen wahalar kenan, amma har yanzu bansan sunankiba da na kaiki ma cewa nayi su saka miki Fatima kawai" da mamaki na kalleshi shima ya juyo ya kalleni sai kuma ya saki baki yana dariya "kar dai na fadi dai dai? Wow lallai kice na iya guessing kinsan sunan sister dinace shiyasa kawai nace a saka miki haka" da gaske na gaji da surutun mutumin nan Allah Allah kawai nake mu isa gida, ko ganin nayi banza dashine sai shima yayi shiru har mukazo chula nayi ta nuna masa hanya har gida.
Wajen 12pm ne yanzu dan haka unguwar ba kowa sai karnuka muna zuwa kofar gidan ya tsaya ni kuma na fito, kamar mutum nake gani kudundune a kofar gida ina maida kofar motar kuwa na rufe ya mike a firgice, "Fadima?" Muryar Halifa naji dan haka na tabbatar shine a wajen, akwai firgici da kuka a cikin muryarsa dan haka nima sai naji tawa zuciyar ta karye sai kuka, cikin kukan na amsa masa aikuwa yanajin ni dince da sauri ya karaso inda nake tare da rungumeni ya saka kuka tamkar wani dan karamin yaro, nima kukan nake shi kuwa wannan bawan Allan yana tsaye kawai yana kallonmu, cikin kuka Halifa ke magana "Fadima ina kikaje I was so scared nayi tsammanin wani abunne ya sameki hankalina ba karamin tashi yayiba babu inda ban nemaba babuke ba alamarki dady momy feena gaba daya kuka suke na rasa yadda zanyi dasu ina kikaje uhmm ina kikaje kika barmu?" Dago shi nayi ina share masa hawayen ina cewa "nima nayi zaton wani abune ya sameka ka fita tun safe baka dawoba ni kuma naji tsoro shine na fita nemanka kuma mota ta bigeni sai yanzu...." Bai bari na karasaba ya fara "what mota ta bigenki bakiji ciwoba? Oh my God Fadima why? Yanzu da wani abu ya sameki fa" ina murmushin ganin rikicewar da yayi yana faman duba jikina nace "hey calm down babu abinda ya sameni I'm OK " har da wata ajiyar zuciya ya saki yace "ohh thank God Fadima I can't take it anymore bansan yadda zanyiba idan wani abun ya sameki" murmushi kawai nayi nace "oya muje gida haka mayi maganar a can" har ga Allah na manta wai mutumne ya kawoni sai da muka juya zamu shige gida sannan yayi gyaran murya tare da cewa " forgotten someone?" Da sauri na juyo ina kallonsa sannan nace "ohh I'm sorry wannan yayanane halifa, Halifa ga Wanda ya kadenin" hannu mutumin ya miko masa amma sai Halifa yayi masa wani kallo daga kasa zuwa sama sannan yace "kai makahone zaka kade mutane?" Da sauri na daki kafadarsa tare da cewa "hey don't be rude tsautsayine beside ba hit and run bane ya kaini asibiti ya kuma dawo dani gida" na juya ina kallon mutumin "I'm sorry he's just looking after his sister" da murmushi kamar ba abinda ya faru yace "ba matsala namayi sa'a da banji naushiba" tsaki kawai Halifa yayi ya shige gida yana fadin "ke kuma taho mu tafi kafin yaji naushin" nabi bayansa da kallo har ya shige gida sannan na juyo nacema mutumin " I'm sorry and thank you for everything" da alama baya gajiya da murmushi dan har yanzu murmushinne a fuskarsa yace "don't mind ni ya kamata ma na baki hakuri sannan ga maganinki idan kinje sai ki sha kafin ki kwanta sannan Dr yace maybe kafar zatayi tsami kafin gobe da safe sai kinyi a hankali" yana fada yana mikomin ledar hannunsa ina karba ya juya da sauri ya shige mota yayi gaba. Halifane ya kuma lekowa "wai bazaki shigo bane ko zaki bishine?" Da dan saurin da zan iya nabi bayansa ina "kai Halifa wallahi babu dadi abinda kayi" yace " karki batamin rai shi da dadi abinda yayi? Ko kuwa kazace ke zaice bai gankiba ya kade?" Muna shiga tsakar gidan kafin na bashi amsa naji an kamamin kunne da sauri na dago momy na gani rike da kunnena ranta a hade tace "ina kikaje?" Wani hawayene mai zafi ya zubo a fuskata nayi missing wannan momyn, ta kuma cewa "ina kikaje" ina kuka nace "ba ko ina momy " ta kuma cewa " zaki kuma fita?" Ina girgiza kai nace "a'a" sai kuma ta cikani "shige" aka nunamin hanyar cikin daki. Halifa na kalla shima ni yake kallo yana murmushi kuma ga hawaye nace "wai saboda idan feena ta fita ina yi mata fada shine ko toilet na shiga bata ganniba sai tace ina kikaje? Zaki kuma fita? Kawai dai bata taba rikemin kunneba sannan expression dinta na yau irin serious dinnnan ne" yana goge hawayen da ya zubo masa yace " kinsan tunda ta tashi bacci take tsaye anan babu yadda bamuyi da itaba ni da feena taki komawa daki wai ita momy har gyangyadi take a tsaye amma kinga daga zuwanki ta shige dakin dama ke take jira" haka muka shiga daki yana bani labarin dramar da sukasha da momy da feena saboda basu ganniba, bayan mun shiga dady ya mikomin hannunsa da sauri ina dingishi na Isa gareshi na kama hannun ina cewa "I'm sorry dady na tayar muku da hankali nima ba a son raina bane amma ganinan na dawo ba abinda ya sameni" yace " Fadima ina kikaje gaba daya hankalinmu ya tashi mun zata wani abune ya sameki?" Kafin na bashi amsa Halifa ya rigani "wallahi dady Allah dai kawai ya tsare motace fa ta bigeta gashinan taji ciwo" nan da nan hankalin dady ya tashi "a ina? Bakiji ciwoba dai ko? Waye ma ya bigeki bashi da Idone?" Ina dariya nace "like father like son, kai dady da Halifa komai naku iri daya same reaction kuka nuna kuma banda abinka halifa ai sai ka tayar masa da hankali yayi zaton wani abunne ya faru ni kuma lafiya kalau, sannan ni na hau titin dan haka ku daina ganin laifinsa nawane" Halifa rai a hade yace "kawai dai zaki kareshine amma da ganinsa irin yan iskan garinnanne kuma kema haushinki nakeji har da wani siding nasa a gabansa ki bar Dan uwanki ko?" Ni abin nasuma dariya yake bani nace "Kaine ai Halifa mutum ya miko maka hannu kayi rejecting ai babu dadi" ai kuwa ya kuma harzuka "to aima laifinkine wayace ki fita daga gidannan da magariba idan ba nemarwa kaiba?" Nace "kaima ina ka shiga tun safe ka kasa dawowa duk hankalinmu ya tashi? Idan da me laifinma ai kaine ina kaje?ina bukatar explanation" zuwa yanzu dariya kawai dady yake mana, sai a lokacin halifa ya nemi wajen zama "wallahi tunda na fita ban sami aiki bane sai bayan azahar wani yazo wai muzo muje dawanau zamu dauko masa kaya shine fa muka tafi nima hankalina yana nan nasan na barku babu komai amma I'm sorry ok?" Momy ce tace "momy" nace "naam momy" ta wani rike ciki wai "cikina" da sauri na kalli Halifa yace "taki cin abinci tun dazu idan nace tazo taci sai tace momy maybe yanzu tunda kin dawo taci" nace "ka samo abincin?" "Eh amma ban iya girkiba beside bakinan bazan iya bata lokacina wajen girkiba instead of nemanki kawai sai na siyo mana garin kwaki da kulikuli yama jangwabe shima ban iyaba" haka ya dauko min garin kwakin na bata loma daya tayi ta tofomin abuna dan haka halifa yace akwai shinkafa da taliya ya siyo sai dai a dafa mata wani abun, ina kikewa zani kitchen nayi Karo da ledar da wannan bawan Allan ya bani ta magani amma sai naji dumi dan haka na tsaya dubawa ai kuwa sai ga naman kaza da yawa da lemon kwali, sai yanzu na tunama cewar ledar dama tayi nauyi da alama ba maganin bane kawai, na ware maganina naman kuma muka zauna mukaci dadyma yaci aka ragewa feena da yake ita ta riga tayi bacci.

FadimatuKde žijí příběhy. Začni objevovat