Ba karamin kuka nayiba jin wayar ta katse ji nakeyi kamar shikenan bazan sake ganinsaba mutuwa zaiyi, Dana gaji da kukan naga bazaiyimin maganiba sai na tashi naje nayo alwala na Fara gayawa ubangiji ina nema daukinsa ya kareminshi daga dukkanin sharri na mutum ko aljan ya dawo min dashi lafiya. Haka nayi ta fama har gari ya waye wani mugun ciwo kaina keyi abinne ya hade masa biyu ga kuka ga rashin bacci, ina fitowa momy ta tsaya tana kallona a tsorace tace "Fadima lafiyarki kalau kuwa? Me ya sameki haka " nan da nan idona ya kuma cikowa da kwalla nace "kaina ke ciwo" da mamaki tace " kuma shine kikayi ta kuka? Wannan idon nakidai daga ganinsa kuka kika sha me ya sameki?" Kafin na amsa mata Halifa ya shigo a shirye zai fita wajen aiki shima yana kallona yace " fadimatu me ya sameki kike kuka kinga idonki kuwa?" Ina goge hawayen idona nace "ba komai kaina fa ke ciwo" wani kallo yayimin sannan yace "har yanzu bai daga kiranba shine kike kuka?" Kawai sai kuka momy kam Halifa ta fara tambaya waye? Kasan Me akayi Mata?" Shikam Halifa jikansa ya jani yana bani hakuri sai da nayi mai isata sannan nace " Halifa ya kirani jiya da daddare" da alamar kulawa yake kallona jin bai bani amsaba na cigaba " yaki suka tafi da yan boko haram a Maiduguri" nan na basu labarin yadda mukayi jiya suma duk jikinsu yayi sanyi nan sukayi ta rarrashina momy na cewa "banda abinki Fadima addu'a ya kamata kiyi masa Allah ya dawo dashi lafiya ya rabashi da sharrin wannan mugayen mutanen amma ba kiyi ta kuka ba, yanzu kije ki zauna zan Kawo miki abinci kici kisha magani sai ki kwanta kiyi bacci kinjiko? Zai dawo lafiya in sha Allah" kai kawai na jinjina na koma daki, aikuwa ina cin abinci na sha magani sai bacci ba ni na tashiba sai da momy ta tasheni da azahar.
Bayan naci abinci na kuma shan magani muka fito tsakar gida dukkanmu halifane kawai babu, ganin yanzu su Na'im basanan yasa muke fitowa da dady idan ba wuta muyi hirarmu kamar yadda muka saba ada.
Ina cikin bawa dady labarin wata customer yau da tazo zahra ta sayi kaya na dubu hudu da dari biyar wai sai a rage mata dari biyar din ita tsakaninta da Allah ciniki zatayi kamar a kasuwa, nace bazai yiyuba shine wai toshikenan zata bada hudu da dari biyu kunga an rage mata dari uku kenan, muna ta faman dariya kawai sai jin sallama mukayi a razane gaba daya muka juya muna kallonsa a tsaye a bakin kofar soron ta ciki. Mu shi muke kallo yayinda shi kuma yake kallon dady, a hankali ya fara shigowa cikin gidan da matukar mamaki a fuskar dady yake kallonsa sannnan ya juya ya kalli momy yace "kubra waye wannan? Ya na ganshi kamar halifana" da sauri Na'im ya karaso gaban dady ya tsugunna tare da kwantar da kai akan cinyar dady wani irin kukane ya kwace masa yinsa kuma kawai yake ba tare da tunanin rikeshiba, dady kam mamakine ya rufe shi ya kasa sanin takamaimai menene ke faruwa ba sai shafa kansa yake alamar lallashi. A hankali momy ta zauna daga mikewar da tayi tun shigowar Na'im cikin tashin hankali kanta a kasa ta farawa dady magana "dady Na'im ne Na'im dinkane Na'im din yaya Ibrahim" nan da nan jikin dady ya fara karkarwa yana kallon momy cikin tashin hankali da bacin rai yace "ashe dama kubra still kinada contact da mutanennan a bayan idona? me kenan cin amanata zakiyi? Ko kuwa kin gaji da jinyatane zaki koma gida? Ko da yake dama sonkaine irin nawa dole tunda na nakasa kiyi tunanin komawa family dinki amma ki Sani ke kadai zaki koma dan ko gawata bana fatan ta koma wannan kasar bani da yan uwa bani da iyaye" yana gama fadin hakan yayi baya da kujerarsa tare da ture kan Na'im daga cinyarsa yayi hanyar cikin daki. Da gudu na mike na tare masa hanyar ina kuka yayin da momyma ke kuka nace " dady hear us out! Dady babu Wanda ya munafunceka babu Wanda ya gaji da jinyarka kai kasan koda ace ruwa jikinka yake yana tsutsa bazamu taba gajiya da jinyarkaba, dady momy taki Bari Ku hadu da Na'im ne saboda tana ganin you are not ready yet, you are not ready to face your past, dady momy tayi duk abinda tayine ko takeyi ko zatayi saboda tana Sonka batason abinda zai taba zuciyarka, dady for God sake ta yaya zakayi tunanin zata gaji dakai wai tace zata koma ta barka? A lokacinda baku dade da aureba ma baku da mu ta yadda tabar family din nata balle yanzu da kukayi going through abubuwa da yawa tare kuke da yaranda zata kalla taji dadi? dady ya kamata ka fara tsayawa ka saurareta kafin ka yanke mata hukunci" shiru nayi ina cigaba da kukana jin bazaiyi maganaba sai na matso kusa dashi na tsugunna a gabansa tare da kama hannayensa shima kukan yake nan nacigaba da cewa "dady Na'im yace gaskiya ta bayyana abbanka yana nemanka dady mamanka na missing dinka, dady kasan irin son da suke maka ya kamata ka koma kaji me zasuce, dady you are not vulnerable like before bazai iyayi maka komaiba kaji dadyna?" Wani kallo yakemin sannan yayi wani murmushi da nima sai da naji ciwonsa bashiba yace " bakisan komain ba Fadima bakisan me akayiminba, Abba yasan halina yasan abinda zan iya da Wanda bazan iyaba amma tayaya zai yadda da wannan sharrin fadimatu ta yaya? Sannan zakice wai I'm not vulnerable kalleni ki gani nine definition na vulnerability bani da kafar guduwa ko karfin fada ta yaya zan tari gidanda a cikinsa akwai wanda ya tsaneni da wanda yace idan ya kuma ganina sai dai a dau gawata?" Na'im ne ya taso ya dawo gaban dadyn shima sannan yace " uncle wallahi duk yanzu babu wadannan mutanen, uncle sagir bashine na da daka saniba umma ta rasu kuma kafin rasuwarta ta bayyana komai, bakaga halin da Abba ya shigaba a lokacin da gaskiya ta bayyana sai dakyar aka sami kansa yana blaming kansa da cewa yasan abinda zaka aikata da Wanda bazaka aikataba amma ya yadda ya koreka alhalin kanason ya tsaya kayi masa bayani amma yaki, yanzu haka ya dau dukkanin son da yake maka ya maidashi kaina saboda kamar da muke, har yau Abba Kabir yake cemin nine akan harkar komai nasa saboda da kaine, ni yake gani matsayinka kullum idan mutum zaiyi hira da Abba ta minti talatin sai ya yi masa labarinka yana missing dinka da yawa haka mama ma, dady plss ka koma gida dan Allah" hannayensa biyu yasa yana goge mana hawaye dagani har Na'im din a lokaci daya shima yana murmushi da kuma hawaye a tasa fuskar sannan yace "Zan koma Na'im amma ba yanzuba bazan koma a matsayin nakasashshe ba sai na sami lafiya" yana gama fadin haka yayi baya da kujerarsa ya zagayemu ya shige daki. Zama mukayi gaba daya a wajen kamar an zare mama laka dady yana nufin nan da shekara nawa kenan? Yanaso mu mutu ba tare da munga danginmuba kenan? Allah sarki Saif zanso yana nan ake wannan maganar shine babban Wanda zanyiwa albishir bayan halifa domin nasan Saif mai son farin ciki nane da dangina baki daya zan gaya masa naga dangina.
Da sauri Na'im ya tashi yayi waje nan muka zauna ina rarrashin momy har Halifa ya dawo na bashi labarin abinda ya faru shima yayi ta mamaki sannan muka zauna tunanin yadda zamuyi mu shawo kan dady ya hakura ya koma gida, akarshe dai mun bari akan momy zata cigaba da lallabashinsa idan yaki yadda muma sai mu shiga idan nan ma yaki yadda to sai muyi threatening dinsa ta hanyar daina walwala ko wani abu tunda dai munsan saboda shi zamuyi koma me zamuyi.
Washe gari ma haka muka saka dady a gaba muna faman rokonsa akan yayi hakuri mu koma gida shi kuma ya dage akan sai ya warke wai abinda yake fada shine yanzu idan ya koma ayadda yake bazai iyayin abubuwa da yawa da kansaba idan gaskiyar bata fitoba bazai iya kare kansaba balle mu sannan idan ya koma a haka zai zama defendant da abbansa Wanda hakan zaisa a kuma yi masa wani sharrin cikin sauki amma idan ya warke kuma arzikinsa ya dawo shikenan babu Wanda zai rainashi, amma abinda dady bai saniba shine abinda yakeso bawai nan da wani watan bane ko nan da wata biyu aa shekaru yake fagana. Har dare muna fama da dady shi kuwa Na'im tunda ya fita bai kuma dawowaba. Bayan mun kwanta kamar kullum ina ta trying number din Saif da wannan number din daya kirani ranar da zai tafi amma bata shiga, can wajen 1am har na hakura bacci ya fara dibana kawai naji ana kwankwasa kofar gidanmu, a tsorace na hantsilo daga kan gadon ina zare ido, tabbas da gaske kofarmu ake bugawa dan haka nayo tsakar gida da sauri muka fito tare da momy sannan muka jiyo motsin Halifa shima ya fito daga dakinsa da sauri momy tayi kiransa ya shigo tsakar gidan tace " karka bude halifa" kafin ya bata amsa aka kuma buga kofar muka kalli kofar a tare sannan Halifa yace "momy idan kuma wani emergency abinne fa?" Tace "kanada Wanda zaizo maka da emergency dinne? Baka dashi Halifa babu Wanda zai buga maka kofa cikin dare idan ba muguba" murmushin kargin hali halifa yayiwa momy yace "kamar yadda babu mugun da zaizo gidannan momy, bamu da kudi bamu da wata kadara dazai sata sannan mugu bazai buga maka kofaba" ita dai momy babu yadda zatayine Halifa ya tafi soron mu kuma muna daga bakin kofar soron ta ciki muna kallon kofar waje. "Waye?" Halifa ya tambaya kafin ya bude kofar daga can mukaji ance "Halifa bude Na'im ne" da mamaki gaba daya muka maimaita "Na'im?" Da sauri Halifa ya bude Na'im ya shigo Halifa na cewa "Na'im lafiya a darenan duk ka bamu tsoro wall..." Bai kai ga karasawaba wani tsoho ya shigo yana rike da wata mata wadda daga dukkan alamu matarsace sai kuma wasu yan mata wadanda bazasu wuce sa'anninaba su biyu sai wata tsohuwa da wasu da sukayimin Kama da wasu mata da mijin, da sauri momy ta rufe bakinta da hannunta sannan ta saka kuka a lokaci daya amma marar sauti. Wannan mata da mijin da suka shigo a karshe matar ta taho da dan gudunta ta rungume momy itama tana kuka, suma ragowar gaba daya kukan suke. Daga daki na jiyo dady yana kiranmu dan haka nayi ciki da gudu ina shiga ya fara tambayata "waye yake buga kofar? Meya faru naga jikinki na karkarwa ina kubra da Halifa? Ina feena?" Babu amsar tambayar dana bashi illah fara kokarin dorashi a wheelchair dinsa da nakeyi, dayake shima burinsa kawai ya fito din yasa na iya dorashi mukayo waje da sauri, a tsakar gida muka tarar dasu muna fitowa naji wannan tsohon na farko da sai yanzu na ga kamarsa da dadyna, halifana da kuma Na'im yana cewa "kubra ina Kabir din? ki nunamin inda Kabir dina yake" kuka yakeyi sosai sannan kuma cak kukan ya dauke yayinda ya ganni tare da dady a wheelchair da sauri ya karaso ya rungume shi yana fadin "me ya sameka haka Kabir? Innalillahi wainnailaihir rajiun, Kabir ka yafemin nayi kuskure dana koreka ka gafartawa babanka dan Allah Kabir kazo mu koma gida ina sonka kai kasan ina sonka fiye da komai na rayuwata fiye da rayuwata ma gaba daya kabir manzon Allah saw kawai nakewa son dayafi naka amma babu wani abu da nakeso a doron kasa sama da kai kayimin afuwa nayi nadama nayi nadama marar misaltuwa nayi kewarka ba kadanba" kuka kawai yake yana sambatu shima dadyn kuka yake, kaf gidan kowa kuka yake kamar wanda akayi mutuwa nidai na koma gefe kukan nima kawai nake ina binsu da kallo. Sai da sukaci kukansu suka koshi sannan dady ya dago abbansa daga rungumar da yayi masa yana cewa "Abba na sani na san kana sona nasan ba acikin hayyacinka kayimin abinda kayinba kuma na yafe maka tun tuni na kasa dawowane saboda ina tsoron kar har yanzu baka huceba banaso kayi abinda daga baya zaizo ya dameka Abba amma na dade da yafe maka na dade ina kewarka ina son ganinka inason ganin mamana"ya karasa fada yana kallon matar da suka shigo tare, hannu ya mika mata itama ta miko masa sannan ta karasu wajensa ta rungumeshi shi kuma Abba ya hadasu duk su biyun ya rungume suna faman zubar hawayen farin ciki.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...