Chapter 44

68 6 0
                                    

Fadima
Numfashina jinsa nake tamkar zai dauke saboda karfin bugawar da zucuyata take, karfin kukan da nake da kuma irin rukon da nayi masa, a hankali na sassauta rukon na fara hakin neman numfashina da baya kaiwa cikina, ina iya jiyo muryar Halifa can sama yana rokona akan na sakeshi amma gani nake ina cikashi zan farka daga mafarkin, gwara na cigaba na kare rayuwa ina mafarkin Saif ya dawo dana sakeshi na farka. Fizgata naji anyi daga jikinsa kafin na gama daidaita kaina na kalli wanda ya rabani da rukon da nayiwa Saif naji saukar Mari a kuncina wanda yayi sanadin karasa daukewar numfashin da nake kokawa dashi.
Ummu Saifeena
Fadima na tashi ta tafi wajen Saif Na'im ya mike tsaye kana ganinsa kasan a cikin tashin hankali yake, ko gani bayayi ya juya yabar wajen ba tare da yayi yunkurin zuwa inda sukeba, wasu matane kannan ammie dake tsaitsaye kamar yadda kowa na wajen ya mike tsaye su suka fahimci barinsa wajen nan fa suka fara surutai, daya daga cikinsu tace "wannan wai wayene?" Wata ta bata amsa da "waya sani fa? Ni fa wallahi dama aurennan bai kwantamin akaiba saboda yadda naga son da Na'im kewa yarinyar yayi yawa wahalar dashi kawai zatayi" wadda ta fara magana tace "wallahi kam amma har da rashin kamun kai inba hakaba a gaban Wanda zaki aura da iyayensa da naki iyayen kije ki rungume wani kato? Kai alhmdulillah tarbiya ma dai dadi gareta" wata da bata tankaba sai yanzu tace "to da tayaya zakiyi tsammanin samun tarbiya a wajen wannan yarinyar? Yarinyar da akace tun tana yar mitsitsiyarta suka dauketa ita kadai ba dangin uwa ba na uba suka kaita kasar marasa tarbiya, nifa kamar China ma naji ance an kaita sai daga baya ta dawo" dayar ta amsa da "haka naji wai dan uwan natama yana can yanzu biki yazo, lallai kam dole suyi abinda yafi haka kunga kuzo muyi gaba tunkafin muga abinda yafi karfin idonmu dan naga da alama za'a iyayin abinda yafi runguma a wajennan" tana gama fada kafin su bar wajen Anty zainab dake jinsu tayi musu wani kallo sannan tace "duk abinda ka aibanta dan wani dashi dai sai ya sami naka" tana gama fadar hakan tayi wajen su Fadima da mutane suka maida abin kallo ta hankade Halifa dake kokarin banbareta daga jikin Saif ita ta banbaretan a zuciye tana juyowa kuwa ta kifa mata mari dan ba zata jawo musu abin magana a dangi ba, tana marinta kuwa ta zube a wajen sumammiya, sai kuma jikinta yayi sanyi. Saif da halifane sukayi kanta suna kiran sunanta amma ina! babu alamar numfashi dan haka Halifa ya sunkuya ya dauketa yayi hanyar gidan Abba da ita tamkar matacciya, a bakin kofa suka hadu da Abban yace "maza kaita dakina kar abar kowa ya shiga bari na kirawo likita" da sauri tamkar ba dan mutum ya daukoba ya haura sama da ita zuwa bedroom din abba, kan Gado ya kwantar da ita sannan ya dauko ruwa mai sanyi yana shafa mata, kofar dakin aka bude mama da goggo da sukaci ango iri daya suka shigo sukayi kanta suma amma still babu numfashi a jikinta dan haka suka fita neman agaji akabar Halifa tare da ita.
Su Abbie dake wajene suka jiyo hayaniya dan haka sukayo cikin gida nan suka tarar da amare na faman kuka mutane anyi cako cako ana jimami, Anty zainab na gefe sai gursheken kuka take tana "shikenan na kasheta na shiga uku na kashe rai" dakyar suka samu akayi musu bayanin abinda ya faru suma sukai gidan Abba da sauri, a bakin kofar gidan sukaga Saif yana faman safa da marwa suna zuwa dady ya ganeshi da matukar mamaki yace "Saif? Saifuddeeni kaine nake gani? dama kana raye?" Da sauri Saif ya daina zagayen da yakeyi yazo ya rike dady wani hawayen farin ciki na zuba a idonsa yace "dady nine ban mutuba na dawo, dadyna kana tafiya alhmdulillah yaushe?" Shima dady dariya yake hade da share hawaye yace "tun watannin baya na fara tafiya Saif ya akai ka tsira? Duk mun dauka ka mutu" Saif ma na goge hawayen fuskarsa yace "dady labarin da tsaho ku fara duba Fadima kar wani abu ya sameta" dan dukan kafadarsa dady ya fara alamar rarrashi yace "karka damu an kirawo Dr din dake dubata babu abinda zai faru in sha Allah" kai kawai ya daga masa sannan dady ya kama hannunsa suka shiga ciki.
Can saman hawa na karshe na gidan Abba ashe wani katon hall ne mai zagaye da kujeru da katon tebur gefe guda kuma wani wajene mai Kama da parlor amma girmansa yasa yaci set na kujeru guda hudu sai center carpet kawai a tsakiya da katuwar TV a jikin bango, bayannan sai office din Abba sukenan a hawa na karshen wanda ba kowane yake hawaba dan tun dawowar su Fadima basu taba hawowaba sai dady kawai shima sau daya ya taba hawa. Wannan hall din ko muce parlon Abba yace a bude duk Wanda yakeda ruwa da tsaki da maganar ya hau can saboda ba'aso mutane su rinka interrupting dinsu dan haka duk suka hau bayan sun dawo daga sallar magriba aka bar yan biki suna faman maida magana da har yanzu basu gamaba.
Fadima
A hankali na bude idona, wani sakayau nakejina tamkar idan na tashi iska zata daukeni, kalle kalle na fara na kasa gane a inda nake zuwa can na hango Halifa kan sallaya yana sallah, ido kawai na kafa masa har ya idar ya juyo muka hada ido sannan ya taso da sauri ya taho gaban gadon da nake ya tsugunna tare da kamo hannuna yace "Fadima kin tashi?" Kai na daga masa yace "kiyi hakuri likitan ya taho yana hanya yanzu zaizo kinji?" Kai na kuma dagawa ina mamakin wai menene ya sameni sannan a ina nake? Zuwa can nace "Halifa zanyi fitsari" da sauri ya mike ya dagani wani jiri nakeji sosai dan haka sai daya kamani har bandakin sannan yace "zaki iya ko na kirawo goggo?" Sink din bandakin na dafa dan kar na fadi nace "zan iya" juyawa yayi ya fita ni kuma nayi fitsarin na wanke fuskata, sai dana kammala nazo gaban mirror din bandakin zan goge fuskata da paper towel din wajen sannan na kula da uwar kwalliyar fuskata da bata gama wankuwaba, ido na kurawa kaina a mudubin na wani lokaci sannan kaina ya fara booting: bikina ake da yaya Na'im, ana bikin Saif yazo, naje wajensa kuma shikenan dif komai ya dauke. Ai kuwa da gudu kamar wadda wani karfi yazowa duk da ina fitowa na fadi nayo waje, da sauri Halifa ya taso daga kan sallayar da yake yayo kaina yana tamabaya lafiya? Kafin na bashi amsa goggo da mama suka sake shigowa da sauri suma sukayo kaina fadi suke "subhanallahi Halifa ta farka ne? Me kuma ya faru?" Bakina har rawa yake na katse Halifa daya fara yi musu bayani da cewa "Halifa Saif ya dawo ka ganshi kaima? Ko mafarki nayi? Wannan ma ba gaskiya bane mafarkine ko?" Murmushi yayimin yace "Fadima ki nutsu Saif ne da gaske ya dawo amma ki nutsu kingafa har kina faduwa kinasone kijiwa kanki ciwone" kuka kawai na saka na saka hannu na rufe bakina ina cewa "dama na sani dama na gaya muku bai mutuba yana raye kuma zai dawo gashinan kuma ya dawo din ni dama na sani" Halifa ne shima yana dariya da kuka a hade yace "tabbas Fadima gashinan ya dawo saif ya dawo" cikin kuka na fara kokarin mikewa ina cewa "kaini wajensa kar ya kuma guduwa kar ya kuma tafiya ina da tambayoyin da zan masa ka kaini wajensa dan Allah" da sauri Halifa ya rikeni yace "kinga bazan kaikiba idan dai baki nutsuba yanzu idan kika nutsu sai na kaiki wajen nasa shima yanzu suka tafi sallah dasu dady" kai kawai na kada na fara tattaro duk wata nutsuwata domin inason ganinsa yanzunnan. Dunguma mukayi muka fito sai a lokacin na fahimci ashe dakin Abbane, sama mukayi maimakon kasa amma ban tankaba ina dai rike gam da hannun Halifa for support dan har yanzu ba dan karamin jiri nakejiba.
Muna shiga wajen na tarar da kowa idan nace kowa ina nufin duk wani jinin Abba yana wajen yarane irinsu feena kawai babu sannan da mamansu Abdul dashi Abdul din da maryam da kuma mai gayya mai aiki Saif dina wanda tunda na shigo wajen idona ya sauka a kansa shima ya dago kai muka kafawa juna ido, jana kawai Halifa keyi har muka zauna a kasa daga can gefen su Saif din. Ido na sauke kasa a hankali hawaye na zuba daga ciki sannan Dr ya sauko zuwa gabana ya fara yimin tambayoyi, tun ina bashi amsa har na daina saboda numfashina da nakeja da kyar dan haka ya hakura kawai ya auna jinina sannan yace wa ammie a daukomin magungunan da nake amfani dasu, da sauri ammie taje ta dauko ta hado da ruwa ta bani nasha sannan Dr ya fara yiwa su dady bayani "ba jinintane ya hauba duk da yadan tashi amma ba sosaiba bai kai yadda zai zama matsalaba, kawai dai ta tsoratane a yadda kuma nake tsammani kamar zuciyarta ma na da dan matsala dalilin da yasa da abu ya faru da ita take fara haki kenan ko numfashin Nata ma ya dauke gaba daya amma in sha Allah bayan komai ya natsa akwai abokin aikina likitan zuciyane zanyi masa magana ya dubamana ita sai asan abinyi" kowa a wajen salati ya dauka mama tace "ikon Allah wannan yarinya kinga rayuwa daga hawan jini sai ciwon zuciya? ubangiji ya dubeki ya baki lafiya" duk suka amsa da ameen sannan Dr yace "hajiya karku damu in sha Allah ba wani abune da zai gagaraba dan ko akwai abinda nake zargin baiyi kamariba za'a iya shawo kansa ba matsala" abbie ne wannan karon yace "to Allah yasa ya karemu da lafiya baki daya " duk suka amsa da ameen sannan Dr ya mike yayi waje Halifa ya bishi sannan uncle sagir ma ya bi bayansu daga baya. Ni dai duk abinda ake kaina na kasa sai ajiyar zuciya nake kamar wadda taci uban kuka ko da yake ba laifi nasha kuka kam. Zuwa can Halifa uncle sagir da yaya Na'im suka shigo, sai yanzu na fahimci yaya Na'im baya wajen shima kallonsa kawai nayi shima ya kalleni kowa ya dauke kai amma fa cikin wadannan yan awannin ba karamar rama naga yayiminba duk ya fita hayyacinsa.
Addu'a aka farayi sannan kuma Abba yace "Malama Fatima muna yi muku barka da zuwa Allah yabar zumunci" Mamansu Abdul ce ta amsa da "ameen ya Allah muna Neman afuwar abinda ya faru dazu bamuzo da shirin hargitsa wajenba ayi mana afuwa" da murmushi Abba yace "ayya ba matsala ai mun sani kuma ba laifi akayiba hakan ya zama dole saboda girman mamakin mutumin da duk muka fitar da ran ganinsa ace yau katsahan kawai an ganshi dole muji mamaki mai yawa" shiru yayi kowa na fadin hakane sannan ya cigaba " Saifuddeen munyi matukar farin ciki da dawowarka gida lafiya muna kuma rokon Allah ya kiyaye gaba ya kare mana alummar musulmi baki daya" duk aka amsa da ameen shi kuma Saif ya amsa da "na gode Abba Allah ya kara girma" Abba ne dai ya cigaba da cewa "amma Mal saifuddeeni ina ka shiga shekara da shekaru babu irin neman da ba'ayiba ba'a gankaba? Ina ka buya?" Ajiyar zuciya Saif yayi sannan ya Fara da cewa " ba buya nayiba babu yadda zanyi na dawone babu kuma yadda zanyi na mutu amma ba buya nayiba".

Thoughts and theories.
Comment & like

FadimatuWhere stories live. Discover now