Ranar wata laraba sagir ya shigo gida da safe yayi crossing da Kabir zai fita kasuwa, motarsa ya kalla Kabir ya sayi mota sabuwar yayi sabuwa mai kyau shi kuwa sagir ko babur bashi dashi, girgiza kai kawai yayi ya wuce zuwa dakin abbansu yana shiga ya tarar dashi yana break mamansu kabir na zaune a gefensa, zama shima yayi ya gaisheshi Abba ya amsa sannan yace "Abba dama akwai maganar da nakeson muyi ne idan ba damuwa" kallonsa Abba yayi yace "inajinka" shiru sagir yayi yana susar keya ya rasa ta inda zai fara, jin yayi shiru Abba ya dago ya kalleshi yace "ka fasa maganar ne?" Da sauri ya girgiza kai " aa Abba dama cewa nayi naga na girmi Kabir kuma nima nayi karatu daidai tsahon Wanda yayi shine nace nima yaushe fara zuwa kasuwar" dariya Abba yayi yace "yanzu so kake na kaika kasuwa na doraka akan dukiyata?" Da sauri sagir yace "eh Abba kamar yadda shi Kabir keyiba" dariya Abba ya kuma yi yace "to idan na doraka a dukiyata nace wa na dora? Gidan saida giya ko kuma gidan karuwai?" Karkarwa jikin sagir ya Fara bai taba tsammanin Abba yasan abinda yakeba cike da kunya yace " Abba...." Da sauri ya katseshi "kaga bani da lokacin irin wannan shirmen naka idan kanaso na doraka akan dukiyata to ka nutsu ka zama na Allah, idan nadamarka tayimin sai nayi tunanin abinda zanyi maka tashi ka bani waje" a zuciye sagir yace "to Abba shima Kabir din dakake yabo ai bakasan abinda yakeyiba shima fa yana zuwa gidan giyar kuma sata kawai yake maka a kasuwar yana bushasharsa, gashinan har mota ya saya kuma uwarsa tasan abinda yake amma ni saboda baa haifeniba ni kawai aka Kawo maka gulmar ina shaye shaye ai duk munsan munafukan gidannan wallahi kuma muma...." Abba bai Bari ya karasaba ya kwada masa mari sannan yace " tashi ka fice ka bani waje mutumin banza mutumin wofi" da sauri mama tace "haba Alh yarone banda duka dan Allah" a zuciye sagir ya fito ya shiga kewayen mahaifiyarsa tana hakimce a kan kujera tana ganinsa a wani yanayi ta mike da sauri tana tambayar abinda ya faru, zama yayi a gefenta yana faman huci yace "wai abbane nayi masa magana akan ya kamata nima na fara zuwa kasuwa shine ya Kama fada ta inda take shiga ba tanan yake fitaba har da marina" da sauri umma tace " Mari kuma? Kawai saboda kace kanason zuwa kasuwa shine har da mari?" Yace "to ba wannan munafukar tana gabansaba ai kinsan zai iya abinda yafi hakama algunguma" jin mama na wajen yasa umma mikewa a zuciye tayi dakin Abba sai dai kafin ta isa ta tarar Abban ya fice kasuwa mama kuma ta koma sashenta da ta bita har dakin ta tarar ta shiga wanka dole haka ta karaci rashin mutuncinta ta hakura wai ita an taba mata da.
Haka zaman gidan ya cigaba ada a boye su umma suke nuna kyashinsu amma tun ranar da Abba ya mari sagir suka koma fitowa da shi fili, basa kunyar yin kowanne rashin mutunci ko a gaban waye. To da Ibrahim yayi aure dama a cikin gidan yake zaune tare da matarsa dan haka sai ya zamana matarsa ta zama tamkar wata kawa a wajen Kabir da kubra a gidanta suke shan soyayyarsu, lokacin da ta haihu ta haifi namiji nan suka dau soyayyar duniya suka dora kan yaron mai suna Na'im komai suka samu shi tamkar su suka haifeshi. Na'im tun yana yaro yakewa kowa kiwa idan dai ba Kabir ko kubrabane har iyayensa kuwa saboda dasu ya saba.
Ganin irin soyayyar dake tsakanina da Kabir yasa abbansu yace ya kamata ayi maganar aurenmu hakan ba karamin faranta mana rai yayiba yayinda ya bakantawa sagir, tun kafin na fara soyayya da Kabir sagir ya nunamin yana sona, naso na bashi dama amma ya watsar da ita ta hanyar kokarin tabamin jiki duk sanda muka hadu dan haka nace masa bana sonsa, a lokacin yayi shiru kamar hakan baiyi masa zafiba sai da ya ganni da Kabir sannan ya nemin yimin hauka wai still yana sona ni kuma na watsar da shirmensa saboda ina son kabir. Kasancewar ina makaranta ss1 yasa aka saka bikinmu nan da bayan na gama karatu wato shekaru biyu kenan. Cikin shekaru biyunnan babu abinda sagir beyimin ba akan na rabu da Kabir naki rabuwa dashi kuma duk wannan abin da ake Kabir bai taba sanin sagir na da feeling akainaba, ban taba gaya masaba. Akace abinda duk aka saka masa Rana sai yazo indai da rai da lafiya shekaru biyun da ada muke ganin tamkar baza suzoba gashi har sunzo an fara shirye giryen biki, alokacin Na'im na da shekaru hudu mamanshi kuma bata kuma haihuwaba sai bari da tayi ta jerawa dan a cikin shekaru biyunnan sau uku tana bari. Na'im yayi wayo sosai komai yace Anty da uncle mu kadai ya sani a gidannan muma kuma ba karamin so mukeyi masaba.
Ana saura sati biyu daurin aure sagir ya kirani a waya wai na Kawo masa abincinsa dakinsa shi da abokanansane bazai shigo yaci ba dan haka naje na shirya musu abinci na dauka na nufi dakinsa dake bayan gidan, ina shiga dakin maimakon na tarar dashi da abokansa kamar yadda yace sai na tarar dashi shi kadai, na ajiye abincin kan table din dake dakin ina cewa "ina abokanan naka na ganka kai kadai?" Dariya kawai yayi ga mamakina sai ya cire rigarsa daman jallabiyace kawai a jikinsa da gajeren wando, ina ganin haka namike na nufi hanyar waje da nufin ficewa amma kawai sai ji nayi ya rungumeni ta baya da masifa na fara kokarin kwacewa ina cewa "sagir meye haka banason iskanci wallahi zanyi maka ihu" dariya kawai yake yaki kulani kafin nace wani Abu kawai sai ganin Kabir nayi ya turo kofar dakin nan wani karfi yazomin nayi saurin kwacewa daga rikon da sagir yayimin ina kallon kabir shima ni yake kallo da wani irin yanayi a fuskarsa mai ban tsoro, dauke idonsa yayi daga kaina ya maidasu kan sagir dake wani shegen murmushi sannan yace "haba dan uwa ba'a koya maka idan zaka shiga daki kayi sallamaba ko knocking?" Kabir bai bashi amsaba illa wani naushi daya kai masa shi kuma da alama ya shiryawa hakan dan bai bari ya sameshiba ya kauce yana cigaba da dariya yana cewa "wow dan uwa irin wannan daukan zafi haka? Dama ai na gaya maka kawai ka barmin ita idan ba hakaba kai ka yiwa kanka dan ragowata zaka dauka" wani tashin hankaline ya shigeni na shiga uku me wannan mugun ya shiryane? Ba karamin baci ran Kabir ya kumayiba dan haka ya turmusheshi suka fara kokawa nikan nama rasa abinda zanyi banda ihu, ihunane ya jawo hankalin yan gidan zuwa dakin dakyar aka samu aka rabasu goggo ta jani mukayi waje su kuma abbansu yayi kiransu falonsa, bansan abinda aka tattauna akan maganarba ban kuma saniba sun fadi meya faru ko basu fadaba amma dai tun daga lokacin babu Wanda ya kuma tada maganar har shi kansa Kabir bai kuma yimin maganarba kuma bai kara kulaniba. Ba'a fasa shirin bikiba amma fa ango baya yimin magana koda kuwa zamu bangaji junane nayi iya bakin kokarina ya fuskanceni amma yaki dan haka na kai kararsa wajen Maman Na'im nan ta kirawoshi ta tasamu a gaba tace "banason sainaji abinda ya hadaku amma tunda tace ka bata dama tayi maka bayani me yasa zakaki bata damar ko kuwa ka gwammace ka bawa makiya dama suci riba a kanku? Tun kafin lokaci ya kure muku Ku sasanta kanku kuna gani dai saura kwana goma afara biki dan haka ku sasanta kanku" tana gama fadar haka ta tashi tayi ficewarta ta barmu. Kuka na fara yi amma yayi shiru yaki kulani dan haka na dago kai da niyyar fara magana tunsa shi yaki ya Fara amma sai ya katseni da cewa "basai kinyimin bayaniba nasan komai nasan makirci ya hada bana bukatar bayaninki na yadda dake" ina kuka nace "to idan ka yadda dani me yasa kake fushi" mikewa yayi nima na mike ya zuba hannu a aljihu yace "kawai na kasa cire hotonki a jikinsa daga kainane duk sanda na kalleki abinda nake tunawa kenan shiyasa amma zanyi kokarin cirewa kafin kwana goman" yana gama fada ya fice daga dakin.

ESTÁS LEYENDO
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...