Daga diffa zuwa zinder tafiyace kamar ta yada shege inji hausawa, abin ya bani mamaki yadda har su Rumaisa suke iya zuwa week end gida dan nidai bazan iyaba gaskiya, mun tsaya munci abinci a wani kauye a hanya mukayi sallah sannan muka cigaba da tafiya. Sai wajen magriba mukaje dan haka already makarantar sun tashi nan yaya Na'im ya kaimu wani hotel ya Kama mana dakuna guda biyu shi da Halifa ni kuma ni kadai, har a lokacin basayimin wata magana sosai sannan kuma mun gaji dan haka muna karbar dakuna kowa yayi dakinsa. Ina shiga daki wanka na farayi da ruwa mai zafi sannan nayi sallah sai bacci ko abinci ban tsaya ciba.
Washe gari da sassafe na farka inajin wata mahaukaciyar yunwa dan haka nayi odar abinda zan iya ci sannan nayi wanka ina fitowa naci abinci na shirya na fice ba tare da na jira su halifaba, ai kuwa da yake na fita da wuri kafin wani lokaci na gama komai na karbi hostel na gama komai dan haka na koma hotel din da muka kwana. Ina shiga daki kiran yaya Na'im na shigowa wayata na dauka na gaisheshi sannan yace "ki fito muyi break sai mu shiga makarantar ki fara da wuri dan kiyi saurin gamawa" dariya na fara yace "meye kike dariya?" Da sauri nace "ba komai ganinan fitowa" sai dana gama shirya komai dama ba wani fito da kayana nayiba sannan na fito tare da jakankunana, a bakin kofar dakin na gansu suka tayani da kayan zuwa mota sannan muka sauka restaurant din wajen mukaci abinci, muna cin abincine yaya Na'im yace "yanzu ki Kira su Rumaisa idan basu da lectures sai su zo su nuna miki yadda zakiyi" kallonsa nayi nace "har na gama fa"da mamaki suka hada baki wajen cewa "kin gama me?" Nace "komaima tun 6am na fita dawowata kenan kuka kirani har hostel na karba" gaba daya sakin baki sukayi suna mamaki ni kuma na basar na cigaba da cin abincina kamar ba dani sukeba, da kyar dai a karshe Halifa yace "tab" kawai suma suka cigaba da cin abincinsu.
Bayan mun gama suka kaini har bakin hostel din suka kawomin jakunkunana saboda bazasu iya shiga cikiba, mukayi sallama kowa nayimin addu'a da nasihar na kula da karatu banda kawaye da samarin banza. Ina shiga dakin dake da number 49 kamar yadda takadduna suka nuna, mukulli nasa na budeshi dakine dan madaidaici mai dauke da gadaje irin na yan makaranta guda uku hakan na nufin mu ukune a dakin kenan, gadaje biyu daga ciki da shimfida a Kansu da kayayyaki sai daya babu kaya dan haka shi na dosa na ajiye kayana na koma na dauko ragowar bayan na ajiyesu akan Gado na juyo na karewa dakin kallo, babu wani shirgi a ciki bayan gadajen guda uku sai doguwar loka tun daga kasa har ceiling mai murfi guda uku shikenan sai dan shirgin kowacce a kusa da gadonta. Lokokin babu key a jiki sai guda daya dan haka na yanke hukuncin itace tawa nan na fara unpacking kayana, bayan na gama komai na shimfida bedsheets a gadona na dauko wayata na fara kiran su momy sai ga wata nan ta shigo da sauri tana ganina kuma tayi turus murmushi nayi Mata na mike tsaye tare da mika Mata hannu nace "sunana Fatima Kabir sabuwar yar dakinnan Enchante" nan da nan fuskarta ta fadada ta miko min hannu tare da cewa " ohh Je suis désolé (I'm sorry) sunana Khadija Mahmud enchante" Nan muka fara hira nace "ke yar nan garince?" Tace "aa daga maradi nake kefa" nace "diffa" muna haka watama ta shigo gaba dayansu ba zamu wuce sa'anni ba, tana shigowa itama ta Bini da kallo kamar yadda nayiwa waccan bayani itama haka nayi mata ita kuma tace sunanta amatullah Ahmad daga Tahoua dukkaninsu yan level 1 ne kamar ni sannan su yan medicine ne sabanin ni. Haka mukayi ta hira suna yimin bayanin makarantar da yadda ake komai tare da kwatancen wuraren da ya kamata na sani. Sai dare muka hadu dasu Rumaisa suka kaini har dakinsu da roommate dinsu mai suna Sumayya awajensu naci abinci sai dare na koma dakinmu.
Washe gari da wuri na tashi na shirya naje cafeteria naci abinci sannan na nemi class din da zanyi first lecture dina. Wayata na dauko bayan na zauna a class ina jiran lokaci ya karasa, labari nake bawa Saif how excited I am zan fara lectures nima kamar yadda yake buri ada, ina cikin typing naji an zauna kujerar kusa dani dan haka na dago Kai na kalli Wanda ya zauna din, wani gayene wanda ina kallonsa sai da zuciyata ta buga saboda tsabar kyansa komai yaji a fuskarnan kamar shi yayi kansa murmushi yayimin bansan sanda nima na maida masaba yace "sannu fa sunana Aliyu kefa?" Sai da kyar na iya kwakulo sauti daga makogarona nace "Fadima, Fadima Kabir" murmushi yayi yace "wow nice name" da mamaki nace "ka iya turanci?" Ya daga kai kawai ya cigaba da fito da littattafan da yake daga backpack dinsa, bai sakemin maganaba nima haka har lecturer din ya shigo muka gama ya tafi wani ya shigo, har 1 muna class sai a lokacin muka fito direct cafeteria na wuce dan yunwa nakeji bayan na karbo abincina na faraci yaya Na'im ya kirani na daga muka gaisa muka fara hira wai kirana yayi na bashi labarin yadda first day dina ta kasance, muna cikin magana naji daga bayana ance "zan iya zama anan?" Da sauri na juya na kalli me tambayar aliyune na dazu murmushi nayi masa nace "bismillah zauna" kafin na gama rufe baki yaya Na'im yace "waye wannan din?" Nace "wani dan ajinmune" ai kuwa a zuciye yace "ke yanzu Fadima har kinyi sabon da zaki zauna cin abinci da namiji daga zuwanki makarantar? Me nace miki akan kula maza? Kinaso nazo har nan na nuna miki bacin raina ko?" Da mamakin fadan da yake nace "haba yaya Na'im ba wani bane fa kawai mun hadu a class ne yanzuma muka kuma haduwa dan munyi magana sai ya zama laifi? Yanzu yaya mutum zaice zai zauna a kusadani na hanashi? Kai dan Allah?" Sai kuma yayi kasa da murya "bazaki gane bane Fadima banasonki da shiga harkar maza yan garinnan yan yaudarane na ajin karshe" dariya nayi nace "ka kwantar da hankalinka na gaya maka hakan bazai taba faruwaba in sha Allah karka wani damu indai nice nan gani nan bari" muryarsa da murmushi ba kamar ta dazuba yace "to yanzu kiyi sauri ki karasacin abincinki ina zaki idan kin gama?" Nace "daki zan koma inaso na duba course outline dina saboda na fara karatu da wuri" yace "yauwa maza ki karasa ki koma daki Zan kiraki an jima kinji?" Nace "ok bye " shima yace "bye" sannan na kashe wayar na ajiye akan tebur din dake gabana, mutumina na kalla abincinsa kawai yakeci tamkar bai fahimci akanshi muke maganaba dan haka nima na koma kan abincina ba tare da nayi masa maganaba, zuwa can naji ance "mijinkine?" Da sauri na dago har na kalleshi har yanzu baya kallona na waiga banga kowa a kusa daniba dan haka nace maybe ba dani akeba na cigaba da abinda nake, kai ya dago yace "bakijine?" Kallonsa nima nayi nace "a iya saniba idan ana magana da mutane kallonsu ake a darajasu ba a dauke kai sannan ace za'ayi magana dasuba" hannu ya daga sama alamar surrender yace "Allah ya baki hakuri banaso na kallekine naje matar aurece shiyasa" dauke kai nayi bayan nace "yayanane" sannan na fara hada kayana na mike da sauri shima ya mike yana cewa "badai na takura mikiba shine zaki tafi Bari na canja waje ki zauna ki cigaba da cin abincinki" nace "no ba takuramin kayiba dama na gama wucewa zanyi kayi zamanka" na dau jakata na Goya sannan nace "sai anjima" shima yace "sai anjima" nayi wucewata zuwa daki.
Haka rayuwata ta cigaba da kasancewa a Abdou Moumouni University kullum zan bawa Saif labarin abinda ya faru yayinda Na'im zai kirani yace na bashi labari. A hankali muka fara sabawa da Aliyu shi ya zama friend dina kullum muna tare a class sai idan na dawo daki muna tare dasu Rumaisa, ranar da Halifa zai tafi China ta airport din zinder ya tashi dan haka sai dana rakashi har sai da suka tashi muna tare, bayan tafiyarsu kuma muka shiga gari dasu momy da suka rakoshi nayi sayayyar abinda nake bukata muka kuma shakata. Watana biyu a makaranta na tafi gida week end tare dasu Rumaisa ai kuwa naji dadin zuwan nawa saboda inason yan uwana sosai gashi munyi sa'a Tj ma yazo gida suna Hutu. Tun da naje gida kullum zamuyi waya da Aliyu zai gayamin yadda ake ciki a ecole kuma wani ikon Allah duk sanda zai kirani muna tare da Na'im ranar lahadi kuwa muna zaune a garden muna hira wayata tana hannunsa kawai akai kirana, da sauri na dago da niyyar ya mikomin amma sai naga ya kafawa screen din ido ransa a hade har wani huci yake, har wayar ta katse bai baniba aka sake kira ganin yanzuma bazai baniba nace "yaya Na'im kirana fa ake" ai kuwa kamar na kunnashi yace "ai nasan kiran naki ake ina da ido ba bani dashiba menene wai hadinki da wannan Aliyun? Wayeshi da zaiyi ta kiranki? Fadima me nace miki akan samari?" Da mamaki nake kallonsa nace "yaya Na'im na gaya maka coursemate dinane kawai babu abinda ke tsakanina dashi sai harkar karatu" yace "to meyasa kullum sai ya kiraki? Yanzu menene dalilin da yake kiranki" nace " shekaran jiya da kaga ya kirani Kira yayi yaji yadda nazo gida sannan akwai assignment dina dana bashi yayimin submitting tare da nasa shine yace malamin yaki karba yace sai na Kawo da kaina yau kuma nace masa yau zan dawo maybe yana kira yaji ko na dawone" still ransa a bace yace "to dolene sai ya kiraki ya gaya miki ya bari idan kin koma kun hadu ya gaya miki mana? Sannan jiya fa menene dalilin kiran jiya ai jiyama ya kiraki" na fara zuciya kuma nima dan haka nace "wai kajika yaya Na'im da wata magana komai nayi sai ka sani? Akwai privacy fa a rayuwa ba komaine zan gaya makaba" ai kuwa ya mike tsaye kamar zai bigeni yace "wato ban isa na hanaki kula samariba ko? Ban isaba ko Fadima?" Ina daga zaunan nace "yaya Na'im bafa aurena kakeba balle kace kai yayanane kawai bai kamata kana shiga irin wannan ba idan soyayyar ma muke ai wannan overreacting kake" Yace "ba aurenki nakeba amma ina fatan auren naki dan haka dole nayi abinda yafi overacting ma" a firgice na mike tsaye ina kallonsa shima ni yake kallo sai kuma yayi saurin juyamin baya yana cewa "ohh shit" a hankali nace "mene kace Na'im?"

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...