Chapter 15

87 7 0
                                    

Bayan na gama bashi labarin rayuwarmu kaf yayi shiru zuwa can yayi gyaran murya yace "Fatima naji duk abinda Kikace na kuma tausaya muku a shekarunku ba karamar jarabawa kuka ganiba ina kuma rokon Allah ya bawa su dady lafiya yasa karshen wahalar kenan" na amsa da "ameen" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba "Fatima ina neman wata alfarma a wajenku ke da Halifa dasu momy baki daya, inason na zama tamkar Halifa a gidannan na zama dan uwanku na jini zan samu?" "Ba zaka samuba" da sauri muka kalli wajen gaba dayanmu halifane a tsaye bakin kofa yana wani muzurai, murmushi saif yayi sannan yace "me yasa?" Yana karasa shigowa yace "kamar yadda kace something is telling you you have a role to play a rayuwarmu haka nima something is telling me you are not good to my family ban yadda da kaiba" da murmushi kamar kullum a fuskar saif yace " saboda me?" Direct ya bashi amsa "saboda bakayiminba, da fari ka kade fadima kaji mata jiyo sannan yanzu kana bugun cikin feena dan ka sami information to idanma aikoka akai ka gayawa Wanda ya aikokan bamu da komai da zai iya damfara yanzu" yana gama fada yayi hanyar cikin gida da sauri na tare masa hanya ina fadin "Halifa ka tsaya yayi bayani bakasaniba ko yana da abin fada" wani mugun kallo yayimin "don't let him manipulate you Fadima bashi da wani abin fada" da sauri saif yace "wallahi Halifa ba da gangan na kade fadimaba ina cikin tafiya kawai ta fito daga wani loko da gudu ta hau titin nayi iya kacin kokarina amma sai da na sameta, sannan jiya ba bugun cikin feena nayiba kawai tambayarta nayi ina abbanta shine tace bashi da lafiya nace meya sameshi tace baya iya tafiya ko hannunsa baya iya dagawa, nace to ina momynta tace idan naje wajen momyma batasanniba itama momy ta mantata  shine fa na fahimci abinda yake damunsu ba wai bugun cikinta nayiba" kallonsa kawai Halifa yayi yace "to meye naka na tambayar momy da dadyn idan ba bugun cikinta kakesonyiba?" "Nasan idan na nemi yin magana daku bazaku saurareniba dama asali kai kaki fuskantata itama fatiman tace kar na kuma zuwa shiyasa nakeson su na gaishesu na kuma nemi izininsu yadda koda nazo Ku bazaku iya korataba" cike da gajiya da maganar nace "to wai kai meye naka na dole sai ka kulamu? Nace maka na warke babu ragowar ciwo a jikina then what?" Tamkar a kotu alkali da mai laifi haka yake bamu amsa "nima ban saniba" ya bani amsa tare da dage kafada, nikam nama rasa mezanyi dan haushi kawai na juya na shige cikin gida shima Halifa ya biyoni.
Samusan me ya faruba kwana biyu dai saif baizoba, har na fara murna ya hakura da shiga rayuwarmu kawai rannan sai gashi ya dawo kamar daga sama, da Halifa suka hadu bansan me sukayiba naga dai ya shigo dashi ina kitchen suka zauna kan tabarmar da nake zaune a tsakar gida gashi ko hijabi babu a jikina Riga da siket nema na saka irin na jeans dinnnan dan haka babu yadda za'ai na fita a haka, Halifa na Kira daga kitchen din yana shigowa cike da masifa nace " wannan wanne irin wulakancine zaka shigo dashi har nan alhalin kasan kayan dake jikina? Me ma yazoyi nayi zaton yayi zuciya" yana kallona yace "to ninasan menene a jikinki? Yazone wai mu bashi chance shine nace mu bashi chance din amma da sharadi... bari na dauko miki hijabin" ya juya zai fita nayi saurin rikoshi "meye sharadin da ka gaya Masan" yace "ai banma gaya Masan ba ki fito Bari na dauko miki" ya juya ya fice, can ya mikomin daga bakin kofa sannan na saka na biyoshi zuwa tsakar gidan.
Ga mamakina biro da takadda Halifa ya dauko wai contract za'a rubuta duk Wanda ya karya shi yaci amana, bayan mun zauna Halifa ya Fara rubuta dokokin yana fada " na farko yaya da kanne kawai babu maganar soyayya tsakaninka da kannena, sannan karkaji mun yadda ka zama yayanmu kace zaka rinka tabamin kanne babu Kai babu su, na uku..." Hannu saif ya daga masa " kaga nasan dokokin naka duk akan kannenka zasu kare to banzo danna cutar nasuba nima kannenane yanzu sai dai na tattare hannun riga mu kara da Wanda zai cucesu ka gane?" Kai Halifa ya daga sannan ya cigaba "karka sake kayiwa momy kallon mahaukaciya dan ba hauka takeba za kuma ta warke nan ba da jimawaba sannan tana warkewa zatayi maka kafa ni na sani" dariya saif yayi yace "ka sani ko idan momyn ma ta warke tafi sona akanka? Aikuwa da sai na gaya Mata duk wahalar da ka bani" a zuciye Halifa yace "never wallahi momy tawace ko Fadima tasan na fita fada a wajen momy balle kai" dariya nayi nace "kai kam Halifa tempern kace zata rinka kadakai a abu wallahi ji shi dariya yake amma kai ka zuciya" sai kuma shima ya saka dariya. Haka dai Halifa yayi ta kafa dokokinsa sai bayan ya gama saif yace duk ya yadda sannan muka kaishi ya gaishe da dady da momy, mukayiwa dady bayaninsa sannan shima ya bashi amanarmu, momy kuwa kallonsa kawai take tunda ya shigo sai can tace "momy" nace "naam" tace "waye wannan?" Ina dariyar ta fara iya hada maganar da tayi making sense na matsa kusa da ita nace "kinga wannan ko sunanshi saif yayanane kamar Halifa yayan halifane kinji? Zai rinka zuwa gidannan yanzu karkiji tsoronsa babu abinda zaiyi miki" kai kawai ta daga still tana kallonsa tace "saif?" Yace "naam momy" sai kuma tayi dariya ta sunkuyar da kai.
Saif yayi murmushi mai sauti bayan mun fito daga wajen su dady yace " wallahi Halifa har yanzu kai yarone to duk wadannan dokokin idan na karya yaza'ayi dani?" Shima murmushin yayi yace " ai shiyasa na rubuta saboda idan ka karya ko dayane ba zaka kuma zuwa gidannanba idan kuwa ka zo da yan sanda zan hadaka " saif yace "to amma ko cikakken sunana baka saniba da yaya zaka hadani da yan sanda?" Sai kuma duk mukayi shiru muna kallonsa, murmushi ya kuma sannan ya zauna akan tabarmar da muka tashi muma muka zauna yafara bamu labarinsa " da farko sunana saifuddeen Abdullahi ringim babana Abdullahi Musa ringim ya rasu tun kafin a haifeni mahaifiyata itama ta rasu a ranar data haifeni dan haka na taso maraya gaba da baya, mu biyar iyayena suka Haifa babbar yayarmu Fatima itace ta rikeni bayan mutuwar mamana lokacin tayi aure itama ta haihu dan haka ita ta shayar dani tare da danta Abdullahi, bayan ita sai Kamaluddeen, Shamsuddeen, Nuraddeen sai ni Saifuddeen. Akwai tazara sosai tsakanina da su yaya Nuru dan haka su a lokacin sun riga da sunyi wayo. Na taso bansan menene maraiciba yaya Fatima da mijinta sun rikeni tare da yayansu cikin amana babu banbanci har zuwa yau, nayi primary da secondary tare da Abdul bayan munyi candy na tafi NDA yayinda shi kuma ya tafi BUK wannan ne sanadin rabuwar karatunmu amma haryau muna tare tamkar twins, Abdul ya karanci business admin. Yayinda na zama soldier a bangaren air force yanzu ina da mukamin captain a air force dake Kaduna kuma ina lecturing a NDA dake kadunan yanzuma Hutu nazo, banyi aureba kuma bani da budurwa haka Abdul ma, watarana ma zan kawo mukushi amma shi miskiline ni kadai yakewa magana" baki na rife ina dariya ya kalleni "meye kike dariya kuma?" nace " kawai na hasko surutunka sannan kana abota da miskili ya abotar taku zata kasance?" Shima dariya yayi yace "idan muna tare ai raba halin mukeyi shi ya Fara magana ni kuma na rage magana sai mu dai daita" na jinjina kai, Halifa na kalla naga ya kafa masa ido ko kiftawa bayayi na taba hannunsa ina cewa "Halifa" sai kuma yayi firgigit kamar ya farka a bacci sannan ya mutstsike ido yace "wai dama duk iskancinnan da nake air force captain nakewa? Fadima me yasa baki hananiba?" Ina dariyar yadda yakeyi nace "ta yaya Zan hanaka bayan kace a hakanma goyon bayansa make?" Yace "eh da yayi fushi ya hawo jirgi ya tashi gidanmu a aiki ai kinga kya goyamin baya mu tafi lahira ko?" Mu dai dariya muke masa, saif yace "wai tsoron force kakeji?" Ya wani marairaice fuska "ai baku fiya imani bane idan kuka zuciya shiyasa" muka kuma kwashewa da dariya yace "kasan kuwa rannan na zuciyan Allah ne kawai ya taimakeku" da sauri Halifa yace "yaushe" nan da nan ya hade rai ni kaina saida na tsorata na daina dariyar da nake gashi kuma ni yake kallo yace "ranar da Fatima ta mari feena, sai da naji kamar na rama mata wallahi raina ya baci sosaida kyar na iya controlling kaina, karki kuma dan ayanzu da nake yayanta Zan rama matane kin gane?" Kai kawai na daga masa sai kuma ya saki fuska, haka mukayi ta hirarmu har safeena ta dawo daga school sannan ya tafi gida.

Saif
Bansan me yake damunaba abinsa kawai na Sani shine ba karamin so nakewa Fadima ba, ada naki yadda da sonta nake ina ganin kamar tausayintane kawai sai daga baya na hakura na yadda sonta nake, nasan idan na nuna musu soyayyace a raina bazasu dauki abin nawa serious ba shiyasa naje musu a matsayin yaya sai sun saba dani yadda bazasu iya rabuwa daniba kafin na nuna soyayyata saboda sunsha wahalar rayuwa ina nuna sonta nake zasu yi zaton nazo cutarsune, ayau da suka yadda dani ba karamin farin ciki nake cikiba tabbas burina ya kusa cika. Ina fitowa daga gidansu na kira Abdul a waya yana dagawa na saka ihu sai da nayi mai isata sannan yace "dadina dakai banzane wallahi ihun me kake kana neman ciremin kunne?" Ina dariyar nace kana ina" yace "zahra" nace "yauwa ganinan labarin bazaiyiyu a wayaba" ina gama fada na kashe wayar tare da juya kan motata zuwa zahra store babban shopping mall da Abdul ya bude na yan zamani.
Ina shiga store din direct office din manager na nufa, yana zaune kan kujerarsa yana kallo a labtop din gabansa, na zauna ina cewa "manager guda da kallo a office?" Yace "to ya zanyi na gama abinda zanyi har na tashi zan fita kace gakanan baka tsaya nayi maka bayaniba ka kashe wayarka kaga dole na tsaya jira" ban tanka doguwar mitarsa ba kawai na Fara bashi labarin Fadima da irin son da nake mata tsayawa kawai yayi yana kallona har na gama ga mamakina kawai sai yayi tsaki ya fara hada kayansa yana zubawa a jaka, da sauri nace "Abdul wanne wulakanci kenan ina maka magana kana yi min tsaki?" A zuciye yace "ba dole nayi maka tsakiba akan wata banzar soyayya ka zauna yara kanana suna bata maka rai suna raina maka hankali? Karyane fa babu wani abu waishi soyayya kawai abune irin naku da shegen kallon finafinan turawa sun jefa muku wata banzar akida kuna ta wahalar da kanku" da sauri nace "karkayi sabo Abdul kai kasan soyayya a musulunci aka sameta ba a wajen turawaba ko ka manta soyayyar annabawa da matayensu? Mallam love really exis and I'm in love" na fada ina dariya tare da rungumeshi shi kuma ya tureni tare da rataya jakarsa yayi waje, da sauri na bishi ina "haba aboki dan uwa rabin jiki ka tsaya ka fahimceni mana".

FadimatuWhere stories live. Discover now