👩👩👦👦👩👩👦👦 Fadimatu 👩👩👦👦👩👩👦👦
Epi 3 and 4
By
Ummu saifAlokacin da Halifa ya fadi haka ba karamin tashi hankalinta yayiba bawai dan su dady zasuga tayi dakikanciba ba kuma dan yana fushiba sai dan yace zai gayawa dady ya maidasu Nigeria alhalin anyi mata alkawarkin nan da sati biyu su Lee min ho zasuyi wani concept a jeju island dan haka za'a kaita har wajensa su gaisa dan har ticket ta siya tuntuni wannan shi ya matukar tayarwa da Fadima hankali kamar zatayi hauka haka ta rinka bashi hakuri tana kuka kamar wadda aka yiwa mutuwa, kin kulata Halifa yayi dan yasan komawa Nigeria shine babban gatan da zaiyi Mata a matsayinsa na dan uwanta. Ganin da gaske Halifa yake sai Fadima ta fara blackmailing dinsa ta hanyar daina cin abinci ta daina zuwa ko Ina kullum tana kwance a daki class dinma ta daina zuwa a karshe dai sai da aka dangana da ita da clinic ai kuwa ba karamin tashi hankalin Halifa yayiba yana ganin duk shine ya janyo yanzu ga sister din nasa kwance a asibiti a dalilin taurin kai irin nasa yana ganin kawai zai hakura ya kyaletane su cigaba da zama a kasar amma duk hanyar da zaibi ya hanata mu'amala da lee yoo shing zaibi danshi yake kuma zigata dan haka dole ne su rabu ko kuma ta koma Nigeria ko me zatayi, bayan ta farka baccin da take (da yake sun Mata allurar baccine) yayi ta bata hakuri da cewa in sha Allah bazai bari a maidasu gidaba idan har tayi alkawarin ba ita ba lee yoo shing sannan ba wani celebrity ai kuwa tayi alkawarin tace ba zata kuma zuwa kallon waniba ba kuma zata kuma bin yoo shing ko inaba.
A ranar da aka turawa dady result din su Fadima ta email(kamar yadda dokar makarantar take) ba karamin baking ciki yayiba ransa ya baci matukar amma sai yayi kamar baisaniba sai kawai ganinsa sukayi a school din ta taho da murnarta zata rungumeshi kawai sai jin saukar mari tayi Tass! Ai kuwa sai da takai har kasa, jikin Halifa na rawa ya dagota ta shide tana kuka sosai ai kuwa dady ya fara fada kamar zai ari baki ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba "wato kinason ki gayamin cewar asarar kudina nayi Dana daukoki uwa duniya na kawoki nan KO? Zancen momynku ya tabbata ba karatunne a gabankiba wata manufa can gareki ta zuwa nan din, Su da suke rawa da wakar an gaya miki jahilaine? To kowannensu da kwalinsa a ajiye sun San me suke sai ke shashasha zaki ajiye naki karatun akan wasu banzaye da basusan kinayiba, kina kallon dan uwanki saukowar da yayi is reasonable dama dole ya sauko tunda an canja makaranta an canja yare amma ke kam iskancine kawai a kanki kuma gani nazo zan cire mikishi yanzu basai anjima ba ki shiga hostel ki hado kayanki gida zamu koma sai Inga ta karyar iskanci shashasha kawai" haka dady yayita fada ita kuwa mutuniyar ta lafe jikin Halifa sai ajiyar zuciya take(su fadimatu anji maza) bayan ya gama fadansa yace ta shirya gobe zai koma Nigeria kuma da ita zai koma.
Bayan tafiyar dady ta tasa Halifa a gaba da kuka yanzu kam ta saddakar bata damu da sai ta zauna acanba a'a tsoro takeji idan har dady zai fusata haka to yaya momy zata zama ita da dama can ba san zuwan nasu takeyiba sannan momy tafi dady zuciya ba kadanba ta fishi saurin hannu musamman akan ita fadiman, nan dai suka zauna suna tunanin yadda za'ayi yadda zasu shawo kan dady ya hakura da tafiyar da ita, sai dare dady ya dawo daukansu yayi da yake da motar hotel din da ya sauka yazo suka tafi wani restaurant bayan sun gama order abinda zasuci Fadima ta tashi daga kujerar da take ta durkusa a kasa hawaye na zuba a idon sannan ta fara bawa dady hakuri "dady dan girman Allah kayi hakuri nasan nayi laifi na kuma karbi laifina and I have no excuse but dady please dan Allah ka yafe min wallahi dady I promise you wallahi ko kuma ganin wani celebrity nayi ko kallonsa bazanyi ba, dady plss karka mai dani gida idan naje momy zaka kashenine zatayi fushi dani sosai please dady" akace tsakanin da da mahaifi sai Allah yadda take kuka da sheshsheka sai ta bashi tausayi ya kamo hannunta ya zaunar kan kujerar da ta tashi sannan yace "shikenan na yadda zan hakura amma da sharadi zaki maimaita wannan shekarar as a punishment sannan idan har next session bakiyi abin arzikiba ko kuma naji labarin kin kuma bin wani wani wajen to wallahi Nigeria zaki koma kuma idan muka koma din sai kin dawo daga jss1 kin yadda" shiru tayi tana weighing maganar dadyn wanne zata dauka ta koma Nigerian ko kuwa tayi asarar shekara daya? Har aka Kawo musu abincin suka gama ci batayi making decision ba. A karshe dai bayan dady ya dawo dasu school tace ta yadda tayi asarar shekara guda din. Nan dai dady yayi tayi musu nasihohi akan rayuwar duniya bata da tabbas Yau ne gareka gobe ga dan uwanka dan Allah ya hore masa arziki hakan baya nufin zaiyi ta zama dashi har karshen rayuwarsa idan ma shi har ya mutu yana da arzikin hakan baya nufin bayan mutuwarsa dole su zauna da arzikinsu rayuwa tana juyawa page page ne. Bayan ya gama yi musu fadan dai ya basu abinda zai basu ya siya musu abinda zai siya musu washe gari ya juyo Nigeria. Wannan shine dalilin da yasa Halifa ya Riga Fadima candy,
Alhmdulillah an sami ci gaba sosai akan Fadima tun daga kashedin da dady yayi Mata bata kuma zuwa kallon wani celebrity ba sai dai a waya ko ta kalli film amma bata kuma komawa kallonsuba, result din wani session din kuwa sai gashi ta fito a ta biyar da 85% average dama iskanci ya hanata, kuma hakan ba karamin dadi ya yiwa dady da Halifa ba dan haka suka kjma zagewa wajen nuna Mata gata sosai. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Halifa ya kammala high school dinsa inda Fadima ke da sauran ahekara daya sai a wannan lokacin sannnan sukazo Nigeria tun bayan tafiyarsu.
💓💓💓💓💓. 💓💓💓💓💓 💓💓💓💓💓
Sunyi murna sosai finally dai gasu a gida tare da yar kanwarsu wadda itama yanzu har tayi wayo tana surutu kamar me halinsu da komai iri daya da Fadima har zuciyar ga uwai kiwa indai kai ba dan gidansu bane to bazata taba kulaka ba, ba kuma zatazo wajenkaba. To dayake su Fadima sun Fara hankali yanzu sai rashin dangi ya fara damunsu suka Fara tambayar Kansu wai Ina damginsu suke Ina yan uwan momy Ina na dady? Su basu da aunties ba uncles haka suke dan haka suka had a plan na zasuje su tuntubi momy suji yadda aka kwana a ragaya dan haka da yamma suka nufi dakin momy sukayi sallama bata amsaba dan haka suka tura kofar a bakin gado suka hangota zaune ta zuba uban tagumi idonta na kallon kasa har sukaje suka zauna both sides nata bata saniba saida Fadima ta janye mata tagumin sannan ta dago a firgice tana kallonsu a hankali kuma ta sauke ajiyar zuciya tana kakaro murmushi sannan tace " ya dai yaran momy menene" Fadima da gaba data hankalinta ya gama tashi tace "momy lafiya? Meya faru? Tunanin me kikeyi haka" murmushin karfin hali tayi tana cewa "ba komai Fadima kawai Ina tunanin rayuwane ba abinda ya faru" surin girgiza kai Halifa yayi yana cewa "no momy dole akwai wani abin nifa dama tunda muka dawo na fahimci kamar akwai abinda yake faruwa dan Allah momy ki fada mana idan baku fada mana damuwarkuba momy wa zaku fadawa bamu da kowa sai ku haka kuma baku da kowa sai mu please momy" nan da nan hawaye ya ciko idon momy tasa hannu tana sharewa tace "kunga na gaya muku babu komai ba abinda ya faru ni bacci ma nakeji" ta gama fada tana kwanciya a kan gadon tare da lunshe idonta, haka suka karaci kallonta suka tashi suka fita ko abinda sukazo tambayar ma basu samu sun tambaya ba. Bayan sun koma daki babu irin hasashen da basuyiba to ko fada sukayi da dady? Halifa yace "kai ba haka bane sanda dady zai fita da safe ita ta rakashi kuma babu alamun sunyi fada" to ko kuma family din nata ta tuna tayi missing dinsu? amma idan hakane me yasa bazataje wajensuba to ko bata da sune gaba daya? Kai amma ai babu Wanda yake fadowa daga sama dole kowa yana da family. Haka dai suka wuni suna juya maganar amma basu sami answer ba .
![](https://img.wattpad.com/cover/200632659-288-k157333.jpg)
ESTÁS LEYENDO
Fadimatu
FanficLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...