Chapter 48

83 4 0
                                    


Na'im
Kuka Fadima take sosai sanda tabar parlon Abba har inajin kamar na bita na rarrasheta sai dai bazan iyaba, Abba ne ya katsemin tunani ta hanyar cewa su dady "to kune iyayensu sai ku yanke hukunci" shiru kowa yayi, jin babu mai shirin magana yasa Saif yin gyaran murya yace "amm Abba kuyi hakuri amma ina ganin Na'im ya kamata a barwa fatima saboda ni na riga da na hakura kuma itama yanzu shi take so ba niba idan akace za'a bani ba'ayi musu adalciba duk su biyun, sannan dady kullum fatima na fadamin bazatayi aure tabarkuba dalilin da yasa taki yadda da maganar aurena kenan tun kuna kano saboda zan tafi Kaduna da ita inaga na dauketa tun daga Niger zuwa kano? Dady farin cikinta nake bukata bawai dole sai na auretaba kuma na tabbatar zatafi farin ciki da Na'im a kaina dan haka ina rokonku dan Allah dan annabi karku saurari Na'im ku cigaba da shirin daura musu aure kamar yadda kuka fara, idan aka fasa wannnan hadin bazan taba jin dadiba bazan yafewa kaina wargaza musu farin ciki da nayiba" shiru kowa yayi na wani lokaci kowa na processing abinda yace sai can sannan Abbie yace "shikenan idan kowa ya yadda sai muyi fatan alkhairi" kai kowa ya kada bandani, bansan meyasaba kawai banajin wannan auren zai haifar da da mai ido, son da Fadima keyiwa Saif yafi Wanda takeyimin, sannan shima ba dan karamin so yake mataba ina ganin kamar banyi musu adalciba idan na rabasu, amma babu yadda zanyi haka nabi ayari akayi addu'o'i aka shafa sannan muka taso muka fito. Bayan munje munyi sallar isha'in da akayi tun dazu, muna shigowa hamida ta fito tana cewa Halifa wai an rasa Fadima sun duba ko ina batanan. Hankalinmu ya tashi matuka bata tafi da wayartaba dan haka idan mun kirama bama samunta wayar na hannun hamidan, kaf gidan babu inda bamu dubaba hatta da incomplete gidajensu Yusuf sai da muka duba amma batanan, haka mukayi ta nema har 12 na dare sannan muka fice waje dan dubawa ko waje ta fita. Ni da Saif muka shiga mota daya Wanda sai da muka fitama na fahimci ni dashine a ciki, munyi nema har mun gaji amma babu ita, ganin yadda hankalinsa ya mugun tashi sai na sami kaina da cigaba da zargin kaina da aikata rashin adalci, sai wajen 1 sannan Halifa ya kiramu wai ta dawo nan muka juya gida muna zuwa muka fara tambayarta inda taje tare da duba lafiyarta, zamewa Saif yayi ya fice na fahimci hakanne ta dalilin ganin da nayi tana kallon bayana ni kuma na juya na niyyar ganin abinda take kallo, inuwarsa kawai na gani amma na ganeshi kuma nasan babu Wanda zata bi da wannan kallon idanba shiba. Bayan ta shiga gida nima na wuce gidan Halifa inda aka sauki maza, bayan nayi wanka na shirya kwanciya sai na tuna na manta agogona a falon gidan Abba na kasa, tashi nayi da niyyar daukowa dan kar gari ya waye wani ya dauke. Ina zuwa bakin kofa da niyyar fita naji maganar da Fadima da Saif sukeyi, tsayawa nayi naji na kuma tabbatar da har yanzu Saif nason Fadima ya dannene kawai saboda koyi da hadisinnan na manzo mai cewa kasowa dan uwanka abinda ka sowa kanka, to idan hakane ni meyasa bazanyi koyi da hadisinba? Kukan Saif ba karamin ciwo yayiminba saboda ina jinsa kamar dan uwana na jini, nasan kuma zai cigaba da kukan har karshen rayuwarsa.
Daki kawai na koma ba tare da nayi abinda na fita da niyyaryiba, a ranar kwana nayi ina tunanin abinda ya kamata nayi, banyi bacciba kuwa sai da na yanke shawarar abinda ya kamata nayi. Washe gari muna dawowa daga sallar asuba na tare Abba a hanya, bayan mun gaisa nace "Abba dama magana nakeson muyi" kallona yayi a tsanake sannan ya kama hannuna muka shiga cikin gidansa har parlonsa muka zauna sannan yace "ina jinka Na'im" shiru nayi na wani lokaci sannan nace "Abba akan hukuncin da aka yankene, Abba kamar yadda na fada da farko na fasa auren Fadima bazan iyaba, banyi musu adalciba Fadima tafi son Saif a kaina sannan shima son da yake Mata ba dan kadan bane, dukda bazance yafiniba amma fa ba karamin so yake mataba, Abba anan ya nuna muku ya hakura ya barmin amma wallahi Abba jiya kusan kwana yayi yana kuka da fari na kamasu sunayi tare da fadiman daga baya kuma na jishi ya kulle kansa a toilet shima yana kuka. Abba bazan iyaba, idan na auretama bazamu taba jin dadin aurenaba" shiru nayi ina maida nima nawa hawayen dan ba karamin zafi kirjina keyiba. Ajiyar zuciya abba yayi sannan yace "amma an riga da an yanke hukunci banason mu dawo da hannun agogo baya" hawayen da ya zubomin na goge da sauri dan karya gani nace "Abba na yanke hukunci kawai ka nemamin auren maryam kanwar Abdul" shiru Abba yayi yana kallona sai can yace "idan bata sonkafa? Idan kuma tana da Wanda takesofa? Babu iyayenta ta yaya za'ayi mu nemi aurenta? Kana ganin zaka iya zama da wadda bakaso alhalin kana da ciwon rabuwa da wadda kakeso? Abin fa da walaha Na'im karka dorawa kanka abinda bazaka iyaba" shiru nayi na wani lokaci ina faman hadiyar zuciya tare da juya maganar da abba yayi, tabbas duk abinda ya fada abin a dubane kuma abune mai wahala amma dai na daure na dago kai na kalleshi da kwarin gwiwata nace "abba zan iya indai zata yadda dani indai zata aureni zan zauna da ita iyaye kuma ba lallai ayi auren yanzuba zan iya binta na nemi aurenta kamar yadda akewa kowacce mace, idan kuma yau dinne akwai Abdul zai iya karbar aurenta ni dai kawai a nemamin auren nata" ajiyar zuciya abba yayi yace "shikenan zanyiwa iyayen naka magana zakaji yadda muka yanke" godiya nayi na tashi na fito wani barin na zuciyata na gayamin nayi dai dai yayinda wani barin ke min fadan nayi wauta ba kadanba kuma zanyi Dana sani wadda banajin zanyin.
Bansan yadda akayiba nidai abba bai kiraniba har akazo daurin aure idan naje wajensa sai yace yana zuwa nima kuma abokaina suka hauni na zama busy dan haka baiyimin bayaniba nidai kawai naji ana daurin aurena da maryam Fadima kuma da Saif. Wani kallo Halifa ya tsaya yanayimin cikin shock ni kuma na maze na cigaba da harkata ban bashi damar da zaiyimin wata tambayaba har muka gama abinda zamuyi muka tafi reception. Wani barin na zuciyata na farin ciki na tabbatuwar farin cikin Fadima yayinda wuta keci a dayan barin domin nasan narasata har abada, ban taba yiwa wani abu son da nakewa fadimaba kuma ban taba neman abu na rasaba sai a kanta, amma na sakawa zuciyata na hakura da ita maryam ce tawa, duk abinda Fadima ke dashi maryamma na dashi dan haka zan sakata a zuciyata na tirsasa kaina na soka duk da yanzu da za'a kasheni banajin idan naganta zan ganeta.

Fadima
Bani na tashiba sai da aka dawo daga kaisu Rumaisa shima juyi kawai nayi na cigaba da baccina. Washe gari tun da asuba Anty zainab tazo ta tasheni, ina tashi tace "Fadima ki tashi ki shirya da wuri zaku tafi gasu haj. Fatima can ma harsun fara shiri" da mamaki nake binta da ido nace "Anty ina zamu tafi?" Kallona tayi sai kuma ta fara murmushi tazo ta zauna a kusa dani tace "ayya babu wanda yayi miki bayani ko?" Kai kawai na daga ta cigaba "da farko Na'im aka zaba miki amma daga baya bansan yadda akaiba ya koma Saif, da Saif aka daura miki aure shi kuma Na'im aka bashi maryam kanwar Saif din, yanzu an yanke hukunci zaki bisu ki hadu da yan uwansu kafin hutunku ya kare sannan sai kuyi shawara tsakaninku idan tarewa zakiyi shikenan idan kuma sai kin gama makaranta to ya rage naku dan haka ki tashi ki shirya kar suzo suna jiranki" tashi tayi ta cigaba da hada min kayana tana maganar da bansan me take cewaba, I was shocked! Saif? Wani abune mai sanyi ya fara zagaya jikina da gudu tamkar yadda jini ke gudu a jikin dan adam, har wani tashi tsigar jikina keyi wani sanyi na shigata, me kenan? Saif din dana danni zuciyata na hakura dashi jiya da daddare tare da saka Na'im a zuciyata shine kuma za'ace ya zama mijina? Kallonta kawai na cigaba dayi har ta cikamin akwatuna biyu da kaya da duk wani abu da zan bukata sannan tace " wai bazaki tashibane kike zaune kina kallona?" Zumbur na mike kamar anyimin allura na wuce bandaki. Bayan nayi wanka na shirya muka ci abinci da maryam wadda itama ta koma tamkar kurma sannan akazo akace mu fito zamu tafi airport. Tunda muka fito daga gida nake ware idon ganin yaya Na'im, ina bukatar ganinsa inason nasan yadda yake inason na bashi hakuri amma babushi ba alamarsa har mukaje airport din muna zaune muna jiran a gama abinda za'ayi mu shiga wajen screening kaina a kasa ina tunannin wannan rayuwa da yadda take juyawa a lokaci kankani, alama naji an zauna kujerar dake opposite tawa ido na dago na zubesu cikin na yaya Na'im da fuskarsa ke dauke da murmushi duk da canjawar da tayi kamar ba tasaba, wata ajiyar zuciyace ta subucemin hawaye na taruwa a idona nace "yaya Na'im..." Saurin katseni yayi yace "karki farayimin kuka anan kisa mutane su rinka kallona kamar nayi miki wani abu kinsan yanzu mutane basa raina abin kallo" da mamaki nake kallonsa da gaske wasa yake yana dariya kamar babu abinda ya faru dan haka nima na goge hawayen fuakata duk da ina gogewa wani na zubane. Hannu ya mikomin na tsaya ina kallonsa yace "sarkata zaki ciromin" da sauri na shafa sarkarsa dake wuyana na sake marairaice fuska nace "yaya Na'im.." Yanzuma bai barni na karasaba yace "malama ciromin sarkata zakiyi kinaso matata ta hanani ganin fuskarta idan na nema?" Ya fada yana kallon maryam dake zaune kusa dani, ita nima na kalla ita kuma ta sauke kai kasa ya cigaba "kin gani ko? Dan kallar da nake ma inajin dadi har an kuma rufewa inaga na bar miki? Malama ciromin kayata" Saif ne dake can wajensu Halifa ya taso ba tare dana saniba yazo ta bayana ya cire sarkar, da sauri na waiga shima murmushi yake yace "haka kurin za'a rinka nima a wulakantamin Mata akan sarka? Cire masa kayarsa idan munje gida nima zansa miki wata" wuyan na kuma shafawa da najishi wani sakayau nace "dan Allah yaya Na'im kabarmin na saba da ita wuyana ba dadi" ai kuwa da sauri ya warce ta daga hannun Saif yana sawa a aljihu yace "anki din idan dai zai kare miki fada to ya saka miki wata sai ki dainajin wani irin" wani chain ne a nannade a hannun Saif ya cireshi ya sakamin yana cewa "yi manage da wannan kafin muje gida kinji " nidai hawayene kawai kebin fuskata ina binsu da kallo, sunayin abu tamkar babu abinda ya faru alhali ni haryanzu zuciyata zafi takemin.
Haka suka cigaba da surutunsu har aka gama komai muka yi sallama dasu momy ina ta kuka suna min dariyar ai ba tafiyar ba kenan amma nidai banijin dadi feena ma dakyar ta rabu da Saif tana ta kuka wai karya kuma tafiya ya barta. Sai da mukaje cikin jirgi sannan na kula ashe harda yaya Na'im za'ayi tafiyar, suna gabanmu shida maryam ni kuma ni da Saif sai Abdul da mama a baya haka muka mika cikin gajimare sai Nigeria.
Tunda mukaje Nigeria bamu zaunaba yau muna gidan wancan gobe muna gidan wancan, naje gidan yayyun Saif, yaya kamaluddeen da matarsa Anty Sadiya sai yaya shamsuddeen da matarsa Anty zarah sai yaya nuruddeen da matarsa Anty Aisha kowa da 'ya'yansa, sai yanzu na fahimci dalilin biyomu da yaya Na'im yayi shima nunashi ake a wajen iyayen maryam wadanda sai da aka kirasu a waya aka nemi aurenta a wajensu sannan Abba yayi mata walicci. Tunda mukazo bamu zauna munyi magana dani da Saif ba sai dai a cikin mutane saboda kullum da safe muke fita kuma sai dare muke dawowa, satinmu biyu yaya Na'im ya shirya ya koma gida ni kuma aka barni sai hutunmu ya kare tukunna nan da wata guda saboda hutun session ne.
Bayan komawar yaya Na'im rannan ina zaune a dakinmu zulai mai aikin mama tazo tace wai naje yaya Saif na kirana yana dakinsa, tashi nayi na yafa mayafina kan doguwar rigar jikina na tafi dakin nasa, yana zaune a bakin gado da fararen takaddu a gabansa ina shiga ya dago kai yana murmushi ya nunamin gefensa yace "zauna kiga wani abu" zama nayi ya dagomin takardar hannunsa yace "wacece wannan?" Kallon takaddar nayi kamar dai zanenane na zare idanu kamar wadda ta tsorata da kwalliya sosai a fuskata, da mamaki na juya na kalleshi har yanzu murmushi yake yace "baki gane ko wacece ba?" Nace "kamar ni" dariya ya fara yace "kamane ma?" Sunkuyar da kai nayi ina dan murmushi yace "kallon da kikayimin kenan ranar da na dawo ranar da kika kuma ganina bayan kinyi tsammanin na mutu" kallon takaddar na kumayi nace "nidai wannan ba idona bane" yace "Anya kuwa? Kije ki kalli mudubi ki zare ido zakiga ya koma haka" dariya na kumayi na maida kaina kasa.

FadimatuTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang