Chapter 50

100 8 0
                                    

Munyi shagali sosai feena yar shekaru goma ta zama yar budurwa kuma tana Kara girma kamarmu da ita na kuma fitowa, cake tawomin wai na graduation da yake sunayin snacks da Anty Rayya, cake din yayi kyau sosai inason yarinyar har fiye da yadda nake son kaina. Daga makaranta muka dungumo sai gida dama acan suka kwana, muna zuwa gida na baje a parlon su goggo ina faman zuri kamar mai cikin lahira dan wata muguwar yunwa nakeji, feenace ta shigo da gudu ta mikomin waya wai Halifa na min magana, ina karba naga video call suke nan nai waving dinsa ai kuwa har da dan ihunsa "happy graduation sister" murmushi nayi nace "thank you bro ya maka makarantar?" Hannu yasa ya yamutsa uban gashin dake kansa yace "gashinan ba dadi" nace "ba wani da dadin kenan tunda munanan muna missing dinka kai kuma kawai ka wani zarce masters" dariya ya fara yace "wai ke bazaki gaji da wannan mitarba? It's been long amma kullum sai kinyi mita" fuska na turbine kamar zanyi kuka nace "to ai abinne yaban haushi da yawa ina ta murna zan ganka kai kuma saboda baka missing dinmu shine kaki dawowa" yace "kinga kwantar da hankalinki inanan zuwa" da zumudi nace "yaushe?" Yace "sai kin haihu" rai na kuma hadewa na kashe wayar kawai su Rumaisa na min dariya.
Kwananmu biyar a diffa muka dau hanyar kano, kusan duk yan gidan sai da sukayi min rakiya mazane kawai babu sai momy mama da goggo. Mazan kuma uncle sagir ne kawai ya bimu sai yaya Na'im da bazai iya nisa da matarsaba. A motoci muka tafi, tunda muka taso karfe bakwai na safe bamu tsayaba sai a potaskum wajen 12 shima kafar maryamce ta kumbura dama sai da aka hanata tahowa ta zauna tayi ta yiwa yaya Na'im shagwaba dole ya daukota. Wani masallacine irin na matafiya dinnan dama a gaban motar mijinta take nan muka fito muma dan mu dan taka tamu kafar, zama dirshan yaya Na'im yayi a kasa yayi ta matsa mata kafa munayi musu dariya har sai da kafar ta dan saki sannan ya Kama hannunta wai sun tafi yawo, ganin abin nasu na gaskene muma muka shiga dan kauyan wajen bayan mun dawo muka siyo abinci sannan aka cigaba da tafiya karfe uku muka kuma tsayawa a shuwarin mukayi azahar mukai la'asar muka sake cin abinci sannan muka karaso kano. Bamu muka shigoba sai bayan magriba, muna shiga gate din gidan su Saif na hango murja a zaune ta zuba uban tagumi a kan baranda tana jiranmu, ina fitowa kuwa ta danno da gudu ta rukunkumeni har muna shirin faduwa sai da Saif ya taromu yana "murja hankali mana sai kin kayar da ita?" Dariya tayi tana cikani tace "sorry yaya nayi missing dintane da yawa" jikina na jawota ina cewa nima nayi missing dinki kanwata" haka muka shiga gidan anata murna, bangare guda aka saukemu saboda yawanmu ai kuwa muna cin abinci sai bacci nidai nasan cikin bacci Saif ya kirani na kuma dauka amma bansan me yaceminba bansan me nace masaba sai da asuba naga wayar kan filona sannan na tuna nayi iya yina kuma na tuna abinda nace na kasa haka na hakura. A ranar bayan mun huta da azahar su Rumaisa suka tafi yimin jere kamar kullum yauma ni da maryam kawai aka bari dan da tace zata yaya Na'im ya hana ta fara yi masa kuka Abdul ya zare Mata ido yace "wlh ko kukan me zakiyi bazamu da keba sai dai mijin Naki ma ya hakura ya zauna" banyi tsammanin zashibama yadda yayi fushin shima ya zauna rarrashinta sai da tayi bacci sannan ya bisu. Sai dare suka dawo washe gari sukaje suka karasa abinda basu karasaba sannan da daddare mukayi walima, anan harabar gidansu Saif akayi dagamu sai yan uwan Saif din yayyansa da matansu da yaransu yaya nuru harda jikokinsa yan yara, munyi kyau sosai munyi anko ni da Saif na shadda milk, anci ansha akayi addu'o'i sannan wajen karfe 10 suka rakani dakina. Kamar yadda akewa kowacce amarya nima haka akayimin sai da aka kara bawa su mama amanata sannan ammie da su Anty Rayya suka kaini har bedroom din gidana da babu nisa sosai daga gidansu mama. Bayan sun watse aka barmu da su Rumaisa sunce wlh sai an basu kudin sayan bakin da ba'a basuba tun tuni dan haka sunajin motsin su Saif suka rufemin fuska, yaya Na'im Saif da Abdul ne suka shigo sune abokanansa nan sukayi ta shakiyancinsu yaya Na'im harda cewa wai gaskiya karmu sake mu rinka cewa tare aka daura mana aure tunda dai shi gashinan har ya kusa zama Abba mu sai yanzu aka rakomu namu gidan danma maryam din ta taba yin bari da yanzu yana da dansa, ansha dariya sosai sai wajen 1 suka watse kowa na hamma ina tausaya musu idan suka kwanta bacci dan ba dan karamin ciwo jikinsu zaiyiba, mun taho a mota sannan tunda mukazo basu hutaba yauma gashi ko bacci basuyi da wuriba.
Bayan kwana biyu suka shirya suka koma Niger harda kukana shikenan nazo kenan ba batun komawa ba batun Zan karasa makaranta ko wani abu bani da kowa a Nigeria tunda ko Anty zainab ai tayimin nisa tafi kusa dasu akaina. Nasha kuka bayan mun dawoma sai da kyar nayi shiru bayan Saif ya sha wahalar lallashi sannan na sake na cigaba da rayuwata a gidana mai kyau, dan karamine ba girmane dashi canba drive in ne Wanda bazai dauki motoci sama da biyuba daya ma dai a sake, sai baranda mai dauke da kofofi biyu daya kofar parlonane Wanda kana shigowa dakin yarane a hannun damanka sai kitchen a kusa dashi sai kuma dan karamin corridor mai dauke da dakuma biyu suna kallon juna kowanne da toilet a ciki, babu komai a dakin yaran tunda basuzoba tukunna murjama mama tace bazata bamuba ta samu 'ya duk da Saif yace sai yasan yadda yayi ya kwato mana kayarmu. Daya kofar kuma dakin Saif ne ciki da falo da toilet shikenan sai public toilet a tsakar gida. Satinmu guda a kano munashan soyayyarmu yan uwa kuma na zuwa ganin gida a lokacin hutun Saif ya kare muka fara shirin komawa kaduna, da farko mama cewa tayi ya koma ya barni a kanon saboda yan uwa dake zuwa kar azo bamanan amma fir ya tubure shi wallahi bazai yaddaba daga karshema bata saniba muka shirya sai sallama mukaje mata, nidai kam da tana fada kunyace ta lullubeni na ce na fasa tafiya shi kuma ya turbine fuska kamar wani yaro, a dole tace muje. Mukullin gidan ya bata wai gashinan in case wani zaije sai a hadashi da murja suje ya gani, wani mugun kallo tayi masa tace " lallai saifu rashin kunyarka ta kai inda takai to dauki mukullinka babu mai zuwa ganin gidanka daga dangina har na abbanku kuje ku cinye juna" dariya ya fara ya koma kusa da kafarta a kasa ya zauna kana matsa mata kafa yana cewa "haba mama karkiyi fushi dani mana haba yayata uwata kinsan idan kikayi fushi dani bani da kowa ko? Allah ba dan nayi muku rashin kunya bane naga ita ansanta gidanne ba'a saniba shiyasa sorry uhm?" Kai ta dungure masa tana dariya tace "zakace wani baka da kowa baga matarkananba" shima dariyar yayi ganin ta fara saukowa yace "haba mama ai kinsan matsayinta daban naki daban ita matatace kanwata kawata zuciyata ke kuma babatace yayata rayuwata kinga ai da banbanci" dariya ta kumayi tace "tafi can sarkin wayo tashi ku tafi kar dare yayi" haka muka taso muka fito murja harda kukanta nace "daina kuka idan anyi Hutu sai ki taho kinji?" Kai kawai ta kada har muka shiga mota tana share hawaye. Tunda muka dau hanya na kwantar da kujera na fara bacci bani na farkaba sai da mukaje Zaria, ina tashi kuwa na fara aikin nawa wato magana, ni yanzuma kamar karamin surutu akai idan na fara zuba ko hutawa bana tsayawayi wani lokacin idan na fara bawa Saif labari sai ya rufemin baki sannan nake jan numfashi. Yunwa nace masa inaji ya tsaya ya siyomin yoghurt da nama sannan muka cigaba da tafiya har air force base cantonment Kaduna dake rafin kura Kaduna. Tun daga bakin gate na sarawa tsaron wajen wai danma shi sun sanshi, gidanjen ma'aikatan gidajene irin blocks dinnan masu apartment uku uku, gidajen sunyimin kyau tun daga waje, wanine yazo da gudu ya sarawa Saif sannan ya gaisheni dan da farko saramin yayi na tsaya kawai ina kallonsa bansan me Zan masaba sai kuma yayi murmushi ya gaisheni. Gidanmune a tsakiya wato na biyu Saif ya saka makulli ya bude muka shiga parlone Babba sai dining area mai kofar kitchen da store a ciki sannan a cikin parlon akwai kofa wadda idan ka shiga corridor ne dogo da dakuna guda uku daya na kallonka biyu kuma a Jere daga gefe sai toilet, gidan yayimin kyau da komai na amfani dan haka bamu taho da komaiba, washe gari yaje aiki sai 4 ya dawo nan muka fita duk abinda bamu dashi muka siyo. Rayuwa muke mai dadi mai cike da soyayya kullum zai fita sai 4 yake dawowa sometimes kuma sukan fita aiki suyi kwanaki, da farko na rinka jin tsoro amma daga baya na sake na kwantar da hankalina ko bayanan baccina nake sha banajin wani tsoro sai dai fargabar wani abu zai iya samunsa har yau na kasa sabawa da ita kullum ya fita ina cikin taraddadi har sai ya dawo. Makwabtanmu na kasa musulmaine hausawa mijin dan jigawane matar kuma yar nan kadunace mai suna zainab da dansu abulkhair, matar ba zata wuce sa'ataba muna mutunci sosai, na samanmu kuma suma Mata da mijine amma su Christians ne mr Adewale da matarsa Gloria suma suna da kirki da yayansu biyu amma nafi sabawa da Maman abulkhair.
Watanmu guda da dawowa akayi promoting Saif daga group captain zuwa air commondore, ranar munyi farin ciki sosai ranar da za'a rantsar dasu su mama sunzo malam Abdul an fara soyayya da muka dawo gida ana hirar Saif yayi ta tsokanarsa.
Nine months.
Ina zaune a parlor muna video call da Halifa sai zuba masa shagwaba nake akan yaki dawowa dariya yake sosai yace "Malama bafa Saif din bane ko bakya ganewane?" Sake turo baki nayi nace "ai na sani kaima kasan da shine nake wannan kukan da tuni ya dawo wallahi saboda shi bayason bacin raina" dariya ya kumayi yace " kinga dama ba nace sai kin haihu zan dawoba? To kinga ai ki kusa ko? Saura wata nawane ma?" Harararsa nayi nace "ban saniba" kafin ya bani ansa murja ta shigo da sallama ina amsawa ta taho da gudu ta rungumeni ta baya da yake na bawa kofar baya, dariya na Fara ina "oyoyo kanwata sannu da zuwa" hannunta na kama na zagayo da ita kan kujera ina cewa Halifa "shikenan dama hausawa na cewa idan wani ya kika da wuni wani da kwana zai soka ga kanwatanan tazo sai anjima" da sauri yace "wait wait Fadima wacece wannan din?" Dariya nayi nace "murjace fa" baki ya rike yace "dama haka take? Ai ban taba ganintaba" rai na hade nace "haka kamar ya?" Hannu ya daga in defense yace "Allah ya baki hakuri na zata bata kai girman hakaba ashe babbace" harararsa na kumayi nace "malam sai anjima" kafin ya kuma magana na kashe wayar na juya ina yiwa murja sannu da zuwa Saif ya shigo john na binsa da jakar murja, hade rai yayi yana harararta yace "shine kika gudo kika barni da jaka ko?" Fuska ta rufe tana dariya tace "afwan yaya ina sauri naga Anty ne shiyasa" ajiye jakar john yayi ya fice bayan ya gaisheni, tsugunnawa Saif yayi a gabana yana kallona nace "sannu da zuwa" yana murmushi yace "yauwa " sannan ya dora hannunsa akan cikina wadda yana dorawa babyn yayi motsi, hannuna nima na dora akan nasa nace "ya aka baro su mama" yace "suna lafiya kalau tanayi mini sannu ga wasu kayan rubutu nan ma ta bayar a Kawo miki" nace "to na gode" yace "ya babyna?" Dan dariya nayi nace "gashinan ai ya baka amsa yana kalau". I'm 8 months pregnant shiyasa Saif yaje ya lallaba mama da cewa bana iya aiki dan Allah ta ara mana murja tunda tayi candy shinefa ta yadda dazu da safe ya tafi ya daukota.

Thoughts and theories

FadimatuDonde viven las historias. Descúbrelo ahora