Tunda na sami ciki ban sha wata wahalaba, ko irin laulayinnan na farkon ciki banyiba sai danbanzan ci kamar jaka, dan a rana nakanci abinci kamar sau shida haka ci kuma da yawa bawai dan kadanba, kullum da asuba tun kafin ayi kiran sallah sai naci idan kuwa tsautsayi yasa ban tashi na nemi abinda zancinba ina mikewa zan fadi saboda jiri sai dai Saif ya nemomin da kansa, cikin ikon Allah haka nayi rainon cikin ba tare da wata matsalaba dan ko yanzu da ya girma bai hanani komaiba murjama mun daukotane kawai dan muyi amfani da cikin a matsayin excuse amma badan da gasken na kasa komai din ba. EDD na ya wuce da sati uku amma shiru kakeji banda wani mugun kumbura da nayi banajin ciwon komai idan naje asibiti ma sai suce lafiya kalau na kuma jinkirtawa ko zan haihu da kaina. Yau na fito daga wanka na tsaya gaban mudubi ina kallon ikon Allah, ada ni din yar siriryace dan gaba daya Rumaisa Rufaida humaira da hamida sun fini kiba amma yanzu at least zanyi hudu ko biyar din da, Saif dake kwance a gado yana danna waya ya kalleni yace "lafiya kika makale anan?" dan murmushi nayi nace "ikon Allah nake kallo zanyi kusan biyar dina ta da fa yanzu ko?" Dariya ya fara yana tashi zaune yace "kai fatima banason sharri biyarfa" nace " da gaske yanzu fa towel ko alamar rufeni bayayi balle nayi zaton zai ritsani, ni kaf dangina ma banajin akwai Wanda yakai haka kiba" dariya kawai ya cigaba sannan yace "yauwa dazu Dr ya kirani yace zuwa Monday zasuyi inducing dinki indai baki haihuba" gabanane ya fadi na dafe kirji ina fadin "Innalillahi wainnailaihir rajiun Deen inducing kuma" kamo hannuna yayi da sauri ya zaunar dani kusa dashi yace "kinga babu wani abu karki wani tada hankalinki kinji ba wani babban case bane it's normal" marairaicewa nayi ina kallonsa nace "Deen nidai tsoro nakeji" dan dariya yayi yace "fatima ke kinsan ba wani abu bane bafa theater akace za'ayi mikiba, inaso ki kwantarmin da hankalinki banason jininki yahau ko wani abu kinsan kinada hawan jini sannan already a sama yake yanzu karkice zaki tada hankalinki kinji? Kinsan zai iya jawo mana Marsala ko?" Kai kawai na kada na kwantar da kai a kan kafadarsa ko kayan bankai ga sakawaba saboda wani sanyi da jikina yayi. Har ranar Monday din kuwa ban haihuba dan haka ranar lahadi mama ta taho washe gari da safe muka shirya amma kememe naki fitowa daga daki nayi kwanciyata, Allah ya sani tsoro nakeji banason zuwa konan da can balle na tafi asibitin. Saif ne ya shigo a Karo na ba adadi yace "wai fatima ki taso mana su mama suna parlor suna ta jiranki plss" dan muskutawa nayi nace "yanzu zan taso dan hutawa nake gaba daya na gaji wallahi kamar nayi wani aiki" zama yayi a kusa dani ya dora kafata akan cinyarsa yana matsamin yace " nasan me kike gudu kawai bakyason zuwa asibitinne kuma idan munje shikenan in sha Allah zakiga kamar babu abinda ya faru an wuce wajen" shiru nayi ina maida numfashi kawai ya kama yimin tafiya tsutsa da sauri na janye kafa na mike ina dariya yace " kinsan wani Abu?" Kai kawai na kada ina murmushin dariyar da ban gamaba ya cigaba "Yau Halifa zai dawo" ido na zare nace "da gaske?" Murmushi ya kumayi yace "eh mana tun rannan muke maganar dashi yace kar na gaya miki saboda surprise yakeson yi miki yanzuma na karya alkawarine saboda na samu ki danyi farin ciki ko kya yadda mu tafi asibitin" da saurin da zan iya na mike tsaye ina cewa tashi mu tafi" dariya yayi yana kada kai shima ya mike muka jero zuwa parlor inda su mama ke jiranmu.
Bayan munje asibitin sunyimin duk abinda ya dace kama daga auna jinina da sauran abubuwa sannan suka maidani wani daki, wani magani nurse din ta kawomin dan mitsitsi nasha sannan ta fita, Saif ne ya shigo shida murja muka fara hira, muna cikin hirar na fara jin ciwo dama an shigo dasune dan karnayi tunani kafin na fara ciwon aje jinina ya hau. Gaba daya saif ya gigice tamkar shine ke nakudar tun kafin ciwon yayi wani nisa, Allah ya taimakeni karfe 10 na safe na fara labour amma kafin karfe 2 na haihu, bansan me na haifaba nidai nasan bayan naci bakar wahala mai kama da zan mutu dan har sai da na cire rai da zan tsira sannan na haihu Wanda babyn na fitowa na fita a hayyacina bani na farkaba sai dare wajen karfe takwas. Ina bude ido na saukesu akan murja da Halifa zaune akan kujera suna kallon babyn cikin showel fari tas, wani abu Halifa ya fada murja kuma na dariya tana kara leken fuskar babyn da alama akansa suke maganar. Dan juyi nayi ina salati, motsin da nayine yasa suka dago suka kalleni, yaushe rabon danaga wannan idon? God ba karamin so nakewa yan uwanaba musamman Halifa da feena banajin inason wani abu sama dasu. Da sauri shima ya taso yayo wajena murja na bin bayansa da babyn a hannunta, kafin suyi magana Saif ya shigo ai kuwa shima da sauri yayo wajen yana fadin ta tashi?" Eh yaya" murja tace yayin da Halifa yayi kneel down a gaban gadon ya kamo hannuna yace "Fadima you scared me na zata bazan kuma ganinkiba, ya kikeji yanzu? Akwai abinda ke miki ciwo? A kirawo likitan?" Hannuna na dora a kumatunsa ina murmushi nace "hey calm down babu abinda kemin ciwo lafiyata kalau, ka cika alkawari sai dana haihu sannan kazo" dan dariyar shima yake ya dora hannunsa akan nawa dake fuskarsa yace "na fada da bakin mala'iku shiyasa" Saif na kalla dake gefe nace "Deen" da sauri Halifa ya mike shi kuma ya karaso yana Kama hannuna yace " love ya kike? Akwai abinda ke miki ciwo?" Kai kawai na kada alamar aa yace "bari dai na kirawo Dr dama yace kina tashi ayi masa magana" mikewa yayi ya fita murja ta matso tace "sannu Anty" nace "yauwa murja" babyn ta kwantarmin a jikina yadda zan ga fuskarsa. My heart skip a beat, ban taba ganin jaririn da yayimin kyan wannan dan ba, tubarkallah Masha Allah alhmdulillah kalmomin da nake ta maimaitawa kenan a fili da zuciya, bacci yakeyi da dan fuskarsa yar karama dana kasa dauke ido daga kai har Dr ya shigo ya gama yimin abinda zaimin ya fita bayan yace a bani wani Abu naci. Zuwa can mama ta dawo dama gida taje, ta taho da abinci bayan nasha maltina da madara ta zubomin abinci naci na koshi sannan na koma na kwanta bayan anyi darun bada nono.
Kwanana biyu da haihuwa suka sallameni dan da rikeni sukai saboda jinina da ya hau, muna komawa gida mama ta fara hada kaya wai kano zamu tafi shi kuma Saif ya fara turbune fuskar bai yaddaba babu inda zamu tafi mu barshi, dole dai badan yasoba ya kyalemu muka tafi muka barshin. Tunda Halifa yazo kullum yana kusa dani babyn na hannunsu shida murja wani shiri sukeyi Wanda nidai zan iya cewa ban taba ganin Halifa na shiri da wata kamar murjaba komai yace ita, da muka tafi kanoma tare muka tafi dashi a ranar kuma su ammie sukazo gaba daya gidan harsu Abba amma su baby kawai suka gani suka koma akabar su ammie anan sai anyi suna. Ranar suna yaro yaci Muhammad nawal, munsha kaya har saida dakin da muke yayi mana kadan muka fara aikawa da wasu gidanmu, kowa a gidannan yace nawal idan aka fara daukansa wataran har tausayinsa nakeji gashi ba damar nace a ajiyemin yaro, ammie ce tace kullum na rinka karanta masa addu'o'i kafin mu kwanta saboda bakin mutane, yaron ban saniba kodan ni na haifeahi? Amma gani nake kamar kyansa har ya baci shiyasa kullum mutane na cikin tankaminshi ni kuma ina cikin tofeshi da lahaula.
To bayan suna aka watse yan Niger suka koma gida da kyar Halifa ya bisu amma yace yananan dawowa ba da dadewaba, daki daya muke kwana da murja nasha kamata tana waya ina zuwa zatayi saurin kashewa ni kuma sai na dauke kai kamar ban gantaba, rannan dai garin saurin kashewar wayar ta fadi ta tarwatse, kallonta na tsaya yi jikinta har rawa yake dan haka na kama hannunta muka zauna kan gado nace "murja waye" shiru tayi kanta a kasa sai da na sake tambaya kawai sai hawaye murya na rawa tace "Anty dan Allah kiyi hakuri wallahi na daina kulashi Allah ni dama nace masa tsoro nakeji shine yace wai ba komai ba zaice komaiba dan Allah Anty kiyi hakuri" da mamaki nace "murja nayi hakurin me? Wanene shi? Shi wa?" Kai ta mayar kasa ta cigaba da kuka bata bani amsaba, muna haka aka kara kiran wayar na dauka kawai na saka a kunne dan naga number ce babu suna, ina dagawa naji ance "wallahi murja tsoronki yayi yawa yauma fadimance ta sakaki kashemin waya? Na gaya miki Zan gaya mata da kai na ki daina jin tsoro kinki" da mamaki nace "Halifa?" Kawai sai shima ya kashe wayar, wata dariyace tazomin na toshe baki sai Dana maidata sannan na kalleta nace "murja" wani kukan ta kuma saki "Anty dan Allah kiyi hakuri wallahi zan fita harkarsa dan Allah karki koreni idan kika koreni bani da inda zani" da sauri na zamo kasa na zauna kusa da ita na kamo hannayenta nace "murja wai me kike fadane daga ina zan koreki? Ashe yadda muka daukeki kanwarmu uwa daya uba daya ke ba haka kika daukemuba? murja kinfi karfin a koreki a gidannan dan kema yar gidance ki kwantar da hankalinki sannan indai halifane bani da matsala dashi nasan zai rikeminke da amana kema zaki rikeshi da amana murja, ina sonki kamar yadda shima nakesonsa dan haka ki kwantar da hankalinki kinji ko?" Kai ta kada tana kuma share hawaye, hannu nasaka na dago habarta ina kallon fuskarta nace "murja karkiga Halifa dan uwanane ki kula da kanki duk namiji namijine komai kankantarsa komai girmansa komai kusancinki dashi nasan baki taba soyayyaba shiyasa nake gaya miki hakan sannan zaki Fara karatu karki bari soyayya ta shiga cikin karatunki ki kula kinji? Zan gayawa yayanki badan wani abuba sai dan bana boye masa komai ku cigaba da fuskantar juna kawai ki tuna koyaushe ina tare dake" kai ta kuma kadawa tace "Anty na gode kuma zan kula in sha Allah bazanyi abinda zakuyi Dana sanin tallafawa rayuwataba na gode da kaunarku na gode sosai" murmushi kawai nayi mata sannnan ta mike ta fita ina binta da kallon kauna, ina son yarinyar sosai. Ajiyar zuciya na sauke sannan na dau wayar murja na kira halifa, yana dauka yace "murja?" Hade rai nayi kamar yana kallona nace "Haifa ka kyauta" da sauri yace "wait Fadima karkiyimin wata fahimtar wallahi da gaske inason murja so na tsakani da Allah karki yanke min hukunci bakiji daga gareniba serious" still raina a hade nace "then fadi ta bakinnaka ina jinka" shiru yayi sai can ya wani karya murya kamar ba halifana ba yace "Fadima I'm serious inason murja wallahi aurenta zanyi ki yadda dani ki bani dama nayi alkawarin bazakiyi dana sanin hakanba Allah kuwan" dan dariya nayi nace "kai Halifa wannan karya muryar fa?" Ajiyan zuciya yayi yace "Fadima please bakisan abinda nakejiba" kafin na bashi amsa Saif ya shigo ya tsaya a bakin kofa yace " ke dawa?" Dan murmushi nayi nace "Wanda ke shirin zama sirikinka ne" da mamaki yake kallona yace "wa?" Gefena na nuna masa alamar ya zauna sannan na saka wayar a hand free nace "gaskiya kanwata tayi kankanta gaba daya fa shekararta sha shida ka kyalemin ita kaje can ka nemi wadda zaka aura" da sauri yace "kai Fadima please mana bafa cewa nayi zan aureta yanzuba ki gane mana" da mamaki Saif yace "Halifa?" Da sauri Halifa yace "yauwa dan Allah Yayana ka shiga maganarnan kasan illar so wai bazata bani murjaba" da wani mamakin dayafi na farko Saif yace "murja kuma? Menene tsakaninku? No Halifa murja yarinyace gaskiya karma muyi wannan maganar" ina iya hango yadda fuskar Halifa ta koma dan haka na fara dariya yace "Saif kun kasa ganewane bafa cewa nayi zan aureta yanzuba, sannan kuna ta batun wai yarinyace murja fa da hankalinta kuma wallahi Sonta nake bazan taba cutar da itaba kawai zanyi rainon soyayyatane kar wani yayimin shigar sauri amma idan na sami waje a zuciyarta kunga na samu tabbas please give me chance" dan murmushi mukayi Saif yace "shikenan Halifa ka bani taka kanwar kaima kasan bazan hanaka tawaba su mama ma nasan baka da matsala dasu so ka kwantar da hankalinka ka raini soyayyar taka ni kuma nayi maka alkawarin zan baka murja indai matarkace" da murna Halifa yace "yes! Thank you so much Saif na gode sosai kuma nayi maka alkawarin sonta tamkar raina har karshen rayuwata Fadima duk da bakiyi maganaba nasan kema kin yadda so thank you" dan dariya kawai nayi na kwantar da kaina kan kafadar Saif ba tare dana bashi amsaba. Nawal ne ya tashi Saif ya daukoshi muka tasashi a gaba muna kallo, hancinsa na taba nace "wai Deen a ina nawal ya dauko wannan kyan?" Yana dan dariya yace "a wajen mamarsa mana" da sauri nace " noo kai kasan bankai haka kyauba kaima bakakaiba so bansan a inda ya daukoba" kallonsa shima yayi yace "sai muyi masa addu'a Allah yasa kyan ya zame masa alkhairi a rayuwarsa" danyatsana na sakala a hannunsa na maida kaina kafadar Saif nace "ameen ya Allah" .Alhmdulillah anan mukazo karshen labarin fadimatu amma in sha Allah akwai bonus chapter da authors note a gaba zanyi post ko zuwa gobe ina fatan zaku karanta dan akwai important maganar da nakesonyi a ciki. Nagode
VOCÊ ESTÁ LENDO
Fadimatu
FanficLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...