Chapter 40

66 4 0
                                    

Haka rayuwa ta cigaba da garamin yadda ya kamata ina karatuna cikin kwanciyar hankali tare da yan uwana, ina zuwa gida kusan duk wata zanzo nayi musu weekend sannan na koma makaranta. Ina level 2 a lokacin kuma su Rumaisa kuma suna level 4 a lokacin na cika shekaru 21, a week end birthday dina ya kama dan haka na hado kaya na taho gida da niyyar zanzo nayi spending birthday dina tare da yan uwana, ranar juma'a nazo ana ta murna muka zauna muka sha hira washe gari ranar birthday din anayin magriba suka tasani a gaba wai sai min tafi dakinmu bacci sukeji haka badan nasoba muka tafi daki amma maimakon muyi baccin sai aka zauna aka kama shirin da bansan inda zamujeba, ina zaune ina danna waya Rumaisa ta fito wanka tace "Fadima saura ke kiyi sauri kar mu makara" da mamaki nake kallonta nace "wai ina zamuje?" Tana shafa mai tace "unguwa dan Allah ki tashi tun kafin yace ya fasa kaimu" still ina zaune nace "waye?" Da fushi ta juyo "yaya Na'im ne shikenan yanzu zaki tashi ko kuwa?" Mikewa nayi ina cewa "kai Rumaisa masifarki tayi yawa wallahi kar kuma ki manta shekara guda na baki zaki rinkamin tsawa" dariya kuma ta Fara tace "Allah ya baki hakuri yaya Fadima yanzu zaki iya shiga wankan?" Kai kawai na kada na wuce ban daki, bayan na fito ina shigowa Rufaida ta jani ta zaunar kan kujerar da muke zaman kwalliya ta fara yimin da mamaki nake kallonta nace "Rufaida kwalliya a wannan Daren?" Tace "party zamuje dole muyi kwalliya" da sauri nace "party kuma?" Kai kawai ta daga na cigaba "kuma su ammie sun yadda?" Kai ta kuma dagawa nace "kuma yaya Na'im ne zai kaimu?" Mikewa tayi sosai daga sunkuyowar da tayi da tace "eh eh eh Fadima zaki iya yin shiru nayi miki abinda zan miki?" Shiru nayi kawai amma zuciyata na ta tunane tunane har aka gama, wata doguwar riga Rumaisa ta shigomin da ita irin na 'yar tsana dinnan mai Kama da wedding gown, rigar lemon green ce da fararen flawers tayi kyau sosai, mikemin ita tayi tace "saka wannan " ganin basuson tambayoyi yasa na karba kawai na saka ba tare da na tambayi meyasa zan saka wannan rigar ba. Bayan na saka Rufaida ta nadamin wani dan kwali fari a kaina nayi kyau sosai sannan suma suka saka nasu kayan wandone fari da 3/4 riga lemon green da farin belt. Waje na nema na zauna suna ta saurin karasawa suna gamawa Rufaida ta Kira Na'im naji tana cewa "yaya kun shirya?" Bansan me yace mataba ta ajiye wayar tare da cewa "sun shirya ku taso muje" har sukaje bakin kofa ko motsi banyiba sai da Rumaisa ta waigo ta ganni zaune tace "Fadima taso mana" kai na kada nace "babu inda zani" da sauri suka dawo ciki da sauri har suna hada baki wajen cewa "me yasa " idona ya fara Kawo ruwa nace "akan wanne dalili ne bazaku gayamin inda zamujeba? Me yasa na saka wannan kayan ku kuma kuka saka wannan?" Da sauri Rufaida ta fara "dan Allah Fadima karkiyi kuka wallahi kina yin kuka kin bata kwalliyarki bamu da lokacin wata kwalliyar sannan yaya Na'im ne yace muzo mu shirya zamu rakashi wajen wani party muma bamusan inda zamujeba kaya kuma shi ya bamu wannan yace ki saka wannan mu kuma mu saka wannan amma bamusan inda zamuba" kallonsu kawai na tsayayi sai can kuma na mike muka fito waje sannan ta kuma dauko waya ta kirashi ta saka a handsfree "yaya kana ina?" Daga cikin wayar yace "ina garden kuzo muyi hoto tukunna" nan muka nufi garden din. Sanda mukaje wajen babu fitila ko daya wajen yayi baki kirin na dauko wayata ina kunna fitila ina cewa "a wannan duhun zamuyi pics din?" Su dai basu bani amsaba har muka shiga wajen sannan fitilun wajen suka kama gaba daya a lokaci daya tare da saka ihun gaba daya yan gidan bandani da na tsorata sosai na rufe idona, sai dana bude a hankali sannan na fahimci abinda ke faruwa, gaba daya wajen yasha decorations da white and green balloons da ribbons, sannan yan gidan ma gaba daya sunsha kwalliya inda yara mata gaba daya suka saka irin kayan jikinsu Rufaida yayin da maza kuma suka sha suit har su Yusuf halifane kawai babu. Nan da nan suka fara yimin wakar happy birthday, wani irin farin cikine yake shigata kawai ina tsaye ina kare musu kallo bakina har kunne, Na'im ne ya turo table din da cake din yake ya kawomin gabana sannan aka mikomin wuka na hanya su kuma suna min waka. Bayan na yanka cake dinne aka fara hotuna me hoto guda aka dauko, ai kuwa munsa pics kamar me nayi farin ciki sosai Halifa ma ya kirani yayimin happy birthday da mitar bayanan haka dai muka sha shagalinmu har da kukana dan farin ciki.
Ba karamin abu bane kaga yan uwanka sun shirya maka wani abu da zai faranta maka su nuna suna sonka su nuna sun damu da farin cikinka, nayi farin ciki sosai da wannan abun da yan uwana suka shiryamin kuma harda su Abba dady Abbie da uncle sagir da matansu gaba daya a wajen bawai iya yaraba nayi hoto da kowa na bawa kowa cake sannan su Abba suka koma cikin gida suka barmu mu yara a wajen nan kuma aka kunna waka aka fara casu. Ban taba yin rawaba a rayuwata dan haka na koma gefe ina kallonsu nan yaya Na'im yazo wai dole sai na taso nayi, nace bazanyiba nan ya saka su Rumaisa suka janyoni muka fara rawar a dole shi kuma yanayi mana video da wayarsa saboda me hotonma an sallameshi, na danyi rawa dasu Rumaisa kadan sannan na gudo na koma na zauna saboda ban iyaba kuma wata irin kunyar Na'im nakeji. Ranar dai munyi abinda mukeso dan har wajen 1am muna wajen sai da Abbie yayi magana yace dare fa yayi ya isa kuma haka sannan muka diba sai falonmu, anan fa muka kuma zubewa akayi ta hira sannan kowa ya bani gift dinsa aka kuma nunamin nasu dady suma da suka ajiyemin a falon, na yaya Na'im na fara daukowa Zan bude da sauri ya warce, kawai na tsaya ina kallonsa yace "ba yanzuba sai kin gama bude na kowa nawane na karshe kuma ba anan zaki budeba sai ke kadai" dariya su Rumaisa suka fara suna cewa "ahh wannan sirrine wannan sirrine" baki kawai na saki ina kallonsu ganin zasu maidani mahaukaciya kawai na fara bude ragowar. Na sami gifts masu kyau da nuna tsantsar soyayya tsakanina da yan uwana, ina cikin budewa kawai na saka kuka sai kuma duk jikinsu yayi sanyi suka tsaya suna kallona, cikin kuka nace "na gode da duk abinda kukeyimin na gode sosai ban taba zaton a rayuwata Zan sami yan uwaba ma balle na yi tsammanin zasu nunamin soyayya irin haka na godewa Allah daya hadani daku a lokacin da na fitar da rai sannan kuma ya bani ku masu sona nima ina sonku sosai thank you so much" su Rufaida ne suka matso muka rungume juna ina ci gaba da kukana a jikinsu, can Tj yayi gyaran murya tare da yin tafi yace "to ya isa haka lokacin kuka ya kare a cigaba da shagali" muka dago kai muna dariya sannan na goge fuskata Rufaida tace "wayyo Allah ta bata kwalliyar"gaba daya mukasa dariya na dauko tissue na karasa goge fuskar tawa gaba daya sannan kuma kowa ya mike akace to sai da safe kuma aje a kwanta yaran dama tuni sunyi bacci. Bayan kowa ya watse har mun hau sama yaya Na'im ya kirani wai na sauko kasa nayi mantuwa, ina saukowa na ganshi tsaye a dai dai farkon benen, ina zuwa ya mikomin kyautar dazu "kin manta baki karbi kyautarkiba" karba nayi ina dariya nace "kai yaya Na'im na zata ma wani abune, na gode" har na juya yace "Fadima" na waigo yace "please aji tausayina haka" Kallonsa kawai na tsaya inayi yace "jeki mana sai da safe" nace "ai ban gane me kake nufiba tukunna" yace "zaki gane a cikin nan" ya fada yana nuna dan kwalin dake hannuna, kallon kwalin nayi nace "OK sai da safe" na juya na haye sama.

FadimatuWhere stories live. Discover now