Fadimatu
Ta saman kafadar Na'im nake bin Saif da kallo har ya fice daga gidan, sannan sauke ajiyar zuciya na kalli Na'im da yake kallona tashin hankali rubuce a fuskarsa nace "yaya Na'im lafiyata kalau ba abinda ya sameni" yace "to ina kikaje menene dalilinki na fita? Gaba daya mun tsorata wallahi" dan kada kai nayi nace "kuyi hakuri kawai na fitane dan na sami fresh air bawai wani abuba" ajiyar zuciya yayi kawai yana kallona, ban kumabi ta kansaba na juya nayi cikin gida ina kuma kallon get din da Saif ya fita. Abinda ya faru a waje shi ya cigaba da faruwa a cikin gidan, kowa tambaya kawai yake ina naje? Babu abinda ya sameni? Blah blah blah. Tun ina basu amsa har na gaji naje na kwanta kawai na kudundune a cikin bargo nayi kamar bacci nake saboda banason kowa ya dameni. Tunda na kwanta ba abinda nake sai tunanin abinda ya faru yau, today was such a long day, na gaji burina kawai nayi bacci sai dai maimakon nayi baccin sai ya zamana duk abinda ya faru yau yana dawowa kaina tamkar film, abubuwa da yawa sun faru yau, gaba daya rayuwata ta canja ayau har bansan yadda zan tunanin gobena ba. Ina kwance hamida tazo ta tabani tana kirana a hankali, bude bargon da na lilliba dashi nayi iya fuskata nace " ya akai?" Tace "ashe bakiyi bacciba" kai kawai na kada mata dan bana bukatar bude bakina balle nayi wata magana, ganin bazan amsaba ta cigaba "yaya halifane ya kiraki a waya" ta fada tana mikomin wayata dake hannunta, karba nayi na saka a kunne nace "hello Halifa?" Maimakon naji muryar Halifa sai naji muryar wadda ban saba tsammaniba a yanzu, Saif ne yace "fatima zan iya ganinki?" Shiru nayi na kasa amsawa sai da ya sake cewa "fatima kina jina?" Kai na girgiza kamar yana kallona sai kuma na tuna ba kallona yakeba sannan da kyar na kakalo sauti can kasan makoshina nace "dare yayi Saif" a hankali yace "idan bakizo yanzuba bazamu kuma ganawaba domin zuwa gobe kin zama ta wani ba niba" bai kuma cewa komaiba ya kashe wayar, a hankali na mike kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, jikina har karkarwa yake hakan na nufin Na'im aka zabamin kenan? Innalillahi wainnailaihir rajiun ya Allah na rokeka kasa hakanne mafi alkhairi ka ciremin Saif a zuciyata ka sa na iya yiwa Na'im biyayya har karshen rayuwata. A hankali na sauko kasa bayan na saka hijabi, ina fitowa waje naga wajen kamar anyi shara babu kowa saboda dare yayi sosai. Kalle kalle na fara sannan naji wayata ta fara vibrating ina dauka yace "ina inda aka saukemu" a gidan Halifa aka sauki maza dan haka can na nufa, ina zuwa na ganshi zaune akan balcony din bakin kofa kan farar kujera da wata kujerar a gefe wadda ke nufin tawace kenan dan haka na zauna kai tun kafin ya gayamin. Shiru mukayi duk mu biyun zuwa can yace "fatima ya kike" sai a lokacin na fahimci tunda ya dawo ni dashi bamu zauna munyi maganaba sai yanzu, kallonsa nayi a hankali muka hada ido saboda shima ni yake kallo na sauke kai kasa sannan nace "I'm glad you are back" dan murmushi yayi mai sauti yace "I know" shiru muka sakeyi na wasu yan seconds sannan yace "Fatima I'm sorry ba tare da na tuntubekiba na sadaukar da soyayyata ga dan uwanki, bansan yadda zaki dauki lamarinba amma nasan bazai cutar dakeba tunda kina sonsa" shiru ya kumayi sannan ya cigaba bayan wasu seconds "fatima bansan yadda zan kwatanta miki yadda nakejiba but it hurts, idan na tuna gobe za'a daura miki aure da wani inajin dama na bari an kasheni a inda naje, dama na tsaya nima na fado daga jirgin na mutu, sai dai inaganin hakan is for the best" shiru ya sakeyi babu abinda kake iyaji sai sheshshekar kukana jin yayi shiru na fara magana da "Saif I'm so sorry ban rike maka alkawariba" da sauri ya katseni da cewa "no fatima don't be nasan kin rike nasan har yanzu kina rike da alkawarina wanda a yanzu nakeso ki saki" nima katseshi nayi da cewa "dana rike da duk wannan bata faruba" yace "dole sai ta faru ko menene kikai saboda wannan din shine kaddararmu it's not your fault it's not anyone's fault kin game?" shiru nayi ina ci gaba da kuka. Zuwa can yace "fatima kiyiwa mijinki biyayya please karkisa nayi danasanin abinda nayi, inason na cigaba da playing role na yayanki kamar yadda na fara farkon haduwarmu, duk abinda kike bukata ki kirani kinji ko menene shi sai dai idan bani da ikon yi miki" ahankali na dago kai nace "Saif why?" Da confusion yake kallona yace "why what?" Hannu na saka na goge hawayen fuskata duk da wani ke fitowa ba daga kafa, nace "menene yasa ka barwa Na'im ni" dan murmushi yayi yace "saboda ina ganin hakanne dai dai" kallonsa kawai nayi na dauke kai zuwa can ya cigaba da cewa "ban taba tsammanin zan iya cewa na barwa wani ke ba fatima inajin kamar a mafarki, nayi wahalar shekaru kusan hudu a banza, nayi komai da nayine dan na dawo wajenki kuma nazo a kurarren lokaci, zuciyata na zafi kamar zata fita daga kirjina inajin kamar numfashina zai dauke duk lokacin da na tuna wannan shine zamanmu na karshe ni dake gobe e yanzu kin zama ta wani" zuwa yanzu shima muryarsa ta fara rawa alamar yanason yin kuka, matso da kujerarsa yayi kusa dani ya kamo hannuna ya rike cikin nasa yana kallon cikin idona duk da nawa idon a kasa yake ya cigaba da cewa "fatima inajin kamar wannan mintunan kamar are harder than the 4 years danayi da boko haram saboda wancan at least ina da hope na wataran zan kubuta zan dawo wajenki amma yanzu shikenan idan kikayi aure kin tafi kenan har abada" hawayen idonsa ya goge ya cigaba da kallona ni kuma ina cigaba da kukana, a hankali ya dora kansa akan hannyenmu dake hade kawai ya fara kuka kamar wani karamin yaro, abin ya bani mamaki sosai ganin irin kukan da yake kamar ba Saif din dana saniba. A hankali na zame hannuna daga nasa sai kuma kawai ya mike zaune sosai tare da rufe fuskarsa da hannunsa ya cigaba da kukansa, sai da yayi mai isarsa sannan ya goge fuskarsa ya kalleni yana murmushin da kana gani kasan yakene irin mai ciwonnan yace "fatima ki koma gida dama so nake nayi magana dake for the last time kuma nayi shikenan kije ki kwanta" kallonsa na tsayayi shima ya dago kai ya kalleni idonsa yayi ja sosai kamar ba idon mutumba, ya kara ramewa akan yadda yazo dazu nace "are you ok?" Dan murmushi yayi yace "yeah, dama wani abune ya tokaremin zuciya kuma ya sauka I'm ok" a hankali na mike shima ya mike ya rakani har bakin kofa sannan muka kuma kallon juna na wasu seconds ne ko minutes ne banma saniba dan it's like time ya tsayane, banajin komai sai bugun zuciyarmu dake tafiya tare, bana ganin komai sai shi kuma wai kallon karshe nake masa kafin na kuma ganinsa dole na canja masa kallo tunda zuwa lokacin na zama matar wani. Ni na fara dauke kai sannan shima ya sauke nasa tare da ajiyar zuciya yace "kije gida Allah ya tashemu lafiya Allah ya sanya alkhairi gobe ba lallaine ki ganniba dan inajin da sassafe zan koma Nigeria" da sauri nace "me yasa?" Kansa ya dan shafa sannan yace yana dan murmushi "bazan iya zama wajen daurin aurenkiba fatima Zan wuce kawai su mama ma hadu a gida kawai" wani hawayene ya kuma zubomin nace "haba Saif please inason kuma ganinka " gyara tsaiwa yayi yace "fatima zaki kuma ganina amma ba yanzuba, sai na tabbatar na sabawa zuciyata ta yadda cewar kinyi aure sannan na tabbatar kema kin Saba da kasancewarki a matsayin matar aure kafin ki sake ganina" hawaye na sake sharewa nace "please nidai ka tsaya ba yanzu ka gama cewa duk abinda nakeso zakayiminba?" Kai ya kada yana cewa "amma wannan fatima is different" da sauri na kuma marairaice murya nace "dan Allah" kallona yayi sosai sannan yace "shikenan zan zauna shikenan?" Kai na daga ya cigaba "shikenan maza kije ki kwanta" wucewa nayi ciki ina tafiya ina waigensa shi kuma yana dagamin hannu har na gama shigewa ciki sannan na hau sama da gudu na fada kan gado na saki wani irin kuka irin me rike numfashi dinnan. Kusan kwana nayi ina kuka har aka Fara kiraye kirayen sallar asuba, zuwa wannan lokacin ba dan karamin zazzabine a jikinaba ga wani irin ciwon kai ina iyajin alamun hawan da jinina yayi, da kyar na samu nayi bacci.
Da safe anyi niyyar tashina amma saboda yanayin jikina dana tashi naci abinci nasha magani kawai sai na koma aka hana kowa shigowa dakin dan haka na samu nayi bacci, bansan sanda akayi daurin aurenba dan sai 12pm na farka, ba laifi nadanji sauki amma har yanzu kaina ba dan karamin ciwo yakeba, bayan nayi wanka akayimin light kwalliya saboda dama haka aka tsara ranar daurin aure ba zamuyi heavy kwalliyaba, na gama shiryawa su Rumaisa na zaune a daki ana ta hira nima na shiga cikinsu duk da har yanzu wani iri nakejina, ina zama akazo akace mana mu fito za'ayi photo, harabar gidan muka fito gidan duk girmansa amma a cike yake da mutane babu masaka tsinke saboda a masallacin jikin estate din aka daura auren dukka ukun, duk dubban mutanen dake wajen ina fitowa na hango Yayana (tunda yanzu ya koma Yayana) ya fito tamkar wata a cikin taurari shi kadai ke walkiya, ido muka hada furkarsa tayi fiyau, murmushi nayi masa shima ya maidamin da nasa murmushin na musamman sannan aka fara daukan hotuna.
Kaya iri daya muka saka ni da Rumaisa da Rufaida su kuma mazan da wuya ka gabe wanene ango saboda gaba dayansu farar shadda suka saka harsu dady sai dai banbancin aiki, munyi hotuna sosai da kowa sai dai abinda ke bani mamaki komai da Saif ake hadani ba Na'im ba duk da shima munyi pics da yawadasu amma ba kamar Saif ba. Muna cikin hotunanne na fahimciwani abu, Maryam ma irin kayanmune a jikinta sai dai banbancin aiki namu iri dayane, hadamu akayi mu takwas aka dauka kowa na sam barka. Sai da aka tsagaita mun koma daki da niyyar canja kaya su kuma mazan sun tafi reception din da zasuyi bayan daurin aure, muna shiga daki naji yan matam nata tsokanar maryam da suna unexpected amarya, ban tambayesuba suma basu yimin bayaniba har yamma aka fara shirin kai amarya, masu shiryamu zunzo amma sai suka shirya Rufaida da Rumaisa mu kuma akayi mana normal shiri, wajen Abba aka kaimu a parlonsa yayi mana fada sosai mai ratsa jiki munsha kuka sosai sannan su dady ma sukayi mana nasu haka su mama, saboda yawan manyan masuyi mana fada sai wajen magrib muka fito daga nan muka tarar matocin daukan amarya sunzo har an fara deban mutane. Su Anty zainab na rike damu har motar dasu Rumaisa zasu shiga muna ta faman kuka haka aka sakasu suka tafi suka barmu ni da maryam kuma muka koma ciki. Muna shiga kowa ya kwanta muka cigaba da kukanmu, Kafin yan kai amarya su dawo nayi bacci bansan dai maryam ba.Tabb me kuke tunanin ya farune wai🤔🤔
Thoughts and theories
YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...