Kallonsa na cigaba dayi shi kuma yaki juyowa sai juya kai kawai yake, ganin bazai bani amsaba yasa na zagaya gabansa hawaye na taruwa a idona nace "yaya Na'im me kake nufi? Wanne alkawari kayimin kake kuma shirin karyashi yanzu?" A hankali ya dago ido ya kalleni sannan yace "I'm sorry Fadima I'm so sorry" sannan ya juya yabar wajen da sauri. Gaba daya ji nayi rayuwar ta isheni me ke shirin faruwa dani? Nasan Na'im nayin tsautsayin fadin abinda ke ransa shikenan tawa ta kare shikenan hope din danake dashi na Saif zai dawo kafin na gama makaranta ya kare bazasu taba bari na gamaba zasu auramin Na'im.
Tunda wannan abin ya faru ban kuma saka Na'im a idonaba har washe gari da safe muka shirya zamu tafi da akaje akace masa mun shirya sai cewa yayi Tj ya kaimu bayajin dadi kuma ko fitowa baiyi munyi sallama ba, bayan mun shiga mota muna cikin tafiya Tj ya kalleni ta mirror nayi shiru ana ta hira amma ni ko kallonsu banayi yace "Fadima wai meya hadaku ke da mutuminki ne?" Da sauri na dago kai nace "naam?" Yace "mutuminki nace meye hadaku? Naga duk ku biyun sai wani shan kamshi kuke yanzuma yaki kaiku kuma lafiyarsa kalau it's like you are avoiding each other" murmushi kawai nayi na maida kaina kasa ban bashi amsaba na cigaba da tunanina. Anya kuwa idan nayiwa Na'im haka nayi masa adalci? Idan na karbi soyayyar Na'im kuma nayiwa Saif adalci? Wai me yake damun rayuwata ne? Irin tunanikan da na rinkayi kenan har muka kai zinder ba Wanda nayiwa magana ba Wanda ya kuma yimin.
Bayan mun koma makaranta na cigaba da rayuwata yadda na saba duk da koyaushe Na'im na raina, na damu sosai da rashin jinsa kwana biyu, ganin har kwana uku da dawowata bai kiraniba yasa bayan na dawo daga class na zauna akan gadona na dauko waya na kirashi, na jima tana ringing sai da ta kusan katsewa sannan ya dauka sai kuma duk mukayi shiru, mun jima da wayoyin a kunne kowa ya kasa magana dagani harshi amma nasan wayar na kunnensa dan ina iya jiyo numfashinsa, ganin bazamuyi maganaba kawai na kashe wayata na koma na kwanta, ina kwanciya wayata ta fata Kara na dauko ta daga kasan filon dana cusata Na'im ne dan haka na ajiye na cigaba da kwanciyata yayi ta kira har ya gaji dan kansa ya daina, kuka na zauna na rinkayi daga nan bacci ya daukeni bani na tashiba sai da magriba amatullah ta tasheni.
Washe gari mun fito daga lectures na sami wata kujera irin na suminti dinnan na zauna ina kallon wayata, bawai chatting ko game nakeba kawai screen din wayar na kafawa Ido a zuciyata inajin ina jiran wani abu amma kuma na rasa menene abun, idona naji an rife ta baya, a hankali nasa hannu na shafa hannun daya rufemin idon da sauri na zame daga rukon na juya a fusace kawai ya kama yimin dariya ya zagayo ya zauna a kusa dani, a zuciye nace "wai Aliyu me yasa bakajin maganane a rayuwarka? Nace ka daina tabani ka daina tabani kakiji ko? Wallahi zanyi maka rashin mutunci na gaya maka" hannu ya daga sama yana cewa "yo yo cool down mana babe menene dan na rufe miki ido? idonki fa kawai na tafa ba wani abinba" kafin nakai ga bashi amsa naga anzo an tsaya a gabanmu dan haka na juyo dan ganin wanne dan rainin hankalinne kuma na huce yanzu a kansa? Amma sai me? Yaya Na'im na gani tsaye ya zira hannunsa cikin aljihun wandonsa kawai yanayiwa Aliyu wani mugun kallo, da sauri na mike tsaye nima ina kallonsa kafin shima aliyun ya mike, hannuna kawai Na'im ya kama ya juya zuwa parking lot inda motarsa take muna zuwa kawai ya bude min kofar motar na shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya side din driver shima ya shiga. Shiru mukayi gaba dayanmu zuwa can na gaji da awkwardness din nayi breaking silence din ta hanyar gyaran murya nace "amm yaya Na'im dan Allah...." Bai barni nace komaiba ya katseni da cewa "just drop it Fadima subutar baki nayi banyi niyyar bayyana mikiba bansan ya akai na fadaba dan haka ki dauka kamar a ban taba fadaba kiyi hakuri" shiru muka kuma yi na wani lokaci zuwa can ya kuma cewa "akan Aliyu ne ko?" Da mamaki nake kallonsa nace "akai me?" Sai da ya hadiye bacin ransa yadda zai iya controlling muryarsa sannan yace "akansane bazaki soniba ko" Baki kawai na saki ya juyo yana kallona nace "ta yaya ma zakayi wannan tunanin yaya Na'im? Menene hadina da Aliyu da har zai iya shiga tsakanina da kai?" Juyowa yayi sosai yana kallona yace "ba gashinan ba har yana rufe miki ido? Idan ba da wani abu tsakaninkuba ai bazaiyi miki hakanba, bayan rufe ido sai kuma me yakeyi miki?" Nima juyowa nayi sosai ina kallonsa nace " wallahi ka bani mamaki yaya Na'im ta yaya zakayi tsammanin zanso wannan abun? Aliyu is such an asshole babu yadda za'ayi nasoshi kuma nayi zaton idan kai aka yiwa wannan tambayar zaka iya bada amsarta amma Kaine me yimin beside ni ba cewa nayi bana sonkaba" ido da baki gaba daya ya saki yana kallona sannan yace "Fadima ..." Nima ban barshi ya karasaba nace "bance banasonkaba ban kuma ce inasonkaba dan haka karkayi wani tunani" na bude kofar motar nayi ficewata na barshi a wajen, raina ya baci ta yaya ma za'ayi ina da Saif yayi zaton zanso wani Aliyu? Aliyu kyaune kawai na fuska dashi amma sam bana fatan rayuwa da irin wadannan mutanan bashi da hali kwatakwata.
Lectures kawai na tafi wadda na tarar ma har na makara amma dai an barni na shiga, jina nake wani sakayau kamar na sauke wasu kaya da nayi kwana da kwanaki dasu a kaina ban kuma san dalilin da yasa nakejin hakanba, muna lectures Na'im ya kirani nayi rejecting na tura masa text muna lectures dan haka muna fitowa da yake wannan ce ta karshe a yau na kirashi a waya ya gayamin inda yake. A mota na kuma tarar dashi kamar dazu yana zaune kawai yana shan kida bayan na shiga yace "kin gama lectures din?" Nace "eh na gama da yau" shiru mukayi na wasu yan seconds sannan yace "fadima dan Allah wata alfarma nake nema a wajenki" nace "Allah yasa ina da ikonyi" yace "kinama dashi indai kinyi niyya" ban bashi amsaba ya cigaba "dan Allah Fadima ki fita harkar Aliyu ki daina kulashi ki nemi wata kawar mace ko namijinma amma mai hankali banda Aliyu, ba abokin kirkibane zai rinka tabaka duk wanda yake irin wannan wallahi ba na Allah bane kinji?" Shiru nayi sai da na tabbatar ya gama sannan na dago na kalleshi nace " yaya Na'im bafa barinsa nake yana tabaninba fa yauma ya shammacenine kuma ba halinsa bane bansan yau me yasa yayiba amma zanyi masa magana zai daina idan kuma bai dainaba zan fita harkarsa in sha Allah" kallona yayi yace "yanzu dai bazaki iya rabuwa dashiba sai kin wani bashi second Chance kenan?" Da sauri nace "no ba haka bane kawai gani nayi bai kamata hakanan na daina shiga harkarsaba sannan irin wadannan idan ana gudunsu suna kuma zama worse ne amma idan aka jasu a jiki ana nuna musu laifinsu zasu daina" wata yar dafiya yayi sannan yace "wallahi Fadima har yanzu ke yarinyace, to kafin ki nuna musu laifin nasu su sunsaki aikata laifin, annabima ya hanamu harka da mugayen abokanai saboda illar hakan su kuma idan sukaga ana gudunsu zasu gyarane saboda bazasu iya zama su kadaiba" nima murmushi nayi masa nace "shikenan nayi maka alkawarin zan fita a harkarsa amma a hankali bazan iya kawai rana daya na daina kulashiba a hankali zan fita harkarsa" yace "yauwa mi sœur yanzu tafiya zanzo nayi kar dare yayimin garinmu da nisa sannan gobe inason zuwa Chad ganin wasu kaya kinga ya kamata ace nayi bacci da wuri" agogo na kalla nace gaskiya kam ya kamata wai dama me ya kawoka garinnan" kai ya maida ya kwantar jikin kujera yana min wani kallo yace "missing din kanwata nayi kawai nazo dan na ganta" dariya na fara sannan nace "eh lallai wannan kanwa da tsada take tun daga diffa a taho zinder kawai ganinta" shima yana dariyar yace "ai ta isane" har na bude kofar zan fita nace " kun gaisa dasu Rumaisa kuwa ?" Kai kawai ya daga still yana kwance a jikin kujerar dan haka na fita tare da rufe masa kofar sannan na ziro kaina ta window nace "Allah ya kiyaye hanya ka gaishemin da kowa musamman Abba dan tsoho sannan a tahomin da tsarabar chadi" mikewa yayi ya zauna sosai sannan yace "zasuji ni wallahi bacci ma nakeji" na rike baki ina dariya nace "bacci kuma kai da zakayi driving?" Yace "ya zanyi dole na watstsake na tafi dama babu abinda zanyi gobe sai na kwana anan gobe na tafi amma ya zama dole na koma yanzu bye take care" nima na daga masa hannu nace "bye " ina tsaye ya juya motarsa ya kuma dago min hannu nima na daga masa har ya fice daga arean sannan na juya zan tafi mukayi ido biyu da amatullah da Khadija sunayimin dariya juyawa nayi zan wuce amah ta sha gabana yace "kawai to ki bishi mana irin wannan bye bye kamar hannun zai tsinke" wani irin bugawa naji kirjina yayi na waiga da sauri ina kallon inda motar tabi amma babushi ba alamarsa komai iri dayane kowa alfarma ya nema a wajena kowa kowa nakiyi masa alfarmar direct sai da nayi musu kowa yace bayason tafiya nayiwa kowa byebye an ganni an fadamin abu iri daya Innalillahi wainnailaihir rajiun. Juyawa kawai nayi ina tafiya ba tare da nasan inda nake saka kafaba ya ubangiji kar ka dora min wannan kaddarar ya Allah ba Na'im ba ba yanzuba ya Allah, bansan yadda akai na kai kaina dakinsu Rumaisa ba ina zuwa na zube a kan gadon Rufaida na Fara kuka, bamasanan sai daga baya suka dawo suka tarar Dani a haka nan hankalinsu ya tashi tambaya babu wadda basuyiminba amma naki basu amsa ban kuma daina kukanba ina duba agogo har karfe daya na dare sannan na Kira wayarsa kirjina na dukan uku uku, sau uku ina Kira tana katsewa ba'a daukaba dan haka na Kara tsananta kukan da nake nan da nan Rufaida da ta shimfida bargo a kasa tana bacci da Rumaisa itama dake bacci a gadonta suka mike suna kallona, tsaki Rumaisa taja tace "wai ke Fadima tsakani da Allah menene matsalarki? Shikenan ki tasa mutane a gaba da kuka kuma kinki fada musu abinda akayi miki? Idan ke bazakiyi bacciba mu bacci mukeji haba" ta kuma wani tsakin ta juya ta cigaba da baccinta Wanda nasan kwanciyar kawai tayi amma ba baccin takeba. A karo na hudu na kuma kira tana fara ringin kuwa ya dauka tare da cewa "mi sœur bakiyi bacciba?" Sai kuma yaji alamar kuka nake nan da nan shima hankalinsa ya tashi ya fara "subhanallahi Fadima me ya sameki? Menene kike kuka?" Ina kukan nace "yaya Na'im dan Allah kaima karka mutu dan Allah ba yanzuba idan ka mutu wallahi mutuwa nima zanyi har yanzu ban gama farfadowa daga mutuwar Saif ba wallahi ka mutu nima mutuwa zanyi" har hada baki yake wajen cewa " wayace miki mutuwa zanyi? Menene ya faru" nace "duk abinda ya faru da ni dakai yau kusan hakane ya faru ranar da zamu rabu da Saif wallahi same abune komai kuma shima ganina dashi na karshe kenan" hankalinsa ya dan Fara kwanciya ina iya ji ta cikin muryarsa yace "menene ya faru ranar" nan na zauna na bashi labarin duk abinda ya faru ranar da Saif zai tafi sai da na gama sannan ya fara yimin dariya yace "kinga kanwata kawai dacene babu abinda zai sameni in sha Allah kinji? Ki kwantar da hankalinki yanzu ki kwanta kiyi bacci badai tun da na taho kike kukaba?" Shiru nayi ban amsaba sai ajiyar zuciya da nake da sauri yace "ya Allah haba Fadima me yasa Innalillahi wainnailaihir rajiun yanzu to ki kwanta kiyi bacci kinji ko? Gobe ma idan kinada lectures da safe kar kije ki samu kiyi bacci kinaso jininki ya haune? Gaki a makaranta ke kadai?" Nan ma shiru nayi sai da yace "ko bakyajina" nace "inaji kayi hakuri" ya cigaba "maza ki kwanta karki kara irin wannan kinji ko?" Na daga kai kamar yana kallona sannan na zame na kwanta yace "kin kwanta ?" Nace "eh" yace "yauwa yanzu Bari na baki wani labari yadda zakiyi bacci bazaki tsaya tunaniba, kiyi baccifa kinji ko? Maza rufe idonki" nan da nan kuwa na rufe sannan ya fara bani labarin da ban kai ga fahimtar abinda yake fadaba ma nayi bacci.

YOU ARE READING
Fadimatu
FanfictionLabari akan yarinya fadimatu da tayi experiencing rayuwar arziki da wadata take rayuwa tamkar sarauniya kwatsam kaddararta ta canja zuwa rayuwa rashi da talauci, ta dandani zazzafar soyayya daga mazaje biyu da sukayi confusing zuciyarta, labari me d...